“Mala’ikan Ubangiji Yana Kafa Sansani A Kewaye Da Masu-tsoronsa”
Christabel Connell
Ce ta ba da labarin
Mun shagala wajen amsa tambayoyin Christopher da babu wani cikinmu da ya lura cewa dare ya yi sosai; kuma ba mu lura ba cewa Christopher yana ta kallon waje ta taga. Daga baya ya juya ya ce mana, “Ya fi kyau ku tafi yanzu.” Sai ya raka mu zuwa inda muka ajiye kekunanmu kuma muka yi ban kwana da shi. Menene ya lura da shi da yake da haɗari haka?
SUNANA Christabel Earl, an haife ni ne a birnin Sheffield, a Ingila, a shekara ta 1927. Bom ya halaka gidanmu a lokacin Yaƙin Duniya na biyu, saboda haka, an kai ni na zauna da kakata don in gama makarantata. A wata makarantar Katolika da nake, na ci gaba da tambayar mata masu zaman zuhudu abin da ya sa ake yawan mugunta. Da su da kuma wasu da suke bin wani addini da na yi wa tambaya sun kasa ba ni amsa mai gamsarwa.
Bayan an gama Yaƙin Duniya na biyu, na koyi aikin malamar asibiti. Na ƙaura zuwa Landan don na yi aiki a Babban Asibitin da ke birnin Paddington, amma mugunta ta fi yawa a birni. Ba da daɗewa ba da yayana ya tafi Yaƙin Koriya, na ga mugun faɗa tsakanin mutane biyu a gaban asibitin da nake aiki. Babu wanda ya taimaka wa mutumin da aka buga, kuma ya yi hasarar idanunsa domin dūkan. A wannan lokacin, mahaifiyata ta kai ni taron mutanen da suke magana da matattu ta hanyar duba, amma duk da haka ban san dalilin da ya sa ake yawan mugunta ba.
An Ƙarfafa Ni Na Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki
Wata rana babban yayana, John, wanda ya zama Mashaidin Jehobah, ya ziyarce mu. Ya tambaye ni: “Kin san dalilin da ya waɗannan miyagun abubuwa suke faruwa?” Na amsa, “a’a.” Ya buɗe Littafinsa Mai Tsarki kuma ya karanta Ru’ya ta Yohanna 12:7-12. Yanzu na fahimci cewa Shaiɗan da aljanunsa ne ainihi suke haddasa mugunta a duniya. Na bi shawarar da John ya ba ni, ba da daɗewa ba na soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma, a lokacin ban yi baftisma ba domin ina jin tsoron mutane.—Mis. 29:25.
Yayata Dorothy, ta zama Mashaidiya. Sa’ad da ta dawo daga taron gunduma na ƙasashe a New York a shekara ta 1953 da saurayinta, Bill Roberts, na gaya musu cewa wata ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Bill ya tambaye ni: “Kin karanta dukan nassosi da ke cikin littafin? Kin ja layin amsoshin da ke cikin littafin?” Sa’ad da na ce a’a, sai ya ce: “Ba ki yi nazari ba tukun! Ki je ki sami wannan ’yar’uwar, ki soma kuma!” A wannan lokacin ne aljanu suka soma damu na. Na gaya wa Jehobah ya kāre ni kuma ya ’yantar da ni daga hannunsu.
Aikin Majagaba a Scotland da Kuma Ireland
Na yi baftisma a ranar 16 ga Janairu, a shekara ta 1954, na kammala aikin malamar asibiti bisa ga yarjejeniyar da na yi da asibitin a watan Mayu, kuma na soma majagaba a watan Yuni. Bayan wata takwas, an tura ni birnin Grangemouth, a ƙasar Scotland, a matsayin majagaba na musamman. A wajen na ga cewa mala’ikun Jehobah suna “kafa sansani” a ko’ina sa’ad da nake aiki a irin wannan karkara.—Zab. 34:7.
An tura ni yin wa’azi a ƙasar Ireland a shekara ta 1956. An aika ni zuwa birnin Galway tare da ’yan’uwa mata biyu. A rana ta farko, na haɗu da wani firist. Ba da daɗewa ba, wani ɗan sanda ya zo ya kama ni da abokiyar wa’azi ta kuma ya kai mu ofishin ’yan sanda. Sa’ad da ya samu sunayenmu da inda muke zaune, nan da nan ya ɗauki tarho. Mun ji yana cewa, “Fada, na san ainihin inda suke zaune.” Firist ɗin ne ya aike shi! An matsa wa mai gidan da muke zaune ya kore mu, saboda haka, ofishin reshe ya ce mu bar wajen. Mun makara da minti goma sa’ad da muka kai tashar jirgin ƙasa. Amma, jirgin bai tashi ba tukuna kuma wani mutum yana jira ya tabbata cewa mun shiga jirgin. Hakan ya faru ne bayan mun yi makonni uku kawai a garin Galway!
An aika mu zuwa Limerick, wani birnin da Cocin Katolika yake da iko sosai. A kai a kai, taron ’yan banza suna yi mana eho. Mutane da yawa suna jin tsoron tattaunawa da mu a bakin ƙofarsu. Shekara guda da ta wuce, an bugi wani ɗan’uwa a wani ƙaramin gari na Cloonlara. Saboda haka, mun yi farin cikin saduwa da Christopher da aka ambata a farkon wannan talifin, wanda ya gaya mana mu dawo mu amsa tambayoyinsa na Littafi Mai Tsarki. A lokacin ziyararmu, wani firist ya shigo kuma ya gaya wa Christopher ya ce mu tafi. Ya ƙi ya amince da abin da firist ɗin ya ce, kuma ya gaya masa: “Waɗannan matan sun ƙwanƙwasa ƙofata, kuma na gaya musu su shigo kafin su shigo cikin gidana. Amma ban gayyace ka ba, kuma ba ka ƙwanƙwasa kofa ba.” Firist ɗin ya yi fushi kuma ya tafi.
Ba mu sani ba cewa wannan firist ɗin ya tara maza da yawa da suke jiranmu a waje ba. Da yake ya san cewa mutanen suna fushi da mu, shi ya sa Christopher ya aikata yadda aka kwatanta a somawar wannan talifin. Ya sa muka zauna har suka watse. Daga baya mun ji cewa an tilasta wa shi da iyalinsa su ƙaura daga wannan yankin, kuma suka koma Ingila.
Gayyata Zuwa Makarantar Gilead
Ina shirin halartan Taron Ƙasashe na Divine Will da aka yi a Amirka a shekara ta 1958 sa’ad da na samu gayyatar zuwa makarantar Gilead, aji na talatin da uku. Maimakon na koma gida bayan taron, na yi hidima a garin Collingwood, Ontario, a Kanada, har sa’ad da aka soma Makarantar Gilead a shekara ta 1959. A lokacin taron, na haɗu da Eric Connell. Ya koyi gaskiya a shekara ta 1957 kuma ya soma aikin majagaba a shekara ta 1958. Bayan taron, yana rubuta mini wasiƙa a kowace rana a lokacin da nake Kanada da kuma lokacin da nake makarantar Gilead. Ban san abin da za mu yi ba bayan na sauke karatu.
Halartan makarantar Gilead abu ne mai muhimmanci a rayuwata. Muna aji ɗaya da yayata Dorothy da mijinta. An aika su zuwa ƙasar Portugal su je su yi aikin wa’azi na ƙasashen waje. Abin mamaki, an tura ni ƙasar Ireland. Na yi baƙin ciki sosai da yake ba zan tafi tare da yayata ba! Na tambayi ɗaya daga cikin malaman ko na yi wani laifi ne. Ya amsa, “a’a. Ke da abokiyar aikinki, Eileen Mahoney kun yarda cewa za ku tafi duk inda aka tura ku a duniya,” kuma ƙasar Ireland tana cikin waɗannan wuraren.
Komawa Ireland
Na isa ƙasar Ireland a watan Agusta, a shekara ta 1959, kuma aka aika ni ikilisiyar Dun Laoghaire. A wannan lokacin, Eric ya koma Ingila kuma ya yi farin ciki sosai da yake ina kusa sosai. Shi ma yana son ya zama mai wa’azi a ƙasashen waje. Sai ya yi tunani cewa tun da yake ana aika masu wa’azi a ƙasashen waje zuwa ƙasar Ireland a lokacin, zai yi aikin majagaba a wajen. Sai ya ƙaura zuwa Dun Laoghaire, kuma muka yi aure a shekara ta 1961.
Bayan watanni shida, Eric ya yi mugun hatsari da babur. Ƙoƙon kansa ya ɗan tsage, kuma likitocin ba su sani ba ko za su iya su ceci ransa. Bayan ya yi makonni uku a asibiti, na kula da shi a gida watanni biyar har ya samu sauƙi. Na ci gaba da hidimata iya ƙoƙarina.
A shekara ta 1965 an aika mu zuwa wata ikilisiya da take da masu shela takwas a Sligo, garin da ke arewa maso yammancin gaɓar teku da kuma tashar jirgin ruwa. Bayan shekara uku, mun soma hidima a can arewa, wata ƙaramar ikilisiya a Londonderry. Wata rana mun dawo daga wa’azi sai muka ga cewa an saka waya mai ƙaya a ƙetaren hanya inda muke da zama. Hayaniya ta Arewacin Ireland ta soma. Taron matasa ’yan iska sun ƙone motoci. An riga an raba birnin zuwa gida biyu, Farostatan da Katolika. Yana da haɗari a ƙetare daga ɓangare ɗaya na birnin zuwa wani.
Rayuwa da Wa’azi a Lokacin Hayaniya
Hidimarmu na kai mu ko’ina. Muna ji kamar mala’ikun Jehobah suna kafa sansani kewaye da mu. Idan muna wani wuri kuma aka soma hayaniya, muna barin wurin da sauri kuma mu koma lokacin da komi ya lafa. Wani lokacin da aka yi tarzoma kusa da gidanmu, raguwar abubuwan da aka ƙone daga kantin fenti da ke kusa sun faɗo a kan tagarmu. Ba mu yi barci ba, domin gidanmu na iya kamawa da wuta. Bayan mun ƙaura zuwa garin Belfast a shekara ta 1970, mun ji cewa an jefa bam na man fetur a wannan kanti na fenti kuma gidanmu na dā ya ƙone kurmus a lokacin.
A wani lokaci, ni da wata ’yar’uwa muna wa’azi kuma muka lura cewa da akwai wani bututu da bai kamata ya kasance a kan wani taga ba. Mun ci gaba da tafiya. Mintoci kaɗan abin ya fashe. Mutanen da suka fito suka aza mu ne muka kafa bam ɗin! Nan da nan wata ’yar’uwa da take zama a yankin ta gayyace mu cikin gidanta. Hakan ya sa maƙwabtanta suka ga cewa ba mu da hannu a bam ɗin da ya fashe.
A shekara ta 1971, mun koma garin Londonderry don mu ziyarci wata ’yar’uwa. Sa’ad da muka kwatanta mata hanyar da muka bi, sai ta yi tambaya, “Babu kowa a hanyar ne?” Sa’ad da muka amsa cewa “akwai, amma ba su damu da mu ba,” sai ta yi mamaki. Me ya sa? Domin ’yan kwanaki da suka wuce an kwace kuma an ƙone motar wani likita da kuma na wani ɗan sanda.
A shekara ta 1972, muka koma garin Cork. Bayan haka, mun yi hidima a garin Naas, da kuma Arklow. A ƙarshe, a shekara ta 1987, an aika mu zuwa garin Castlebar, inda muke a yau. A nan mun sami gata mai girma na taimakawa wajen gina Majami’ar Mulki. Eric ya soma rashin lafiya sosai a shekara ta 1999. Duk da haka, da taimakon Jehobah da kuma ikilisiya na iya jimre wa yanayin kuma na kula da shi har ya samu sauƙi.
Ni da Eric mun halarci Makarantar Hidima ta Majagaba sau biyu. Har ila shi dattijo ne. Ina ciwon amosanin gaɓa kuma an yi mini tiyata a ƙugu da duka gwiwoyi na. Ko da yake na fuskanci hamayya na addini mai tsanani kuma na yi rayuwa a lokacin hayaniya na siyasa da jama’a, abu mafi wuya da na fuskanta shi ne, an ce in daina tuƙa mota. Hakan gwaji ne domin ba na zuwa wurare duk lokacin da nake so. Ikilisiya ta taimaka sosai. Ina tafiya yanzu da taimakon sanda, kuma ina amfani da keken guragu mai amfani da batir idan za ni wurare masu nisa.
Ni da Eric mun yi hidima na majagaba na musamman fiye da shekaru ɗari, a cikinsu mun yi shekara tasa’in da takwas a ƙasar Ireland. Ba ma son mu daina wannan aikin don mun tsufa. Ba ma tsammani za a yi mana mu’ujiza, amma mun gaskata cewa mala’ikun Jehobah masu iko suna “kafa sansani a kewaye” da waɗanda suke jin tsoronsa kuma suke bauta masa da aminci.