Jana’iza ta Kirista Mai Daraja, Daidai wa Daida, da ke Faranta wa Allah Rai
ANA jin kuka ko’ina. Masu makoki da suke sanye da baƙaƙen tufafi na musamman suna makoki, suna ta birgima a ƙasa don baƙin ciki. Masu rawa suna ta rawa don kiɗan da ake yi. Wasu kuwa suna ci suna dariya da annashuwa. Wasu suna kwance a ƙasa, sun sha sun bugu don sun sami bammi da giya kyauta. Wane biki ne ake yi? A wasu ɓangarorin duniya, waɗannan abubuwa ne da ake yi a jana’iza inda mutane da yawa suke taruwa don su yi wa wanda ya rasu ban kwana.
Shaidun Jehobah da yawa suna zaune ne a yankunan da dangi da maƙwabta suke camfi sosai kuma suna jin tsoron matattu. Mutane da yawa sun gaskata cewa sa’ad da mutum ya mutu, sai ya zama ruhun kakanni da zai iya taimakon masu rai ko kuma ya yi musu mugunta. Wannan imani yana da alaƙa sosai da al’adun jana’iza da yawa. Hakika, yin makoki game da wanda ya rasu ba laifi ba ne. Akwai lokacin da Yesu da manzanninsa suka yi kukan mutuwar ƙaunatattu. (Yoh. 11:33-35, 38; A. M. 8:2; 9:39) Duk da haka, ba lokacin da suka wuce gona da iri ta wurin yin irin makokin da ake yi a zamaninsu. (Luk 23:27, 28; 1 Tas. 4:13) Me ya sa? Dalili ɗaya shi ne, sun san gaskiya game da mutuwa.
Littafi Mai Tsarki ya faɗa sarai cewa: “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san komi ba ... Ƙaunarsu duk da ƙiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun ƙare ... gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari [na ’yan adam] inda za ka.” (M. Wa. 9:5, 6, 10) Waɗannan hurarrun ayoyi na Littafi Mai Tsarki sun bayyana sarai cewa sa’ad da mutum ya mutu, bai san kome ba kuma. Ba zai iya tunani ba, ba zai ji abu a jikinsa ba, ba zai iya magana ba, ko kuma ya fahimci wani abu. Ta yaya ne fahimtar wannan gaskiyar mai muhimmanci da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta shafi yadda ake yin jana’iza na Kirista?
“Kada Ku Taɓa Kowane Abu Marar-Tsarki”
Ko daga wace ƙabila ko al’ada ce suka fito, Shaidun Jehobah suna guje wa kowace al’ada da ke da alaƙa da imanin cewa matattu sun san abubuwan da ke faruwa kuma suna iya rinjayar masu rai. Al’adu kamarsu kwanan zaune, bukukuwa na jana’iza, tuna lokacin mutuwa, hadayu ga matattu, da kuma bukukuwan gwauranci, ba su da tsarki kuma suna ɓata wa Allah rai domin suna da nasaba da koyarwa ta aljanu wadda ba ta cikin Nassi, wadda ta ce kurwa ko kuma ruhu ba ya mutuwa. (Ezek. 18:4) Kiristoci na gaskiya ba za su “ci daga table na Ubangiji, da na aljanu ba,” saboda haka, ba sa saka hannu cikin waɗannan al’adu. (1 Kor. 10:21) Suna yin biyayya da umurnin nan: ‘Ku ... ware, kada ku taɓa kowane abu marar-tsarki.’ (2 Kor. 6:17) Ba koyaushe ba ne yake da sauƙi mu ware kanmu daga irin waɗannan al’adu ba.
A Afirka da kuma wasu wurare, an gaskata cewa idan ba a yi wasu al’adu ba, ruhun kakanni za su yi fushi. Idan mutum ya ƙi ba da haɗin kai, ana ɗaukan hakan a matsayin mugun laifi da zai iya kai ga la’anta yankin ko kuma ya jawo musu bala’i. Domin sun ƙi su sa hannu cikin bukukuwa na jana’iza da suka saɓa wa Nassi, iyalai ko yankunan da mutanen Jehobah suke da zama sun suki ra’ayinsu sun zage su, kuma sun mai da su bare. An zargi wasu cewa ba sa hulɗa da mutane kuma ba sa daraja matattu. A wasu lokatai, marasa bi sun shirya jana’izar Kirista ƙarfi da yaji. Saboda haka, ta yaya za mu guji yin jayayya da waɗanda suka nace cewa sai an bi al’adu na jana’iza da ke ɓata wa Allah rai? Mafi muhimmanci, menene za mu iya yi don mu ware kanmu daga bukukuwa marar tsarki da kuma ayyuka da za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah?
Ka Bayyana Matsayinka Sarai
A wasu ɓangarorin duniya, al’ada ce dangi da ba sa cikin ainihin iyalin da kuma dattawan iyalin su kasance cikin masu tsai da shawara game da jana’iza. Saboda haka, dole ne Kirista mai aminci ya bayyana sarai cewa Shaidun Jehobah ne za su shirya kuma su za su yi jana’izarsa bisa mizanan Littafi Mai Tsarki. (2 Kor. 6:14-16) Bai kamata abubuwa da suka faru a lokacin jana’izar Kirista ya dami lamirin ’yan’uwa masu bi ba ko kuma ya sa waɗanda suka san imaninmu da kuma abin da muke koyarwa game da matattu yin tuntuɓe.
Sa’ad da aka ce wani wakilin ikilisiyar Kirista ya yi jana’iza, dattawa suna iya ba da shawarwari masu kyau da kuma taimako na ruhaniya domin dukan shirye-shiryen su jitu da ƙa’idodi na Nassi. Idan wasu da ba Shaidu ba suna son su kawo ayyuka marasa kyau, yana da muhimmanci mu yi tsayin daka kuma mu bayyana musu matsayinmu na Kirista a hanya mai kyau kuma da ladabi. (1 Bit. 3:15) Amma idan dangi marasa bi har ila suka nace yin bukukuwa marasa tsarki a jana’izar kuma fa? Iyalin da masu bi ne suna iya tsai da shawarar janye hannu daga cikin jana’izar. (1 Kor. 10:20) Idan hakan ya faru, ana iya ba da jawabin jana’iza a Majami’ar Mulki da ke yankin ko kuma wani wurin da ya dace domin a yi tanadin “ta’aziya” daga Nassi ga waɗanda suke baƙin ciki da gaske don mutuwar wanda suke ƙauna. (Rom. 15:4) Ko da yake babu gawar mamacin a wurin, irin wannan tsarin zai zama mai daraja kuma karɓaɓɓe. (K. Sha 34:5, 6, 8) Idan marasa bi suka saka hannu a hanyar da bai dace ba, hakan na iya jawo ƙarin wahala da baƙin ciki, amma za mu iya samun ta’aziyya da sanin cewa Allah yana ganin ƙudurinmu na yin abin da ya dace, kuma shi ne zai iya ba mu “mafificin girman iko.”—2 Kor. 4:7.
Ka Rubuta Abin da Kake So a Yi
Sa’ad da mutum ya rubuta umurninsa game da shirin jana’izarsa, ya fi sauƙi a tattauna da waɗanda suke cikin iyali da ba Shaidu ba, tun da yake mai yiwuwa za su daraja abin da mamacin yake so. Yana da muhimmanci a rubuta dalla-dalla yadda za a yi jana’izar da kuma inda za a yi hakan, da kuma wanda yake da ainihin hakkin shirya da kuma yin jana’izar. (Far. 50:5) Mafi amfani shi ne takardar da aka sa hannu kuma akwai shaidu. Waɗanda suke shiri don nan gaba da fahimi da kuma hikima da ke bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sun san cewa ba sa bukatar su jira har sai sun tsufa sosai ko kuma suna ciwon ajali kafin su yi hakan.—Mis. 22:3; M. Wa. 9:12.
Wasu ba sa farin cikin rubuta irin wannan umurnin. Amma, yin hakan tabbaci ne cewa mutum Kirista ne da ya manyanta kuma yana ƙaunar waɗansu. (Filib. 2:4) Ya fi kyau mutum ya rubuta waɗannan batutuwan dalla-dalla da kansa maimakon ya bar wa waɗanda suke cikin iyali da suke baƙin ciki su magance su, don ana iya matsa musu su yi na’am da ayyuka marasa kyau da mamacin bai yi imani da su ba kuma bai amince da su ba.
Ka Sa Jana’izar ta Zama Mai Sauƙi
A ɓangarorin Afirka da yawa, an gaskata a ko’ina cewa dole ne a yi jana’iza mai girma da zai burge mutane don kada a sa ruhohin kakanni fushi. Wasu suna amfani da jana’iza don su nuna matsayinsu da tattalin arziki “ta wofi.” (1 Yoh. 2:16) Yana ɗaukan lokaci da aiki tuƙuru kuma ana kashe kuɗi da yawa don a yi wa mamacin jana’izar da ta “dace” a ganinsu. Don mutane su zo da yawa, ana manna babbar takardar sanarwa wadda ke ɗauke da hoton mamacin a wurare dabam dabam, ta haka ana sanar da jana’izar ga jama’a. Ana ɗinka ti-shat da ke ɗauke da hoton mamacin kuma a rarraba wa masu makoki don su saka. Ana sayan akwatin gawa mai tsada sosai don a burge mutane. A wata ƙasar Afirka, wasu suna ƙera akwatin gawa da ya yi kama da mota, jirgin sama, jirgin ruwa, da wasu abubuwa don a nuna arziki, ɗaukaka, da alatu. Ana iya cire gawar daga cikin akwatin kuma a ajiye ta a kan gado da aka yi wa ado mai kyau don a riƙa gani. Idan mace ce ta rasu, ana iya saka mata farin kaya na aure, a yi mata kwalliya kuma a saka mata kayan ado da dutsen wuya. Zai dace mutanen Allah su saka hannu a cikin irin waɗannan ayyukan?
Kiristoci da suka manyanta sun san amfanin guje wa abubuwan da ba su dace ba da mutanen da ba su san ƙa’idodin Allah ba suke yi ko kuma ba sa son su bi ƙa’idodin. Mun san cewa al’adu da ba su dace ba kuma da ba su da tushe na Nassi ‘ba na Uba ba ne, amma na duniya ne da take wucewa.’ (1 Yoh. 2:15-17) Dole ne mu mai da hankali don kada mu soma halin da ba na Kirista ba na yin gasa, wato, yin ƙoƙari mu fi wasu. (Gal. 5:26) Abubuwan da suke faruwa sun nuna cewa idan tsoron matattu sashe ne na musamman na wata al’ada da zaman jama’a, sau da yawa jana’izar tana yin girma kuma tana kasance da wuya a kula da ita kuma ba za a iya ja-gorar ayyukan ba. Bauta wa matattu tana motsa marasa bi su soma yin ayyukan da ba su da kyau. A irin wannan jana’iza, ana yin kururuwa, ana rungumar gawar, ana yi mata magana kamar tana da rai, kuma ana saka kuɗi da wasu kaya wa mamacin. Idan irin waɗannan abubuwa suka faru a jana’iza ta Kirista, hakan zai ɓata sunan Jehobah da mutanensa.—1 Bit. 1:14-16.
Ya kamata sanin yanayin matattu ya ba mu gaba gaɗin yin jana’izarmu ba tare da halin duniya ba. (Afis. 4:17-19) Ko da yake Yesu ne mutum mafi girma kuma mafi muhimmanci da ya taɓa rayuwa a duniya, an binne shi a hanya mai kyau kuma mai sauƙi. (Yoh. 19:40-42) Waɗanda suka san “nufin Kristi” sun san cewa irin wannan jana’iza ce ta fi kyau. (1 Kor. 2:16) Hakika, yin jana’iza mai sauƙi da mutane kaɗan, hanya ce mafi kyau na guje wa ayyuka marar tsarki da ba ta da tushe bisa Nassi kuma a kasance da yanayi na lumana, mai daraja, wanda ya dace da waɗanda suke ƙaunar Allah.
Ya Kamata a Yi Biki Ne?
Bayan jana’izar, al’adar tana iya zama cewa dangi, maƙwabta, da mutane za su taru da yawa don su yi biki kuma su yi rawa ga kiɗe-kiɗe da ake yi. A waɗannan bukukuwa na jana’iza sau da yawa ana maye da kuma ayyukan lalata. Wasu suna da’awar cewa irin waɗannan shagulgula suna kawar da baƙin cikin mutuwa. Wasu kuma suna jin cewa wannan al’adarsu ce. Amma, mutane da yawa sun gaskata cewa dole ne a yi irin waɗannan shagulgula domin a ɗaukaka kuma a yaba wa mamacin kuma a saki kurwar mamacin ta je ta haɗu da ta kakanninsa.
Kiristoci na gaskiya sun san amfanin shawarar Nassi da ta ce: “Bācin rai ya fi dariya: gama ta wurin ɓāta fuska zuciya ta kan gyaru.” (M. Wa. 7:3) Ƙari ga haka, sun san amfanin yin tunani game da rayuwa da ba ta da tsawo da kuma begen tashin matattu. Hakika, a wajen waɗanda suke da dangantaka na kud da kud da Jehobah, ‘ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.’ (M. Wa. 7:1) Saboda haka, da yake sun san cewa shagulgula na jana’iza yana da nasaba da koyarwa na sihiri da kuma ayyukan lalata, shi ya sa bai dace ba Kiristoci na gaskiya su shirya ko kuma su halarci irin waɗannan bukukuwa. Kasancewa tare da masu neman jin daɗi a jana’iza zai nuna rashin daraja ga Allah da kuma lamirin ’yan’uwa masu bi da suke bauta wa Jehobah.
Bari Mutane Su Ga Bambancin
Muna godiya cewa ba ma tsoron matattu, halin da ya zama ruwan dare a tsakanin waɗanda ba su san gaskiya ba! (Yoh. 8:32) A matsayin “’ya’yan haske,” muna yin baƙin ciki da kuka a hanyar da ta nuna cewa muna da wayewa na ruhaniya, a hanya mai kyau kuma mai daraja, da ke cike da tabbataccen bege na tashin matattu. (Afis. 5:8; Yoh. 5:28, 29) Irin wannan begen zai hana yawan makoki da sau da yawa ake gani tsakanin waɗanda “ba su da bege.” (1 Tas. 4:13) Zai ba mu ƙarfin zuciya mu yi tsayin daka ga bauta mai tsarki, ba tare da jin tsoron mutum ba.—1 Bit. 3:13, 14.
Bin ƙa’idodi na Nassi zai ba mutane zarafi su ga bambanci ‘tsakanin waɗanda suke bauta ma Allah da waɗanda ba sa bauta masa.’ (Mal. 3:18) Wata rana, mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba. (R. Yoh. 21:4) Yayin da muke jiran wannan alkawarin ya cika, bari Jehobah ya ga cewa mu marasa aibi ne, marasa laifi, kuma mun ware kanmu gabaki ɗaya daga wannan muguwar duniya da ayyukanta da suke rena Allah.—2 Bit. 3:14.
[Hotunan da ke shafi na 30]
Rubuta abubuwan da muke so a yi lokacin jana’iza tafarki ne na hikima
[Hotunan da ke shafi na 31]
Ya kamata jana’iza na Kiristoci ta kasance daidai wa daida kuma mai daraja