Domin Matasanmu
Yesu Ya Sa Masu Sauraransa Sun Yi Mamaki
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda za ka iya mai da hankalinka wuri ɗaya. Sa’ad da ka ke karanta Nassosi ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KA KARANTA LUKA 2:41-47.
A ganinka waɗanne batutuwa ne ake tattaunawa da aka kwatanta a aya ta 46?
․․․․․
KA YI BINCIKE SOSAI.
Me kake gani ya taimaki Yesu ya tattauna da shugabannin addini tun yana yaro ƙarami haka? Domin shi kamili ne ko kuwa dai domin wani dalili ne?
․․․․․
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN.—KA KARANTA LUKA 2:48-52.
A ganinka, wane irin hali ne Yesu ya nuna sa’ad da ya yi tambaya, “Ina abin da ya sa kuka neme ni?”
․․․․․
Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Yesu bai raina iyayensa ba sa’ad da yake masu magana?
․․․․․
KA YI BINCIKE SOSAI.
Me ya sa Yusufu da Maryamu suka damu ƙwarai?
․․․․․
Ko da yake shi kamili ne, me ya sa Yesu ya ci gaba da yi wa iyayensa biyayya?
․․․․․
Kana gani Yesu ya ji kunya a yi masa gyara a gaban mutanen da suke yaba masa?
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Yin biyayya.
․․․․․
Amfanin samun ilimin Littafi Mai Tsarki sa’ad da mutum yake yaro.
․․․․․
WAƊANNE BANGARORIN WANNAN LABARI NE YA FI MA’ANA A GARE KA KUMA ME YA SA?
․․․․․