Abin Da Muka Koya Daga Yesu
Game da Mulkin Allah
Menene Mulkin Allah?
Mulkin Allah gwamnati ce da za ta yi mulki bisa dukan duniya. Yesu ya ce: “Da hakanan fa za ku yi addu’a: . . . Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Matta 6:9, 10; Daniel 2:44.
Su wanene za su yi sarauta a Mulkin Allah?
An haifi Yesu ne don ya zama wanda zai yi Sarauta a Mulkin Allah. Wani mala’ika ya gaya wa mahaifiyar Yesu cewa: “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki.” (Luka 1:30-33) Bugu da ƙari, Yesu ya zaɓi wasu a cikin mabiyansa su yi sarauta da shi. Ya gaya wa manzanninsa: “Ku ne waɗanda kun lizimce ni a cikin jarabtuwana; ni ma na sanya maku mulki, kamar yadda Ubana ya sanya mani.” (Luka 22:28, 29; Daniel 7:27) Mabiyan Yesu su 144,000 ne za su yi sarauta tare da shi.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1.
A ina ne gwamnatin za ta kasance?
Mulkin Allah zai yi sarauta ne daga sama. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Kadan na tafi na shirya muku wuri kuma [a sama], sai in sake dawowa, in karɓe ku wurin kaina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma . . . domin ina tafiya wurin Uban.”—Yohanna 14:2, 3, 12; Daniel 7:13, 14.
Menene Mulkin Allah zai yi game da mugunta?
Yesu zai kawar da mugayen mutane daga duniya. Yesu ya ce: “Sa’anda Ɗan mutum [Yesu] za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna . . . Waɗannan [marar adalci] kuwa za su tafi cikin hukunci na har abada: amma masu-adalci cikin rai na har abada.”—Matta 25:31-34, 46.
Su wanene za su zauna a duniya a matsayin talakawan Mulkin?
Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Matta 5:5; Zabura 37:29; 72:8) Duniya za ta cika da mutanen da a yanzu suna ƙaunar juna. Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yohanna 13:34, 35.
Menene Mulkin Allah zai yi wa mutane a duniya?
Yesu zai warkar da dukan cutar da ke damun mutane. Sa’ad da yake duniya, Yesu ya gaya wa taro “zance a kan mulkin Allah; waɗanda su ke bukatar warkaswa kuma, ya warkadda su.” (Luka 9:11) Bayan ya ga Yesu da aka ta da daga matattu a wahayi, manzo Yohanna ya ce: “Na ga sabuwar sama da sabuwar duniya kuma: . . . Na ji babbar murya kuwa daga cikin kursiyin, ta ce, Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, . . . za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.
Mulkin Allah zai mai da duniya ta zama Aljanna. Wani mai laifi da aka kashe tare da Yesu ya ce: “Yesu, ka tuna da ni lokacinda ka shiga mulkinka.” Kuma Yesu ya ce masa: “Gaskiya ina ce maka, yau kana tare da ni cikin Paradise.”—Luka 23:42, 43; Ishaya 11:4-9.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 8 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.