Ka Sani?
A Afisawa 2:11-15, manzo Bulus yana yin nuni ne ga bango na zahiri sa’ad da yake maganar bangon da ya raba Yahudawa da ’yan Al’ummai?
Sa’ad da yake rubuta wannan wasiƙar ga Afisawa, manzo Bulus ya ambata bambancin da ke tsakanin Isra’ilawa da “baƙi.” Ya ce akwai “bango” da ya ‘raba’ rukunonin biyu daga juna. (Afisawa 2:11-15) Bulus yana nuni ne ga “shari’a ta dokoki” da aka bayar ta hanyar Musa, amma kalmar nan “bango” da ya yi amfani da ita wataƙila ta tuna wa masu karatu bangon dutse da ya taɓa wanzuwa.
A ƙarni na farko A.Z., haikalin Jehobah da ke Urushalima yana da farfajiya masu yawa da wasu mutane ne kawai suke da ikon shiga. Kowa zai iya shiga Farfajiyar Al’ummai, amma Yahudawa da shigaggu ne kawai suke da ikon shiga farfafajiyar da ke cikin haikali. Wani bango mai tsawo da aka yi da dutse mai suna Soreg ne ya raba farfajiyar da kowa ke shiga da kuma waɗanda wasu ne kawai suke da ikon shiga, kuma an ce tsawonsa ya kai kafa huɗu. In ji ɗan tarihi Bayahude na ƙarni na farko mai suna Flavius Josephus, an manne rubuce-rubucen da aka yi da yaren Helenanci da kuma Latin a jikin wannan bangon, wanda ke ɗauke da gargaɗin da aka yi wa ’yan Al’ummai cewa kada su wuce bangon don kada su shiga wuri mai tsarki.
An gano wani cikakken rubutun da aka yi da yaren Helenanci a jikin wannan bangon da ya raba wuraren nan. Ya ce: “Kada wani baƙo ya wuce bangon da aka kewaye wuri mai tsarki da shi. Duk wanda aka kama zai ɗauki alhakin mutuwarsa.”
Wataƙila Bulus ya yi amfani da Soreg ne ya wakilci alkawarin Dokar Musa, wadda ta raba Yahudawa da ’yan Al’ummai tun da daɗewa. Mutuwar haɗayar da Yesu ya yi ta kawar da alkawarin Dokar kuma ta ‘rushe bango mai-rabawa da ke tsakani.’
Me ya sa ake yawan ambata ƙabilu 12 na Isra’ila, yayin da ƙabilu 13 ne ke akwai?
Ƙabilu, ko kuwa iyalin Isra’ila sun fito ne daga ’ya’yan Yakubu, wanda aka canja sunansa zuwa Isra’ila. Wannan uban iyalin yana da ’ya’ya 12—Reuben, Saminu, Lawi, Yahuda, Dan, Naphtali, Gad, Asher, Issachar, Zebulun, Yusufu da kuma Benyamin. (Farawa 29:32–30:24; 35:16-18) Sha ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwan suna da ƙabilun da ke ɗauke da sunansu, amma babu ƙabilar da ke ɗauke da sunan Yusufu. Maimakon haka, an sanya wa ƙabilu biyu sunayen ’ya’yansa, Ifraimu da Manassa, kuma an ɗauki kowannensu a matsayin shugaban ƙabila. Saboda haka, ƙabilu 13 ne ke Isra’ila. Amma, me ya sa Littafi Mai Tsarki yake ambata ƙabilu 12?
A cikin Isra’ilawa, an ware mazan da ke ƙabilar Lawi su yi hidima a mazaunin Jehobah kuma daga baya a haikali. Da haka, an cire su daga aikin soja. Jehobah ya gaya wa Musa: “Sai kabilar Levi kaɗai ba za ka ƙididiga su ba, ba kuwa za ka lissafta yawansu a cikin ’ya’yan Isra’ila ba: amma ka sanya Leviyawa a bisa mazaunin shaida, da bisa dukan kayansa, da dukan abin da ya tabata gareshi.”—Litafin Lissafi 1:49, 50.
Ba a ba Lawiyawa yankuna a Ƙasar Alkawari ba. Maimakon haka, an saka su a birane dabam dabam guda 48 a yankin Isra’ila.—Litafin Lissafi 18:20-24; Joshua 21:41.
Saboda waɗannan dalilan biyu, ba a saka ƙabilar Lawi a cikin jerin sauran ƙabilun ba. Shi ya sa aka ce ƙabilun Isra’ila su sha biyu ne.—Litafin Lissafi 1:1-15.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 27]
Archaeological Museum of Istanbul