Ka Sani?
Me ya sa Yesu ya warkar da Makaho da sannu-sannu?
A Markus 8:22-26, mun karanta cewa Yesu ya warkar da Makaho a Baitsaida. Labarin ya nuna cewa Yesu ya tofa wa idanun mutumin yau sai ya tambaye shi me yake gani. Amsar mutumin ta nuna cewa ya ɗan rikice: “Ina duban mutane; gama ina ganinsu kamar itatuwa; suna yawo.” Sai Yesu ya sake taɓa idanun mutumin ga abin da ya faru: “Shi ma ya kafa ido, aka warkadda shi, ya ga kome sarai.” A bayyane yake cewa Yesu ya warkar da mutumin ne da sannu-sannu. Me ya sa?
Littafi Mai Tsarki bai ba da cikakkiyar amsa ba, amma za mu iya yin la’akari da abin da wataƙila shi ne dalili wannan yanayi. Sake gani bayan mutum ya kasance makaho na shekaru masu yawa, wataƙila ma dukan rayuwarsa, canji ne ƙwarai a rayuwarsa. Alal misali: Ƙuru da ake amfani da su wajen tonon arzikin ƙasa. Sukan saba da duhu a cikin kogo da sa’ad da suka fito wajen sai su bukaci rana guda domin su yi gyara su saba da hasken rana. Ga makaho gyara da zai yi zai fi ma haka. A zamanin yau, likitoci masu tiyata a wasu lokatai sai su yi tiyata su gyara wata matsala a idanun makaho su mai da masa iya ganin gari. Amma, yawan abubuwa da suke gani da idanunsu da suke shiga ƙwaƙwalwa ta dame su. Domin suna mamakin launi, tsari, da kuma wasu abubuwa da suka gani, sai su ruɗe su kasa gane abin da suka saba da shi. Bayan ɗan lokaci sai ƙwaƙwalwa ta fara gane abin da idanu suka gani.
Warkar da wannan makaho sannu-sannu da Yesu ya yi zai iya kasancewa nuna damuwa ne ga wannan mutumin. A ƙarshe, mutumin “ya ga kome sarai” ya fahimci abin da yake gani.
Me ya sa a zamanin Yesu karatu daga littafin da ake naɗe wa yake da wuya ƙwarai?
Tsawon yawancin fallen da ake haɗawa su zama littafin inci 9 ne zuwa 11, faɗinsa kuma inci 6 zuwa 9. Ana haɗa irin waɗannan fallen ne da danƙo ko kuma a ɗinka su da zaren auduga. A wasu yanayi, ana amfani da falle masu tsawo. Dead Sea Scroll (Littafi da ake naɗewa na Ishaya da aka tsinta a wuraren Tekun Gishiri) an haɗa falle 17 ne da tsawonsu ya kai ƙafa 24 a yadda suke a yau. Littafin Ishaya da Yesu ya yi amfani da shi a majami’a a Nazarat wataƙila tsawonsa ya yi daidai da wannan.— Luka 4:16, 17.
Game da wannan, Alan Millard ya ce a littafinsa Discoveries From the Time of Jesus: “Mai karatu zai riƙe littafin ya warware shi da hannunsa na hagu, ya riƙe inda ya ware da hannunsa na dama ya rika naɗewa sa’ad da yake karatu. Domin mutum ya karanta Ishaya sura 61, wato surar da Yesu ya karanta a majami’a, yana bukatar ya warware yawancin littafin bayan haka kuma ya naɗe shi.”
A wannan lokacin, ba a raba littafin Ishaya zuwa surori da ayoyi ba kamar yadda yake a yau. Sa’ad da aka bai wa Yesu littafin Ishaya a Nazarat, ana bukatar ya nemi wurin da aka ba shi lamba, Ishaya 61:1, 2 a Littafi Mai Tsarki namu. Da yake Yesu ya “sami wurin ba wuya” ya nuna cewa ya san Kalmar Allah.