Ka Sani?
Menene girman kwatarniyar da ke haikalin Sulemanu?
Labarin da ke 1 Sarakuna 7:26 ya ce kwatarniyar tana cin garwar ruwa “dubu biyu” wanda firistoci suke amfani da shi, amma wani labarin kuma na wannan kwatarniyar haikali da ke rubuce a 2 Labarbaru 4:5 ya ce yana cin garwar ruwa “guda dubu uku.” Hakan ya sa wasu mutane suka yi da’awar cewa wannan ya faru ne saboda kuskuren da marubucin labarin Labarbaru ya yi.
Amma, fassarar Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu fahimci yadda waɗannan ayoyin suka yi daidai. 1 Sarakuna 7:26 ta ce: ‘Takan ci garwa dubu biyu.’ Amma, 2 Labarbaru 4:5 ta ce: ‘Kamar kuma siffar furen bi-rana. Kwatarniya kuwa tana iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa.’ 2 Labarbaru 4:5 ta nuna yawan garwar ruwan da kwatarniyar haikalin za ta iya ɗauka gabaki ɗaya, amma 1 Sarakuna 7:26 ta faɗi yawan ruwan da ake zubawa cikin kwatarniyar haikalin. A wata sassa kuma, ba a taɓa cika kwatarniyar da ruwa ba maƙil. Kamar dai suna zuba garwar ruwa guda 2,000 ne kawai a cikin kwatarniyar.
Me ya sa Yesu da Bitrus suka biya haraji na haikali da shekel guda kawai?
A zamanin Yesu, kowane namiji Bayahude da ya wuce shekara 20 yana bukatar ya biya shekel biyu don haraji na haikali kowace shekara. Wannan ya yi daidai da kuɗin aiki na kwana biyu. Sa’ad da tambaya ta taso game wannan harajin, sai Yesu ya ce wa Bitrus: “Je ka wurin teku, ka jefa ƙugiya, ka ɗauki kifi wanda ya fara tasowa; sa’anda ka buɗe bakinsa, za ka iske shekel guda: ka ɗauka, ka ba su dominmu, da ni da kai.”—Matta 17:24-27.
Yawancin masana sun gaskata cewa shekel ɗin da aka ambata a nan shi ne wanda ake kira tetradrachma. Wannan shekel ɗin ya yi daidai da shekel guda huɗu, ko kuma harajin haikali na mutane biyu. An fi samun Tetradrachama fiye da didrachma, wato, shekel biyu. Littafin nan The New Bible Dictionary ya faɗi cewa: “Kamar dai Yahudawa suna haɗuwa su biya harajin Haikali na mutane biyu.”
Ƙari ga haka, duk wanda yake son ya canja kuɗi don ya biya haraji na mutum ɗaya yana bukatar ya biya abin da ake kira agio, wato, ɗan kuɗin da ake biya na canja kuɗi. Kuɗin da zai biya zai kai kashi takwas na adadin kuɗin da yake son ya canja. Amma, waɗanda suka biya na mutane biyu a lokaci ɗaya ba za su biya wannan kuɗin ba. Saboda haka, a cikin wannan ɗan bayanin, labarin da ke cikin Matta ya jitu da abubuwan da ake yi a zamanin Yesu.
[Hoto a shafi na 27]
Kobon tetradrachma da aka faɗaɗa