Masu Karatu Sun Yi Tambaya
Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Amfani Da Alamar Gicciya Wajen Bauta?
Shaidun Jehobah sun yi imani ƙwarai cewa mutuwar Yesu Kristi ta yi mana tanadin fansa da ta buɗe zarafin samun rai madawwami ga waɗanda suka ba da gaskiya a gare shi. (Matta 20:28; Yohanna 3:16) Amma, ba su yarda ba cewa Yesu ya mutu a kan gicciya, kamar yadda ake yawan zanawa a kan hotuna. Sun yi imani da cewa Yesu ya mutu ne a kan gungume da ba a gicciye ba.
Shekaru dubu biyu kafin zuwan Kristi ana amfani da gicciya a Mesopotamiya. Wasu mutane a Ture sun sassaƙa alamun gicciya a kan duwatsu a Zamanin Jan ƙarfe, shekaru ɗarurruwa kafin a haifi Yesu. Arna sun yi amfani da gicciya “Alama sihiri ce . . . da take ba da kāriya, da sa’a,” haka Sven Tito Achen, ɗan tahiri kuma ƙwararren masani kan alamu, ya rubuta a littafinsa Symbols Around Us (Alamu da Suke Tare da Mu). Ba abin mamaki ba ne da littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “An sami alamar gicciya a aladu kafin zuwan Kiristanci da kuma a aladu da ba na Kirista ba, wanda alama ce ta sararin samaniya ko kuma wasu abubuwa da suke sama.” To, me ya sa coci suka zaɓi alamar gicciya ta zama alamarsu mafi tsarki?
W. E. Vine, wani malami mai martaba ɗan Britaniya, ya ba da wannan dalilin: “A tsakiyar ƙarni na 3 A.Z., . . . an karɓi arna cikin coci . . . kuma an ƙyale su da alamun abubuwan bautarsu na arnanci. Saboda haka aka ɗauki wannan baƙi T, . . . mai gicciya a tsakiya.”—Vine’s Expository Dictionary of Old and New Testament Words.
Vine ya kuma kula cewa kalmar suna “gicciya” da kuma ta aikatau “gicciye” suna nufin “gungume ne . . . da ya bambanta da wanda coci suka yarda da shi wanda aka gicciye.” Domin ya yarda da hakan, Oxford University’s Companion Bible ya ce: “Tabbaci ya nuna cewa . . . an kashe Ubangiji a kan miƙaƙƙen gungume ne, ba gumagumai biyu da aka gicciya ba.” A bayyane yake cewa coci sun karɓi al’ada da ba ta Littafi Mai Tsarki ba.
Achen ɗan tarihin nan da aka yi ƙaulinsa a baya, ya ce: “Cikin ƙarnuka biyu bayan mutuwar Yesu ba tabbaci cewa Kiristoci sun yi amfani da alamar gicciya.” Ga waɗannan Kiristoci na dā, in ji shi, gicciya, “alamar mutuwa ce da mugunta, kamar yadda wajen sare kai ko kuma kujeran kisa da wutar lantarki suke ga mutanen zamani.”
Mafi muhimmanci ma shi ne, ko da wane irin abu aka yi amfani da shi aka gana wa Yesu azaba kuma aka kashe shi, bai kamata siffarsa ya zama abin bauta ba ga Kiristoci. Littafi Mai Tsarki ya ba da umurni cewa: “ku guje ma bautar gumaka.” (1 Korinthiyawa 10:14) Yesu kansa ya ba da alama da za ta nuna mabiyansa na gaskiya. Ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yohanna 13:35.
Game da dukan wani batu na bauta, Shaidun Jehobah, kamar Kiristoci na ƙarni na farko, suna ƙoƙari su bi Littafi Mai Tsarki maimakon al’ada. (Romawa 3:4; Kolossiyawa 2:8) Domin wannan, ba sa amfani da alamar gicciya wajen bauta.
[Hoto a shafi na 30]
Siffa da take nuna alaman arne sarkin Assuriya yana sanye da gicciya, akalla shekara ta 800 K.Z.
[Inda aka Dauko]
Hoto da wajen matattarin kayan al’ada na Britaniya ta ɗauka