Masu Karatu Sun Yi Tambaya
A Ina Ne Za A Yi Yaƙin Armageddon?
Yaƙin Armageddon ba za a yi shi a wani fili takamaimai na yaƙi ba. Maimakon haka, dukan duniya ce za ta kasance filin yaƙin. Me ya sa? Domin abokan gaban biyu suna da yawa da babu wani wuri guda da zai ishe su duka.
Armageddon, ko kuma Har–Magedon, shi ne “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” Jehobah Allah zai yi amfani da Ɗansa, Yesu Kristi, ya tara dakaru na mala’iku su yaƙi dakarun dukan miyagun sarakuna na duniya.—Ru’ya ta Yohanna 16:14; 19:11-16.
Dakarun Shaiɗan suna rinjayar al’ummai su shiga wannan yaƙin. Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “ruhohin aljanu ne su, masu-aika alamu; suna kuwa fita zuwa wurin sarakunan dukan duniya, garin su tattara su zuwa . . . wurin da a ke ce da shi da Ibrananci Har–Magedon.”—Ru’ya ta Yohanna 16:14-16.
Fiye da dukan wani littafi na Littafi Mai Tsarki Ru’ya ta Yohanna ta sa mutane da yawa masu karatun Littafi Mai Tsarki tunani. Waɗanda suka ga ya kamata a ɗauki abin da aka karanta a zahiri sun nuna wani wuri da suka gaskata cewa a nan za a fara yaƙin, kuma sun zuba idanu wurin suna lura da yadda abubuwa suke faruwa a wannan yanki. An sami ra’ayin da wai Armageddon yana nufin wuri ne takamaimai a bayanin Helenanci bisa Ru’ya ta Yohanna da Oeconomus ya rubuta a ƙarni na shida K.Z.
Da yake magana game da ra’ayin yawancin mutane tsakain masu tsattsauran ra’ayi wani shugaban addini, John F. Walwoord, shugaban makarantar koyar da addina na Dallas na dā, ya ce Armageddon “yaƙi ne na ƙarshe na rashin bege na duniya da za a yi a Gabas ta Tsakiya.” Walwoord ya nuna ainihin wurin da za a yi wannan yaƙin yana cewa wannan yaƙi na nan gaba zai kasance ne a birni na dā na Megiddo, inda da tudu mai tsawon ƙafa 70 kuma da ƙwari.
Amma littafin Ru’ya ta Yohanna ba taswira ba ce ta zuwa wani wuri na zahiri da ake kira Armageddon. Kalmomin farko na littafin sun ce an bayar da shi ne cikin “alamu.” (Ru’ya ta Yohanna 1:1) Shaidun Jehobah da daɗewa sun ce a Littafin su Studies in the Scriptures Littafi na 4: “Ba za mu yi tsamanin za a tara mutane a zahiri zuwa Tudun Megiddo a zahiri ba.”
A tarihi Megiddo ya nuna wurin ne da babu hanyar tsira, ga abokan gaban Allah. Saboda haka, a Armageddon, Allah zai tabbata cewa dukan lalata da mugunta ko da a ina ne aka same su a wannan duniyar, an halaka su.—Ru’ya ta Yohanna 21:8.
Masu ƙaunar Jehobah Allah da Ɗansa Yesu Kiristi, ba sa bukatar su ji tsoron Armageddon. Yaƙin da Allah zai yi ne da mutane da ya zartar da sheri’a a kansu cewa miyagu ne. Yaƙin zai zaɓi waɗanda zai halaka. “Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa,” in ji Littafi Mai Tsarki. (2 Bitrus 2:9) Wani alkawari mai daɗaɗa rai a Zabura 37:34 ya ce: “Ka yi sauraro ga Ubangiji, ka kiyaye tafarkinsa, shi kuma za ya ɗaukake ka ka gaji ƙasan: Lokacinda an datse miyagu, ka gani.”