Masu Karatu Sun Yi Tambaya
Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Wahala?
Ba Allah ba ne ya sa ’yan adam suke shan wahala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Daɗai Allah shi yi mugunta!” (Ayuba 34:10) To, wanene ainihi yake jawo wahala?
Yesu ya kira Shaiɗan “sarkin duniya.” (Yohanna 14:30) Hakika, Jehobah ne Mamallakin Dukan Halitta. Ba zai taɓa barin wannan matsayin ba. Amma, Allah ya ƙyale Shaiɗan ya yi sarautar yawancin ’yan adam na ɗan lokaci.—1 Yohanna 5:19.
Wane irin sarki ne Shaiɗan? Tun lokaci na farko da ya sadu da ’yan adam, Shaiɗan ya zama mai kisan kai da maƙaryaci. Shaiɗan ya jawo wa mutane matsaloli a hanyoyi masu yawa. Yesu ya kira shi da waɗannan kalmomin: “Shi mai-kisan kai ne tun daga farko, ba ya tsaya a kan gaskiya ba, domin babu gaskiya a cikinsa. Sa’anda ya ke yin ƙarya, don kansa ya ke yi: gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.” (Yohanna 8:44) Yesu ya kuma ce mutane da suke neman su kashe shi ’ya’yan mai kisan kai na farko ne. Sun mai da kansu ’ya’yansa ta wajen yin yadda yake yi. Shi ya sa wani karin magana ya ce, barewa ba ta haihuwa ɗanta ya yi rarrafe.
Har ila Shaiɗan yana shuka halayen mugunta a zukatan ’yan adam. Alal misali, farfesa R. J. Rummel da ke Jami’a na Hawaii a Amirka ya ce daga shekara ta 1900 zuwa 1987, gwamnatoci sun kashe mutane 169,198,000 a lokacin kawar da wani gwamnati, kisan ƙare-dangi, da kuma kashe mutane ba dalili. Wannan ya haɗa da biliyoyin mutanen da aka kashe a bakin daga a cikin waɗannan shekarun.
Idan ba Allah ba ne yake haddasa wahala, me ya sa ya ƙyale ta? Domin ana bukatar a sasanta batutuwan da suka shafi dukan mutanen da ke duniya da kuma abu mai kyau da marar kyau da aka ta da tun da daɗewa. Bari mu tattauna ɗaya kawai a cikinsu.
A somawar tarihin ’yan adam, Adamu da Hauwa’u sun bi Shaiɗan. Sun ƙi sarautar Allah kuma suka zaɓi gwamnatin kansu da Iblis ke sarautarsa.—Farawa 3:1-6; Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Mizanan Jehobah na adalci na bukatar a ba da lokaci don a samu isashen tabbaci. Menene hakan ya tabbatar? Sarautar ’yan adam a ƙarƙashin ikon Shaiɗan tana jawo wahala ne kawai. Hakika, dogon lokacin da Allah ya ba da ya amfane ’yan adam. Ta yaya? Waɗanda suka yi nazarin tabbacin kuma suka gaskata da shi sun nuna cewa suna son Allah ya shugabance su. Waɗanda suka koya game da mizanan Allah kuma suka yi rayuwar da ta jitu da su suna da begen yin rayuwa har abada.—Yohanna 17:3; 1 Yohanna 2:17.
Hakika, a yanzu duniya tana ƙarƙashin ikon Shaiɗan. Amma hakan ba zai daɗe ba. Ba da daɗewa ba Jehobah zai yi amfani da Ɗansa ya “halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yohanna 3:8) A ƙarƙashin ja-gorar Allah, Yesu zai gyara karyayyen zukata kuma ya mai do wa mutane yanayi mai kyau. Zai dawo da biliyoyin mutanen da suka sha wahala kuma suka mutu duk cikin tarihin ’yan adam.—Yohanna 11:25.
Tashin da Yesu ya yi daga matattu misali ne cewa Allah ya yi nasara bisa ayyukan Iblis, wannan ƙaramin abu ne idan aka gwada shi da abin da ’yan adam da suka zaɓi sarautar Allah za su samu. (Ayukan Manzanni 17:31) Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu fahimci yadda wannan lokacin zai kasance da waɗannan kalmomin masu ban ƙarfafa: “Allah kuma da kansa za ya zauna tare da [’yan adam], ya zama Allahnsu: za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.