Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 11/1 pp. 13-17
  • Ka Bi Abin Da Lamirinka Ya Ce

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bi Abin Da Lamirinka Ya Ce
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Waɗanda Lamirinsu ya Ƙazamtu
  • Tsabta “Ga Masu-Tsabtan Rai”
  • Lamiri da Shawarwari da Suka Bambanta
  • Ta Yaya Za Ka Kasance da Lamiri Mai Kyau?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Mu Bauta wa Allah da Zuciya Mai Tsabta
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Lamirinka Yana Yi Maka Ja-gora da Kyau Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Saurari Lamirinka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 11/1 pp. 13-17

Ka Bi Abin Da Lamirinka Ya Ce

“Ga masu-tsabtan rai dukan abu da tsabta ya ke: amma ga waɗanda ke ƙazamtattu da marasa-bangaskiya babu abin da ke da tsabta.”—TITUS 1:15.

1. Menene ya haɗa Bulus da ikilisiyoyin da ke Karita?

BAYAN da manzo Bulus ya ƙarasa tafiye tafiyensa na wa’azi a ƙasashen waje sau uku, an kama shi kuma aka aika shi zuwa Roma inda aka tsare shi shekara biyu. Menene ya yi sa’ad da aka sake shi? Bayan an sake shi, shi da Titus sun ziyarci tsibirin Karita, kuma Bulus ya rubuta masa cewa: “Na bar ka cikin Karita, domin ka daidaita al’amuran da suka tauye, ka kafa dattiɓai.” (Titus 1:5) Wannan aikin da Titus zai yi ya ƙunshi bi da mutanen da lamirinsu ya bambanta.

2. Wace matsala ce Titus zai bi da ita a tsibirin Karita?

2 Bulus ya gargaɗi Titus game da abin da zai sa mutum ya cancanta ya zama dattijo a ikilisiya, sai kuma ya nuna cewa akwai “mutane dayawa masu-ƙin hukunci, masu-maganar banza, masu-ruɗi.” Waɗannan suna “jirkitadda gidaje ɗungum, suna koyarda abin da ba ya kamata ba.” Titus zai ci gaba da “tsauta musu.” (Titus 1:10-14; 1 Timothawus 4:7) Bulus ya ce zuciyarsu da lamirinsu sun “ƙazantu,” ya yi amfani da kalmar da ke nufin ɓatawa kamar yadda bula za ta iya ɓata kaya mai kyau. (Titus 1:15) Wataƙila wasu cikin waɗannan mutanen Yahudawa ne, domin sun ‘manne wa yin kaciya.’ Babu irin waɗannan mutanen da suke da wannan ra’ayin a cikin ikilisiyoyi a yau; duk da haka za mu iya koyan abubuwa da yawa game da lamiri daga gargaɗin da Bulus ya yi wa Titus.

Waɗanda Lamirinsu ya Ƙazamtu

3. Menene Bulus ya rubuta wa Titus game da lamiri?

3 Ka lura da yanayin da Bulus ya ambata lamiri. “Masu-tsabtan rai dukan abu da tsabta ya ke: amma ga waɗanda ke ƙazamtattu da marasa-bangaskiya babu abin da ke da tsabta; amma hankalinsu duk da lamirinsu sun ƙazantu. Suna shaida, cewa, sun san Allah; amma ta wurin ayyukansu sun yi musunsa.” Babu shakka, wasu a lokacin suna bukatar su yi canje-canje domin su “zama sahihai cikin imani.” (Titus 1:13, 15, 16) A bayyane yake cewa wasu a lokacin suna bukatar su yi gyara domin su “zama sahihai cikin imani.” (Titus 1:13, 15, 16) Suna da matsala wajen bambanta abin da yake da tsabta da marar tsabta, kuma wannan ya ƙunshi lamirinsu.

4, 5. Wane aibi ne wasu a cikin ikilisiyoyi suke da shi, kuma ta yaya hakan ya shafe su?

4 Shekaru goma kafin ya rubuta wannan wasiƙar, hukumar mulki ta kammala cewa ba a bukatar a yi wa mutum kaciya don ya zama mai bauta ta gaskiya, kuma ta sanar da ikilisiyoyin. (Ayukan Manzanni 15:1, 2, 19-29) Duk da haka, wasu a Karita suna ‘manne wa kaciya.’ Sun ƙi su ba da haɗin kai da hukumar mulki, kuma “suna koyarda abin da ba ya kamata ba.” (Titus 1:10, 11) Da yake suna da ra’ayin da bai dace ba, mai yiwuwa suna ɗaukaka farillai daga Doka game da abinci da bukukuwa na tsabta. Wataƙila sun ƙara wa Dokar gishiri kamar yadda kakaninsu a zamanin Yesu suka yi, kuma suna ɗaukaka almarar Yahudawa da dokokin mutane.—Markus 7:2, 3, 5, 15; 1 Timothawus 4:3.

5 Irin wannan ra’ayin yana da lahani ga tunaninsu da lamirinsu. Bulus ya rubuta: “Ga waɗanda ke ƙazamtattu da marasa-bangaskiya babu abin da ke da tsabta.” Lamirinsu ya zama matacce da ba zai iya ba su matabbacin ja-gora ga ayyukansu da kuma tunaninsu ba. Bugu da ƙari, suna shara’anta Kiristoci masu bi a kan batutuwan da suka shafe su kaɗai, a kan al’amura da wani Kirista zai tsai da shawara dabam kuma wani zai yi zaɓi dabam. Shi ya sa mutanen Karita suka ɗauki abubuwan da ke da tsabta a matsayin marar tsabta. (Romawa 14:17; Kolossiyawa 2:16) Yayin da suke da’awar cewa sun san Allah, ayyukansu bai nuna hakan ba.—Titus 1:16.

Tsabta “Ga Masu-Tsabtan Rai”

6. Waɗanne mutane iri biyu ne Bulus ya ambata?

6 Ta yaya za mu amfana daga abin da Bulus ya rubuta wa Titus? Ka lura da bambancin da ke cikin wannan furcin: “Ga masu-tsabtan rai dukan abu da tsabta ya ke: amma ga waɗanda ke ƙazamtattu da marasa-bangaskiya babu abin da ke da tsabta.” (Titus 1:15) Ba wai Bulus yana cewa kome yana da tsabta kuma ya dace ga Kirista mai tsabtan ɗabi’a ba ne. Mun tabbata da hakan domin Bulus ya bayyana sarai a cikin wata wasiƙa cewa waɗanda suke fasikanci, bautar gunki, sihiri da sauransu “ba za su gaji mulkin Allah ba.” (Galatiyawa 5:19-21) Saboda haka dole ne mu kammala cewa Bulus yana magana ne game da mutane iri biyu, masu tsabta a ɗabi’a da ruhaniya da kuma waɗanda ba su da tsabta.

7. Menene Ibraniyawa 13:4 ta ce kada a yi, kuma wace tambaya za a iya yi?

7 Wannan ba ya nufin cewa abubuwan da ainihi Littafi Mai Tsarki ya hana ne kawai ya kamata Kiristoci na gaskiya su guje su. Alal misali, ka yi la’akari da wannan furci na kai tsaye: “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane, gado kuma shi kasance mara-ƙazanta: gama da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” (Ibraniyawa 13:4) Waɗanda ba Kiristoci ba ne da kuma waɗanda ba su san kome ba game da Littafi Mai Tsarki za su kammala cewa wannan ayar ta hana yin zina. A bayyane yake a cikin wannan ayar da wasu ayoyi cikin Littafi Mai Tsarki cewa Allah ba ya son namiji da yake da aure ya yi jima’i da wadda ba matarsa ba ko kuma mata mai aure ta yi hakan. Mutane biyu da ba su yi aure ba amma suna tsotsar al’aurar juna fa? Matasa da yawa suna da’awar cewa hakan ba shi da lahani domin ba jima’i ba ne. Ya kamata Kirista ya ɗauki tsotsar al’aura abu mai tsabta ne?

8. Idan ya zo ga batun tsotsar al’aura, ta yaya Kiristoci suka bambanta da mutane da yawa a duniya?

8 Ibraniyawa 13:4 da 1 Korinthiyawa 6:9 sun nuna cewa Allah ya hana kwartanci da fasikanci (Helenanci, por·neiʹa). Menene fasikanci ya ƙunsa? Kalmar nan ta Helenanci ta ƙunshi yin amfani da al’aura yadda ainihi ake amfani da ita ko kuma a wata hanyar dabam don yin lalata. Ta haɗa da dukan hanyoyin yin jima’i da aka haramta tsakanin waɗanda ba su auri juna ba. Saboda haka, ta ƙunshi tsotsar al’aura, ko da yake an gaya wa matasa da yawa a dukan duniya ko kuma su da kansu sun amince cewa tsotsar al’aura ba laifi ba ne. Kiristoci na gaskiya ba sa barin ra’ayin “masu-maganar banza, masu-ruɗi” su ja-goranci tunaninsu da kuma ayyukansu. (Titus 1:10) Suna manne wa mizani mai girma na Littafi Mai Tsarki. Maimakon su yi ƙoƙari su nemi hujjar tsotsar al’aura, sun fahimci cewa hakan fasikanci ne ko por·neiʹa bisa abin da Nassi ya faɗa, kuma sun koyar da lamirinsu kada su amince da wannan lalata.a—Ayukan Manzanni 21:25; 1 Korinthiyawa 6:18; Afisawa 5:3.

Lamiri da Shawarwari da Suka Bambanta

9. Idan “dukan abu da tsabta ya ke,” menene amfanin lamiri?

9 Amma, menene Bulus yake nufi sa’ad da ya ce “masu-tsabtan rai dukan abu da tsabta ya ke”? Bulus yana magana ne game da Kiristocin da suka sa tunaninsu da sanin ya kamata ya yi daidai da mizanan Allah da suke cikin hurarriyar Kalmarsa. Irin waɗannan Kiristoci sun fahimci cewa ya yi daidai masu bi su kasance da ra’ayi dabam dabam a kan batutuwan da Allah bai haramta kai tsaye ba. Maimakon su zama masu sūkar mutane, sun yarda cewa abubuwan da Allah bai haramta ba suna da “tsabta.” Ba sa tsammanin cewa dukan mutane za su yi tunani daidai yadda suke yi game da fannoni na rayuwa da Littafi Mai Tsarki bai ba da ja-gora kai tsaye ba. Bari mu tattauna wasu misalai.

10. Ta yaya bikin aure (ko kuwa jana’iza) zai kawo ƙalubale?

10 Akwai iyalai da yawa da miji ne kawai ko kuma mata ce kawai ta zama Kirista amma ɗaya bai zama ba. (1 Bitrus 3:1; 4:3) Wannan zai iya jawo ƙalubale dabam dabam kamar sa’ad da ake bikin aure ko kuma jana’iza na dangi. Ka yi tunanin yadda zai kasance da matar da mijinta ba ya bin imaninta. Wani a cikin danginsa yana aure kuma za a yi bikin ne a cikin coci. (Ko kuwa dangin, wataƙila baba ko mama ta rasu kuma za a yi jana’izar a cikin coci.) An gayyaci ma’auratan, kuma yana son matarsa ta bi shi. Menene lamirinta ya ce game da batun? Menene za ta yi? Ga abubuwa biyu da za su iya faruwa.

11. Ka kwatanta yadda wata mata Kirista za ta iya yin tunani ko ta halarci bikin aure da ake yi a coci, kuma hakan ya sa ta tsai da wace shawara?

11 Lois ta yi tunani a kan umurnin Littafi Mai Tsarki da ya ce, ‘Ku fito daga Babila Babba,’ wato, daular duniya na addinin ƙarya. (Ru’ya ta Yohanna 18:2, 4) Cocin da take zuwa ne a dā ake bikin auren kuma ta san cewa a lokacin bikin za a gaya wa dukan mutanen su yi ayyuka na addini, kamar yin addu’a, rera waƙa, ko kuwa wasu alamu na addini. Ta ƙuduri aniya ba za ta sa hannu cikin waɗannan ayyukan ba kuma ba ta ma son ta kasance a wajen kuma a matsa mata ta karya amincinta. Lois tana daraja mijinta kuma tana son ta haɗa kai da shi wanda Nassi ya ce shi ne shugabanta; duk da haka ba ta son ta taka mizananta na Nassi. (Ayukan Manzanni 5:29) Shi ya sa, cikin dabara ta bayyana wa mijinta cewa idan zai je, ita ba za ta iya zuwa ba. Tana iya gaya masa cewa zai ji kunya idan ta je kuma ba ta sa hannu cikin wasu ayyukan ba, saboda haka zai fi kyau idan ba ta je ba. Shawarar da ta yi ya sa ta kasance da lamiri mai tsabta.

12. Ta yaya wani zai yi tunani kuma ya aikata game da gayyatar zuwa bikin aure a coci?

12 Ruth ta fuskanci irin wannan matsalar. Tana yi wa mijinta ladabi, ta ƙuduri aniya za ta kasance da aminci ga Allah kuma tana bin abin da lamirinta da Littafi Mai Tsarki ya koyar ya ce. Bayan ta yi tunani a kan darussa kamar irin waɗanda Lois ta yi, Ruth ta yi addu’a ta kuma bincika “Tambayoyi Daga Masu Karatu” da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Mayu, 2002 na Turanci. Ta tuna cewa Ibraniyawa uku sun bi umurnin cewa su kasance inda za a yi bautar gunki, duk da haka sun riƙe amincinsu ta wajen ƙin bauta wa gunkin. (Daniel 3:15-18) Ta tsai da shawara za ta bi mijinta amma ba za ta sa hannu cikin ayyukan addini ba, kuma tana aikata daidai da lamirinta. Cikin dabara ta bayyana wa mijinta sarai abin da lamirinta zai ƙyale ta ta yi da kuma abin da ba za ta iya yi ba. Ruth ta sa rai cewa mijinta zai ga bambanci tsakanin bauta ta gaskiya da ta ƙarya.—Ayukan Manzanni 24:16.

13. Me ya sa ba ma bukatar mu damu don Kiristoci biyu sun tsai da shawara dabam dabam?

13 Da yake Kiristoci biyu za su iya tsai da shawara dabam dabam a kan wani batu ya nuna cewa abin da mutum ya yi ba shi da muhimmanci ne ko kuma cewa ɗaya cikin su biyu tana da lamirin da ba ya aiki da kyau ne? A’a. Domin abin da ta shaida a dā a wajen waƙoƙi da alamu na bukukuwan coci, Lois ta fahimci cewa zuwa cocin zai kasance da lahani a gare ta. Kuma abin da ta tattauna dā da mijinta a kan batutuwa na addini zai iya shafan lamirinta. Saboda haka ta tabbata cewa shawarar da ta tsai da ya fi mata kyau.

14. Ya kamata Kiristoci su tuna da menene game da shawarar da mutum ya yi da kansa?

14 Amma shawarar da Ruth ta tsai da tana da kyau ne? Bai kamata mutane su sa baki a wannan batun ba. Bai kamata su shara’anta ko kuma su zarge ta don ta zaɓi ta halarta amma ba za ta yi kowane ayyukan addini ba. Ka tuna da gargaɗin Bulus a kan shawarar da mutum ya yi da kansa game da cin wasu abinci ko kuma kada ya ci: “Kada mai-ci ya rena wanda ba ya ci ba; wanda ba ya ci kuma kada ya zartas ma mai-ci: . . . tsayawassa ko fāɗuwassa ga nasa ubanɗaki ne. Hakika, za a ƙarfafa tsayawassa; gama Ubangiji yana da iko ya tsayadda shi.” (Romawa 14:3, 4) Hakika ba wani Kirista da zai so ya aririci wani ya ƙyale ja-gorar lamirinsa, gama yin haka zai zama kamar yin banza da muryar da za ta iya idar da saƙo mai ceton rai.

15. Me ya sa ya kamata a mai da hankali sosai da yadda wasu za su ji game da abubuwan da muka yi ko yadda zai shafi lamirinsu?

15 Ta wajen ci gaba da wannan batun, ya kamata matan biyu su bincika ƙarin abubuwa, ɗaya kuma shi ne yadda shawararsu za ta shafi wasu. Bulus ya gargaɗe mu: “Kada kowa ya sa abin tuntuɓe a cikin tafarkin ɗan’uwansa, ko kuwa dalilin fāɗuwa.” (Romawa 14:13) Mai yiwuwa Lois ta san cewa irin wannan yanayi ya kawo damuwa cikin ikilisiya ko kuma cikin iyalinta, kuma abin da ta yi zai iya shafan yaranta. Mai yiwuwa Ruth kuma ta san cewa irin wannan zaɓen bai kawo damuwa a cikin ikilisiya ba ko kuma a yankin. Ya kamata ’yan’uwa mata biyu da dukanmu mu fahimci cewa lamiri da aka koyar da kyau yana mai da hankali ga yadda abubuwa za su shafi mutane. Yesu ya ce: “Dukan wanda za shi sa guda ɗaya a cikin ƙanƙananan nan masu-bada gaskiya gareni shi yi tuntuɓe, gwamma dai a gareshi a rataya ma wuyansa babban dutsen niƙa, a nutsadda shi cikin zurfin teku.” (Matta 18:6) Idan mutum ba ya damuwa cewa abin da yake yi zai shafi wasu, lamirinsa zai ƙazantu yadda na wasu Kiristoci a Karita ya ƙazantu.

16. Waɗanne canje-canje ne Kirista zai yi da shigewar lokaci?

16 Ya kamata mutum ya ci gaba da kyautata dangantakarsa da Allah, yadda ya kamata ya ci gaba da saurara da kuma bin abin da lamirinsa ya ce. Bari mu yi tunanin yanayin Markus da ya yi baftisma ba da daɗewa ba. Lamirinsa ya gaya masa ya ƙi ayyuka da ba na Nassi ba ne da yake yi a dā, wataƙila sun ƙunshi bautar gunki ko kuma ƙarin jini. (Ayukan Manzanni 21:25) Hakika, yanzu yana ƙin abubuwa da sun ɗan yi kama da abubuwan da Allah ya hana. A wani ɓangare kuma, yana mamakin abin da ya sa wasu suka ƙi wasu abubuwa da ya amince da su, kamar wasu tsarin ayyuka na talabijin.

17. Ka kwatanta yadda lokaci da cin gaba na ruhaniya zai iya shafan lamiri da shawarwarin Kirista.

17 Da shigewar lokaci, Markus ya ƙara sanin Allah kuma ya kusance shi. (Kolossiyawa 1:9, 10) Yaya wannan ya shafe shi? Lamirinsa ya sami koyarwa sosai. Yanzu Markus ya fi son ya saurari lamirinsa kuma ya bincika ƙa’idodi na Nassi sosai. Yanzu ya fahimci cewa wasu abubuwa marar tabbaci da sun “ɗan yi kama” da ya ƙi ba su saɓa wa tunanin Allah ba. Ƙari ga haka, da yake ya fi mai da hankali ga bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma yana shirye ya bi abin da lamirinsa ya ce, yanzu lamirin Markus ya motsa shi ya guji tsarin talabijin da dā yana ganin sun dace. Hakika, ya tsabtata lamirinsa.—Zabura 37:31.

18. Waɗanne dalili na farin ciki muke da shi?

18 A yawancin ikilisiyoyi, akwai mutanen da suke da ci gaba na ruhaniya dabam dabam. Wasu cikinsu sababbi ne. Mai yiwuwa lamirinsu ba ya gaya musu kome a kan wasu batutuwa, amma lamirinsu na shafan yadda suke tsai da shawara a kan wasu al’amura. Irin waɗannan mutanen suna bukatar lokaci da taimako don su bi ja-gorar Jehobah daidai kuma su bi abin da lamarinsu da aka koyar ya gaya musu. (Afisawa 4:14, 15) Abin farin ciki, a cikin ikilisiyoyi da akwai mutane da suke da sani sosai kuma sun ƙware wajen yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, da lamiri da yake aikatawa cikin jituwa da tunanin Allah. Abin farin ciki ne a kasance tare da irin waɗannan mutane masu “tsabta” waɗanda suka fahimci abubuwa na ɗabi’a da na ruhaniya da suke da “tsabta” a wurin Ubangiji! (Afisawa 5:10) Bari dukanmu mu kasance da makasudin ci gaba har mu kai wannan matsayin kuma mu kasance da irin wannan lamiri da ya yi daidai da cikakken sani na gaskiya da ibada.—Titus 1:1.

[Hasiya]

a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris, 1983, shafuffuka 30-31 na Turanci, ya yi kalami da ya kamata a bincika game da ma’aurata.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa wasu Kiristoci da suke Karita suke da lamiri da ya ƙazantu?

• Ta yaya Kiristoci biyu da suke da lamiri da aka koyar da kyau za su tsai da shawara dabam dabam?

• Da shigewar lokaci, me ya kamata ya faru da lamirinmu?

[Taswira a shafi na 14]

Sicily

HELLAS

Karita

ASIYA ƘARAMA

Ƙubrus

BAHAR MALIYA

[Hoto a shafi na 16]

Kiristoci biyu da suke fuskantar yanayi ɗaya suna iya tsai da shawara dabam dabam

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba