Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 4/1 pp. 4-7
  • Amsoshin da Suka Dace!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin da Suka Dace!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance da Daidaita Wajen Shan Giya
  • Ka Guji Halayen da Ke Ɓata Jiki
  • “Ku Guje ma Fasikanci”
  • Ka Kasance da Dangantaka Mai Kyau da Iyalinka
  • Ma’aikaci Mai Ƙwazo da Shugaban Aiki Mai Kirki
  • Tushen Hikima da ya Fi Kyau
  • Ka Kasance Da Daidaitaccen Ra’ayi Game Da Shan Giya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ku Tattauna da Yaranku Game da Shan Giya
    Taimako don Iyali
  • Yadda Za Mu Nemi Shawara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 4/1 pp. 4-7

Amsoshin da Suka Dace!

YAWANCIN shawarar da ke cikin littattafai masu ba mutane shawara a yau suna mai da hankali ne a kan taimaka wa mutanen da suke fuskantar matsala a rayuwarsu. Amma Littafi Mai Tsarki ya bambanta. Ko da yake shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta iya taimakon waɗanda suke shan wahala, amma shawararsa ba don waɗanda suke shan wahala kaɗai ba ne. Shawararsa tana taimakon mutum ya guji matsalolin da suke sa rayuwa ta yi wuya.

Littafi Mai Tsarki zai iya “bada azanci ga marasawayo, ilimi da hankali ga sarmayi.” (Misalai 1:4) Idan ka yi amfani da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, “hankali za ya riƙa tsaronka, Fahimi kuma za ya kiyaye ka: Domin a cece ka daga hanyar mugun.” (Misalai 2:11, 12) Ka yi la’akari da waɗansu misalai da suka nuna yadda bin shawarar Littafi Mai Tsarki zai kiyaye lafiyarka, ya kyautata rayuwar iyalinka kuma ya sa ka zama ma’aikaci ko kuma shugaba mai kirki.

Ka Kasance da Daidaita Wajen Shan Giya

Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya daidai kima ba. Manzo Bulus ya nuna amfanin ruwan anab sa’ad da ya shawarci Timothawus: “Ka mori ruwan anab kaɗan saboda tumbinka da yawan kumamancinka.” (1 Timothawus 5:23) Wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Allah bai yi inabi don magani ba kawai. An ce ruwan anab yana sa “zuciyar mutum ta wartsake.” (Zabura 104:15) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi game da zama ‘bayi ga yawan ruwan anab.’ (Titus 2:3) Ya ce: “Kada ka kasance kana cikin masu-shayeshaye: Ko wurin masu-zarin cin nama: Gama mai-maye da mai-zarin ci za su yi talauci.” (Misalai 23:20, 21) Wane sakamako ne za a samu idan aka ƙi bin wannan shawara? Ka yi la’akari da waɗannan bincike daga wasu ƙasashe.

Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta ce a cikin Global Status Report on Alcohol 2004 (Rahoto A Kan Shan Giya a Duniya ta 2004): “A kowace shekara mutanen ƙasar Ireland suna kashe fiye da dala biliyan 3 saboda matsalolin da giya take jawowa.” Kuɗin da ake kashewa ya haɗa da “dala biliyan 350 don kāre lafiyar jiki, da dala biliyan 380 don hatsari na kan titi, da dala biliyan 126 don laifin da masu shan giya suke yi da kuma dala biliyan 1,300 na hasarar da ake yi don waɗanda suka kasa yin aiki don sun sha giya sun bugu,” in ji rahoton.

Abin da ya fi muhimmanci fiye da kuɗin da ake kashewa a shan giya shi ne wahalar da mutane suke sha. Alal misali a Australiya, a shekara guda, waɗanda suka bugu da giya suna zaluntar mutane fiye da 500,000. A Faransa, kashi 30 na zaluncin da ake yi a gida saboda buguwa ne da giya. Saboda haka, shawarar Littafi Mai Tsarki game da shan giya ya dace.

Ka Guji Halayen da Ke Ɓata Jiki

A shekara ta 1942, sa’ad da mutane suke ɗaukan cewa shan taba abu ne mai kyau, wannan jaridar ta taimaki mutane su fahimci cewa shan taba taka ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ne kuma ya kamata a guje ta. Wani talifi da aka buga a shekarar ta ce waɗanda suke son su faranta wa Allah rai dole ne su bi umurnin Littafi Mai Tsarki da ya ce mu “tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu.” (2 Korinthiyawa 7:1) Yanzu bayan shekaru 65, shawarar da Littafi Mai Tsarki ya ba da ya dace.

A shekara ta 2006, Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta ce “shan taba ce take jawo yawancin mutuwa da ake yi a duniya.” A kowace shekara, mutane miliyan biyar suna mutuwa don shan taba. Kusan mutane miliyan uku suna mutuwa kowace shekara saboda ƙanjamau. A ƙarni na 20, shan taba ta kashe mutane kusan miliyan 100, fiye da waɗanda aka kashe a yaƙe-yaƙe da aka yi a wannan ƙarni. Hakika, yanzu an yarda da shawarar guje wa shan taba.

“Ku Guje ma Fasikanci”

Mutane da yawa ba sa son su yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da jima’i. Littafi Mai Tsarki bai hana yin jima’i ba, yadda aka rinjaye mutane su gaskata. Amma ya ba da shawarar da ta dace game da jima’i. Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa jima’i ya dace a tsakanin mata da miji da suka yi aure ne kawai. (Farawa 2:24; Matta 19:4-6; Ibraniyawa 13:4) Jima’i hanya ce da ma’aurata za su nuna ƙaunarsu ga juna. (1 Korinthiyawa 7:1-5) Duka yaran da aka haifa ta wannan dangantaka za su more kulawa daga iyayen da suke kula da juna.—Kolossiyawa 3:18-21.

Littafi Mai Tsarki ya ce game da lalata: “Ku guje ma fasikanci.” (1 Korinthiyawa 6:18) Menene dalili ɗaya na yin haka? Ayar ta ci gaba: “Kowane zunubin da mutum ya ke yi na bayan jiki ne; amma mai-aikin fasikanci shina yi ma jiki nasa zunubi.” Menene zai faru idan aka ƙi bin shawarar Littafi Mai Tsarki game da jima’i?

Ka yi la’akari da abin da ke faruwa a Amirka. A cikin duka ƙasashe masu arziki, wannan ƙasar ce take da matasan da suka fi yin cikin shege, su wajen 850,000 a kowace shekara. Yawancin jarirai da ba a zubar da cikinsu ba ba su da uba. Babu shakka, shi ya sa wasu cikin waɗannan ’yan mata suna iya ƙoƙarinsu su yi renon yaransu cikin ƙauna da kuma horo, kuma wasu sun yi nasara. Amma, gaskiyar ita ce yawancin irin waɗannan yara maza da mamarsu matasa ne suna ƙarewa a gidan yari, yaransu mata kuma sukan ɗauki cikin shege. Bayan ya bincika adadin shekaru da yawa da suka wuce, wani mai bincike Robert Lerman ya ce: “Wataƙila yawan iyaye gwauraye ne ya ƙara jawo matsaloli a cikin al’umma, kamar yawan yara da suka bar makaranta, masu shan giya da ƙwayoyi, masu cikin shege, haihuwar yara, da kuma rashin da’a na yara.”

Waɗanda suke yin lalata suna iya kama cuta ta jiki da ta hankali. Alal misali, wata jarida mai suna Pediatrics ta ce: “Bincike ya nuna cewa matasa masu yin lalata suna iya yin baƙin ciki da kuma kisan kai fiye da wasu.” Game da wasu haɗari na lafiyar jiki, ƙungiyar American Social Health Association ta ce: “Fiye da rabin mutane a Amirka za su kamu da cuta da ake samu ta lalata a wani lokaci a rayuwar su.” Ka yi tunanin irin wahalar da za a guje wa idan aka bi umurnin Littafi Mai Tsarki game da jima’i!

Ka Kasance da Dangantaka Mai Kyau da Iyalinka

Littafi Mai Tsaki bai ba da umurni game da halayen banza kawai ba. Ka lura da shawarar da ya ba da game da kyautata rayuwar iyali.

Kalmar Allah ta ce: “Mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu.” (Afisawa 5:28) Maimakon su raina matansu, ta gargaɗi maza su zauna da matansu ‘bisa ga sani, su bada girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi.’ (1 Bitrus 3:7) Game da matsalar da za ta iya tasowa, an gargaɗi maza: “Ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.” (Kolossiyawa 3:19) Duk namijin da ya bi wannan shawarar, matarsa za ta ƙaunace shi kuma ta yi masa ladabi.

Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan gargaɗin ga matan aure: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji. Gama miji kan mata ya ke, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne . . . matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:22, 23, 33) Duk matar da ta bi wannan shawarar sa’ad da take wa mijinta magana ko kuma tana magana game da shi, mijinta zai ƙaunace ta.

Game da renon yara, Littafi Mai Tsarki ya ba iyaye shawara cewa su riƙa tattaunawa da yaransu ‘sa’anda suke zaune cikin gidansu, da sa’anda suke tafiya a kan hanya, da sa’anda suke kwanciya, da sa’anda suka tashi.’ (Kubawar Shari’a 6:7) Musamman an umurci iyaye maza su koya wa yaransu tarbiyya mai kyau da horo cikin ƙauna. Kalmar Allah ta ce: “Ku ubanni kuma, kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) An umurci yara su ‘yi biyayya ga waɗanda suka haife su,’ kuma su ‘girmama ubansu da uwarsu.’a—Afisawa 6:1, 2.

Kana ganin cewa iyalai za su amfana ta wurin bin wannan shawarar kuwa? Za ka iya cewa ‘hakika,’ ‘yana da daɗin faɗa amma yana taimako kuwa?’ Muna gayyatarka ka ziyarci Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah. A wajen za ka ga iyalai waɗanda suke ƙoƙari su bi umurnin Littafi Mai Tsarki. Ka yi magana da su. Ka lura da yadda waɗanda suke cikin iyalin suke yi da juna. Za ka ga cewa bin umurnin Littafi Mai Tsarki yana kawo farin ciki a cikin iyali!

Ma’aikaci Mai Ƙwazo da Shugaban Aiki Mai Kirki

Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya ba da game da ƙoƙarin riƙe aiki? Ya ce za a so ma’aikacin da ya san aikinsa sosai kuma za a yabe shi. Sarki Sulemanu ya yi tambaya: “Kana ganin mutum mai-gwaninta cikin sana’atasa? Wannan za ya tsaya a gaban sarakuna.” (Misalai 22:29) A wani ɓangare kuma, “rago” yana kama da ‘hayaƙi a idanun’ shugabansa. (Misalai 10:26) Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi ma’aikata su riƙa faɗin gaskiya kuma su yi ƙwazo. “Mai-yin sata kada shi ƙara yin sata: amma gwamma shi yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da ya ke da kyau.” (Afisawa 4:28) Za a bi wannan shawara har lokacin da shugaban aikin ba ya nan. “Cikin abu duka ku yi biyayya da waɗanda su ke iyayengijinku bisa ga tabi’ar jiki; ba da bautar ganin ido ba, kamar masu-gamin mutane, amma da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.” (Kolossiyawa 3:22) Idan kai shugaba ne, ba za ka ƙaunaci ma’aikacin da yake bin wannan shawarar ba?

Littafi Mai Tsarki ya gaya wa shugaban aiki: “Ma’aikaci ya isa hakinsa.” (1 Timothawus 5:18) Dokar Allah ga Isra’ilawa ta ce shugaba ya ba ma’aikatansa hakkinsu. Musa ya rubuta: “Ba za ka zalumci maƙwabcinka ba, ba kuwa za ka yi masa ƙwace ba: hakin ma’aikaci na ijara kada ya kwana a wurinka har safiya.” (Leviticus 19:13) Ba za ka yi farin cikin yin aiki a ƙarƙashin irin wannan shugaba mai yin biyayya ga umurnin Littafi Mai Tsarki kuma da yake biyan ka hakkin ka ba?

Tushen Hikima da ya Fi Kyau

Ka yi mamakin ganin cewa irin wannan tsohon littafin, wato Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da irin wannan shawarar mai amfani a yau? Abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya tsira fiye da wasu littattafai shi ne, yana ɗauke da “Maganar Allah,” ba ta mutum ba.—1 Tassalunikawa 2:13.

Muna ƙarfafa ka ka san Kalmar Allah sosai. Idan ka yi haka, za ka soma ƙaunar Mawallafin Littafi Mai Tsarki, wato Jehobah Allah. Ka bi umurnin da ya ba da, zai taimake ka kuma ya gyara rayuwarka. Idan ka yi haka za ka ‘kusaci Allah, shi ma zai kusace ka.’ (Yaƙub 4:8) Babu wani littafin da zai taimaka maka kamar wannan.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaki iyali, ka duba littafin nan Asirin Farin Ciki na Iyali, da Shaidun Jehobah suka wallafa.

[Hoto a shafi na 4]

Kana ganin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shan giya ya dace?

[Hoto a shafi na 5]

Ka yarda da shawarar da Littafi Mai Tsarki ya yi game da guje wa shan taba?

[Hotuna a shafi na 7]

Bin umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana kyautata rayuwar iyali

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 5]

Duniya: An ɗauko daga hoton NASA

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba