Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 4/1 p. 3
  • Neman Amsoshin da Suka Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Neman Amsoshin da Suka Dace
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Makamantan Littattafai
  • Amsoshin da Suka Dace!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Yadda Za Mu Nemi Shawara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Wace Irin Shawara Ce Kake Ba Mutane?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 4/1 p. 3

Neman Amsoshin da Suka Dace

Ta yaya zan iya kiyaye lafiyar jikina?

Ta yaya zan kyautata farin cikin iyalina?

Menene zan yi don in riƙe aikina?

KA TAƁA yin irin waɗannan tambayoyin? Ka sami amsoshin da suka dace? A kowace shekara, ana buga littattafai dabam dabam guda 2,000 da suke ɗauke da shawara game da waɗannan tambayoyi da waɗansu batutuwa masu muhimmanci. A Britaniya kaɗai, mutane suna kashe dala miliyan 150 kowace shekara a littattafai masu ba da shawara game da yadda za a jimre wa kalubale da ake fuskanta a rayuwa. A Amirka, mutane suna kashe kusan dala miliyan 600 wajen sayen littattafan da za su ba su shawara a kan yadda za su magance matsalolisu. Hakika, ba kai kaɗai ba ne ka ke neman shawara mai kyau game da yadda za ka bi da rayuwa ta yau da kullum ba.

Game da wannan shawarar da ke cikin waɗannan littatafai masu yawa, wani mawallafi ya ce: “Yawancin sababbin littattafai suna maimaita abin da aka riga aka rubuta ne a dā.” Hakika, waɗannan littattafai suna maimaita yawancin shawarar da ke cikin wani tsohon littafi da ke duniya ne. Wannan littafin shi ne littafin da aka fi rarrabawa a tarihi. An fassara rabi ko duka a harsuna 2,400. Fiye da kofi biliyan 4 ne aka buga a dukan duniya. Littafi Mai Tsarki ne wannan littafin.

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci.” (2 Timothawus 3:16) Hakika, ba a rubuta Littafi Mai Tsarki kamar littattafai masu ba mutane shawara game da yadda za su magance matsala ba. Dalilin da ya sa aka rubuta littafin shi ne don ya sanar da ’yan adam nufin Allah. Duk da haka Littafi Mai Tsarki ya faɗi abubuwa da yawa game da yadda za a jimre wa matsalolin da suke shafan mutane, kuma ya yi alkawari cewa waɗanda suka bi shawararsa za su amfana. (Ishaya 48:17, 18) Idan mutum ya yi amfani da shawarar, komin yarensa, al’ada, ko kuma iliminsa zai yi nasara. Ka yi la’akari da talifi na gaba kuma ka yanke wa kanka shawara ko abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da irin waɗannan batutuwa kamar su lafiyar jiki, iyali, da kuma aiki yana da amfani.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba