Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 2/1 p. 3
  • Wasu ne Kawai Ya Kamata Su Faɗi Gaskiya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wasu ne Kawai Ya Kamata Su Faɗi Gaskiya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Lahanin da Ƙarya Take Jawowa
  • Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Jehovah, Allah Na Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Yin Koyi Da Allah Na Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Faɗi Gaskiya Ga Maƙwabcinka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 2/1 p. 3

Wasu ne Kawai Ya Kamata Su Faɗi Gaskiya?

“BA NA son ƙarya, kuma ba na son a yi mini ƙarya!” in ji wata yarinya ’yar shekara 16. Yawancinmu muna jin hakan. Muna son abin da aka gaya mana ko ta maganar baki ko kuma a rubuce ya kasance gaskiya ce. Amma muna faɗin gaskiya sa’ad da muke gaya wa mutane wani abu?

A wani bincike da aka yi a Jamus, yawancin mutane suna jin cewa “ba laifi ba ne mutum ya yi ƙarya a ƙananan al’amura don ya kāre kansa ko wasu daga lahani, kuma hakan ya dace don mutane su yi abokantaka da juna.” Kuma wata ’yar jarida ta rubuta: “Faɗin cikakkiyar gaskiya yana da kyau amma hakan ba shi da daɗi.

Muna jin ya fi kyau wasu su faɗi gaskiya amma mu mu yi ƙarya a wani lokaci? Yana da muhimmanci ne mu faɗi gaskiya ko mu yi ƙarya? Menene sakamakon yin ƙarya?

Lahanin da Ƙarya Take Jawowa

Ka yi la’akari da lahanin da ƙarya ke jawowa. Yin ƙarya na jawo rashin aminci tsakanin mata da miji da kuma cikin iyali. Gulma za ta iya ɓata sunan mutum. Idan ma’aikata suna sata wannan na sa a ƙara kuɗin gudanar da kasuwanci kuma hakan na sa kaya su yi tsada. Cin wasu daga cikin kuɗin haraji yana hana gwamnati samun isashen kuɗin haraji da za ta yi wa mutane hidima. Labaran ƙarya da masu bincike suke bayarwa yana ɓata aikinsu da kuma ma’aikatar da suke wa aiki. Sa hannu a tsarin yin arziki na dare ɗaya na sa mutane su yi hasarar kuɗin da suka tara ko kuma fiye da haka. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “harshe mai-ƙarya” da “mai-shaidan zur wanda ya ke furtawa da ƙarya” suna cikin abubuwa da Jehobah Allah ya ƙi!—Misalai 6:16-19.

Yin ƙarya zai iya jawo lahani, ga mutane da kuma al’umma gabaki ɗaya. Ba wanda zai yi musun wannan.

[Hoto a shafi na 3]

Yin ƙarya yana jawo rashin aminci tsakanin mata da miji

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba