An Soma “Tashi Na Fari”
“Matattun da ke cikin Kristi za su fara tashi.”—1 TASSALUNIKAWA 4:16.
1, 2. (a) Wane bege ne waɗanda suka mutu suke da shi? (b) Menene ya sa ka gaskata cewa akwai tashin matattu? (Duba hasiya.)
“MASU-rai sun san za su mutu.” Hakan ya ci gaba da faruwa tun lokacin da Adamu ya yi zunubi. A cikin tarihi, duk wanda aka haifa ya san cewa wata rana zai mutu, kuma yana iya tunani: ‘Menene zai faru bayan haka? Menene yanayin matattu?’ Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa: “Amma matattu ba su san komi ba.”—Mai-Wa’azi 9:5.
2 Akwai bege kuwa ga waɗanda suka mutu? Ƙwarai kuwa. Dole ne hakan ya kasance idan ainihin nufin Allah ga ’yan adam zai cika. Tun shekaru da yawa, bayin Allah masu aminci sun ba da gaskiya ga alkawarin Jehobah game da Zuriyar da zai halaka Shaiɗan kuma ya kawar da ɓarnar da ya yi. (Farawa 3:15) Yawancinsu sun mutu. Idan suna son su shaida cikar wannan alkawarin da kuma wasu da Jehobah ya yi, dole ne a ta da su daga matattu. (Ibraniyawa 11:13) Hakan zai yiwu kuwa? Ƙwarai kuwa. Manzo Bulus ya ce: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Bulus ya taɓa ta da wani saurayi daga matattu mai suna Aftikos da ya faɗo daga tagar bene mai hawa uku “aka ɗauke shi matace.” Wannan shi ne tashin matattu na tara kuma na ƙarshe da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki.—Ayukan Manzanni 20:7-12.a
3. Wane ƙarfafa ne ka samu daga kalaman Yesu da ke Yohanna 5:28, 29, kuma don me?
3 Waɗannan tashin matattu guda tara sun ba da dalili na amincewa da maganar Bulus. Sun ƙarfafa tabbacinmu a alkawarin Yesu: ‘Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryar [Yesu,] su fito kuma.’ (Yohanna 5:28, 29) Waɗannan kalaman suna da ban ƙarfafa! Kuma abin ƙarfafa ne ga miliyoyin da ƙaunatattunsu suka mutu!
4, 5. Waɗanne irin tashin matattu ne Littafi Mai Tsarki ya ambata, kuma wannene za mu tattauna a cikin wannan talifin?
4 Yawancin waɗanda aka ta da daga matattu za su komo duniyar da ke cike da salama a ƙarƙashin Mulkin Allah. (Zabura 37:10, 11, 29; Ishaya 11:6-9; 35:5, 6; 65:21-23) Amma, za a yi wasu tashin matattu kafin hakan ya faru. Da farko, za a ta da Yesu Kristi daga matattu don ya gabatar da hadayarsa mai tamani ga Allah a madadinmu. Yesu ya mutu kuma an ta da shi daga matattu a shekara ta 33 A.Z.
5 Bayan haka, shafaffu “Isra’ila na Allah” za su je su sami Ubangiji Yesu Kristi a ɗaukakarsa na samaniya, a inda za su “zauna har abada tare da Ubangiji.” (Galatiyawa 6:16; 1 Tassalunikawa 4:17) Ana kiran wannan aukuwar “tashi na fari.” (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Bayan an kammala wannan tashin matattun, za a ta da miliyoyi daga matattu zuwa duniya domin su sami rai na dindindin a Aljanna. Saboda haka, ko da begen mu na samaniya ne ko na duniya, muna sha’awar “tashi na fari.” Wane irin tashin matattu ne wannan? A wane lokaci ne ya faru?
“Da Wane Irin Jiki?”
6, 7. (a) Kafin shafaffun Kiristoci su je sama, menene zai faru? (b) Da wane irin jiki ne za a ta da su?
6 A cikin wasiƙarsa ta farko da ya yi wa Korinthiyawa, Bulus ya yi tambaya game da tashin farko: “Ƙaƙa a ke tada matattu? da wane irin jiki kuma su ke zuwa?” Sai ya amsa tambayar: “Abin da kai da kanka ke shibkawa ba shi samun rai ba, sai ya rigaya ya mutu tukuna: . . . amma Allah ke ba shi jiki yadda ya nufa, . . . amma na sama darajassu dabam, na duniya kuwa darajassu dabam.”—1 Korinthiyawa 15:35-40.
7 Kalaman Bulus sun nuna cewa dole ne Kiristocin da aka shafa da ruhu mai tsarki su mutu kafin su sami sakamakonsu na samaniya. A lokacin da suka mutu, jikinsu na duniya zai koma ƙasa. (Farawa 3:19) A lokacin da Allah ya zaɓa, za a ta da su da irin jikin da ya dace da rayuwa a sama. (1 Yohanna 3:2) Allah ya ba su rai marar mutuwa. Wannan ba abin da aka haife su da shi ba ne. Bulus ya ce: “Wannan mai-mutuwa kuwa shi yafa rashin mutuwa.” Rai marar mutuwa kyauta ce daga Allah, wadda waɗanda suka tashi da farko daga matattu suka “yafa.”—1 Korinthiyawa 15:50, 53; Farawa 2:7; 2 Korinthiyawa 5:1, 2, 8.
8. Ta yaya muka san cewa Allah bai zaɓi mutane 144,000 daga addinai dabam dabam ba?
8 Mutane 144,000 ne kaɗai za su sami tashin matattu na farko. Jehobah ya soma zaɓansu a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z., ba da daɗewa ba bayan an ta da Yesu daga matattu. Dukansu suna da “sunan [Yesu] da sunan Ubansa, a rubuce bisa goshinsu.” (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3) Ba wai an zaɓe su ba ne daga addinai dabam dabam. Dukansu mabiyan Kristi ne, kuma suna ɗokin amsa sunan Ubansa, Jehobah. Sa’ad da aka ta da su daga matattu, za su karɓi aikin da za su yi a sama. Begen yi wa Allah hidima a wannan hanyar tana sa su farin ciki.
An Soma Shi Kuwa?
9. Ta yaya ne Ru’ya ta Yohanna 12:7 da kuma sura 17:14 suka taimaka mana mu kimanta lokacin da aka soma tashi na farko?
9 A wane lokaci ne aka soma tashin fari? Muna da isashen tabbacin da ya nuna cewa an soma shi. Alal misali, ka kwatanta waɗannan surori biyu na Ru’ya ta Yohanna. Na farko, ka duba Ru’ya ta Yohanna sura 12. A nan mun karanta cewa Yesu Kristi da aka naɗa tare da mala’ikunsa masu tsarki, sun yi yaƙi da Shaiɗan da kuma aljanunsa. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-9) Kamar yadda wannan jaridar take ambatawa a yawancin lokaci, an soma wannan yaƙin a shekara ta 1914.b Ka lura cewa, ba a ambata ba cewa shafaffu mabiyan Kristi suna tare da Yesu a wannan yaƙin na samaniya ba. Yanzu ka duba sura ta 17 na Ru’ya ta Yohanna. Mun karanta cewa bayan an halaka “Babila Babba,” Ɗan Rago zai kame al’ummai. Sai ta daɗa cewa: “Kirayayyu, zaɓaɓu, masu-aminci, za su yi nasara.” (Ru’ya ta Yohanna 17:14) Ya zama cewa an riga an ta da “kirayayyu, zaɓaɓu, masu-aminci” daga matattu idan suna tare da Yesu a lokacin da zai ci duniyar Shaiɗan. Babu shakka, shafaffu da suka mutu kafin Armageddon an soma ta da su a shekara ta 1914 kuma hakan zai ci gaba har Armageddon.
10, 11. (a) Su wanene dattawa 24, kuma menene ɗaya daga cikinsu ya bayyana wa Yohanna? (b) Menene za mu iya kammalawa game da wannan?
10 Muna iya faɗin ainihin sa’ad da aka soma tashin matattu na farko? An ba da ƙarin haske da muka gani a Ru’ya ta Yohanna 7:9-15, inda manzo Yohanna ya kwatanta wahayinsa na “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa.” Ɗaya daga cikin dattawa 24 ne ya bayyana wa Yohanna taron mai girma, kuma waɗannan dattawan suna wakiltar mutane 144,000 waɗanda za su yi mulki tare da Kristi a ɗaukakarsa na samaniya.c (Luka 22:28-30; Ru’ya ta Yohanna 4:4) Yohanna da kansa yana da begen zuwa sama, amma tun da yake yana duniya sa’ad da dattijon ya yi masa magana, a wahayin, Yohanna yana wakiltan shafaffun da suke duniya da ba su tafi sama ba tukun.
11 Menene ya kamata mu kammala game da gaskiyar cewa ɗaya daga cikin dattawa 24 ne ya bayyana wa Yohanna taro mai girma? Kamar waɗanda aka ta da daga matattu a cikin rukunin dattawa 24 ne suke sanar da hurarriyar gaskiya a yau. Me ya sa haka yake da muhimmanci? Domin an bayyana ko su wanene taro mai girma ga shafaffun bayin Allah da ke duniya a shekara ta 1935. Idan an yi amfani da ɗaya daga cikin dattawa 24 ya sanar da wannan gaskiya mai muhimmanci, hakan na nufin cewa an ta da shi zuwa sama a shekara ta 1935. Hakan na nufin cewa an soma tashin matattu na farko tsakanin shekara ta 1914 da 1935. Zai yiwu mu ba da cikakken amsa?
12. Ka bayyana dalilin da ya sa ake tunanin cewa an soma tashin matattu na farko a cikin daminar 1918.
12 Zai taimaka mana sosai mu tattauna abin da za mu kira kwatanci na Littafi Mai Tsarki. An naɗa Yesu Kristi a matsayin Sarki mai jiran gado na Mulkin Allah a ƙarshen shekara ta 29 A.Z. Shekara uku da rabi bayan haka, a cikin damina ta shekara ta 33 A.Z., an ta da shi daga matattu ya zama ruhu mai iko. Zai dace mu yi tunani cewa tun da yake an naɗa Yesu a ƙarshen shekara ta 1914, an soma ta da amintattun mabiyansa shafaffu daga matattu shekara uku da rabi bayan haka, wato a cikin damina ta shekarar 1918? Hakan zai yiwu. Ko da yake ba za a iya samun hakan ba a cikin Littafi Mai Tsarki kai tsaye, amma hakan ya jitu da sauran Nassosi da ya nuna cewa an soma tashin matattu na farko ba da daɗewa ba bayan bayyanar Kristi.
13. A wace hanya ce 1 Tassalunikawa 4:15-17 ta nuna cewa tashin matattu na farko ya soma ne a farkon zuwan Kristi?
13 Alal misali, Bulus ya rubuta: “Mu da mu ke da rai, wanzazzu ne har zuwan Ubangiji, [ba har ƙarshen zuwansa ba] ba za mu rigaya waɗanda sun yi barci ba ko kaɗan. Gama Ubangiji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai-ƙarfi, da muryar sarkin malaiku, da ƙafon Allah kuma: matattun da ke cikin Kristi za su fara tashi. Sa’annan mu da mu ke da rai, mun wanzu, tare da su za a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu tarbi Ubangiji a sararin sama: hakanan za mu zauna har abada tare da Ubangiji.” (1 Tassalunikawa 4:15-17) Saboda haka, shafaffun Kiristocin da suka mutu kafin zuwan Kristi za su tashi zuwa sama kafin waɗanda suke raye a lokacin zuwan Kristi. Hakan na nufin cewa an soma tashin matattu na farko a farkon zuwan Kristi, kuma ya ci gaba “cikin zuwansa.” (1 Korinthiyawa 15:23) Maimakon hakan ya faru sau ɗaya, tashin matattu na fari yana ci gaba da faruwa.
“Aka ba Kowane a Cikinsu Farar Riga”
14. (a) A wane lokaci ne wahayin da aka rubuta a Ru’ya ta Yohanna sura 6 ya cika? (b) Menene aka kwatanta a Ru’ya ta Yohanna 6:9?
14 Ka yi la’akari da shaidar da ke cikin Ru’ya ta Yohanna sura ta 6. An ga Yesu a kan doki a matsayin Sarki mai nasara. (Ru’ya ta Yohanna 6:2) Al’ummai sun saka hannu a yaƙi mai girma. (Ru’ya ta Yohanna 6:4) Yunwa ta zama ruwan dare. (Ru’ya ta Yohanna 6:5, 6) Mugun annoba ta addabi mutane. (Ru’ya ta Yohanna 6:8) Duka waɗannan aukuwar da aka annabta sun yi daidai da yanayin duniya tun shekara ta 1914. Amma akwai abin da ya faru. An jawo hankalinmu ga bagadi na hadaya. A gefensa akwai “rayukan waɗanda aka kashe sabili da maganar Allah da shaida da suka riƙe kuma.” (Ru’ya ta Yohanna 6:9) Tun da yake “ran nama yana cikin jini,” abin da kasancewa a gefen bagadi yake wakilta shi ne jinin amintattun bayin Yesu da aka yanka domin shaidar da suke ba da wa da ƙwazo da kuma gaba gaɗi.—Leviticus 17:11.
15, 16. Ka bayyana abin da ya sa kalaman da ke Ru’ya ta Yohanna 6:10, 11 suke nuni ga tashin matattu na farko.
15 Kamar jinin Habila mai aminci, jinin waɗannan Kiristocin da aka kashe domin imaninsu yana kuka domin adalci. (Farawa 4:10) “Suka tada murya da ƙarfi, suka ce, Har yaushe, ya Ubangiji, mai-tsarki, mai-gaskiya, za ka yi jinkiri da shari’a bisa mazamnan duniya da ɗaukan fansar jininmu?” Me ya faru bayan haka? “Aka ba kowane a cikinsu farar riga: aka ce masu kuma, su huta tukuna kaɗan, har lissafin abokan bautansu da yan-uwansu, waɗanda za a kashe kamar yadda aka kashe su, ya cika.”—Ru’ya ta Yohanna 6:10, 11.
16 An tsoma fararen rigunan waɗanda suke kwance a gaban bagadin cikin jini ne? A’a! An ba da fararen rigunan ne ga waɗanda aka zubar da jininsu a alamance a kan bagadin. Sun sadaukar da rayuwarsu domin sunan Yesu kuma yanzu an ta da su daga matattu su zama ruhu. Ta yaya muka san haka? A cikin littafin Ru’ya ta Yohanna mun karanta cewa: “Wanda ya yi nasara za a yafa shi hakanan da fararen tufafi: ba ni kuwa shafe sunansa daga cikin littafin rai ba daɗai.” Ka tuna kuma cewa dattawa 24 “suna yafe da fararen tufafi; bisa kawunansu kuma akwai rawanai na zinariya.” (Ru’ya ta Yohanna 3:5; 4:4) Bayan da yaƙi, yunwa, da annoba suka soma addabar duniya, an soma ta da mutane 144,000 da suka mutu da suke wakiltar jinin da ke gefen bagadin, zuwa rayuwa ta samaniya, kuma suna sanye da fararen kaya na alama.
17. Ta yaya ne waɗanda suka karɓi fararen tufafi za su “huta”?
17 Waɗanda aka ta da daga matattu suna bukatar su “huta.” Dole ne su jira cikin haƙuri ranar ɗaukan fansa na Allah. “Abokan bautansu,” shafaffun Kiristocin da suke duniya, suna bukatar su tabbatar da amincinsu a lokacin gwaji. Idan lokacin hukuncin Allah ya yi, ‘hutun’ zai ƙare. (Ru’ya ta Yohanna 7:3) A wannan lokacin, waɗannan da aka ta da daga matattu da kuma Ubangiji Yesu Kristi, za su hukunta miyagu, tare da waɗanda suka zubar da jinin Kiristoci marar laifi.—2 Tassalunikawa 1:7-10.
Abin da Hakan ke Nufi a Gare Mu
18, 19. (a) Domin waɗanne dalilai ne za ka iya cewa an soma tashin matattu na fari? (b) Yaya ka ji da ka fahimci ma’anar tashin matattu na farko?
18 Kalmar Allah ba ta faɗi ainihin kwanan watan da aka soma tashin matattu na farko ba, amma ta bayyana cewa hakan ya faru ne a wani lokacin da aka ƙayyade, wato a lokacin zuwan Kristi. Waɗanda za a soma ta da wa, su ne shafaffun Kiristocin da suka mutu kafin dawowar Kristi. Yayin da dawowar Kristi ke ci gaba, shafaffun Kiristocin da suka gama aikinsu a duniya cikin aminci za su canja “da ƙyaftar ido” su zama halittun ruhu masu iko. (1 Korinthiyawa 15:52) Duka shafaffun za su sami gadōnsu kafin yaƙin Armageddon? Ba mu sani ba. Abin da muka sani shi ne cewa, idan lokacin da Allah ya zaɓa ya yi, duka mutane 144,000 za su tsaya a kan Dutsen Sihiyona na samaniya.
19 Mun san cewa yawancin mutane 144,000 suna tare da Kristi. Kaɗan ne kawai suka rage a duniya. Wannan ƙwakƙwarar shaida ce da ta nuna cewa lokacin hukunci na Allah yana ƙara gabatowa! Nan ba da daɗewa ba, za a halakar da wannan duniyar Shaiɗan. Za a saka Shaiɗan cikin kurkuku. Sa’an nan, za a iya soma tashin matattu gabaki ɗaya, domin ta hadayar fansa na Yesu, mutane masu aminci za su iya zama kamiltattu, gatar da Adamu ya rasa. Annabcin Jehobah da ke Farawa 3:15 yana cika. Kasancewar mu a raye a wannan zamanin gata ne mai girma!
[Hasiya]
a Domin sauran tashin matattu guda takwas ɗin, ka duba 1 Sarakuna 17:21-23; 2 Sarakuna 4:32-37; 13:21; Markus 5:35, 41-43; Luka 7:11-17; 24:34; Yohanna 11:43-45; Ayukan Manzanni 9:36-42.
b Don tabbaci na Nassosi cewa bayyanar Kristi ta soma a 1914, ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shafofi na 215-218, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
c Don ƙarin bayani a kan yadda muka san cewa dattawa 24 suna wakiltar shafaffun Kiristoci a matsayinsu na samaniya, ka duba Revelation—Its Grand Climax At Hand! shafi na 77, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Bayyanawa?
Ta yaya ne nassosin da ke gaba suka taimaka mana mu fahimci lokacin da aka yi “tashi na fari”?
• Ru’ya ta Yohanna 12:7; 17:14
• Ru’ya ta Yohanna 7:13, 14
• 1 Korinthiyawa 15:23; 1 Tassalunikawa 4:15-17
• Ru’ya ta Yohanna 6:2, 9-11
[Hotuna a shafi na 28]
Wane tashin matattu ne za a yi kafin a ta da ’yan adam gabaki ɗaya daga matattu?