Yadda Za Ka Iya Yin Nasara
KAMAR yadda iyaye suke kula da ’ya’yansu kuma suke son su yi nasara, hakazalika, Ubanmu na sama yana kula da mu kuma yana son mu yi nasara. Domin ya nuna cewa yana kula da mu, ya gaya mana abubuwa masu yawa game da nasara da kuma hasara. Hakika, sa’ad da yake magana game da mutumin da ya mai da hankali ga abin da Allah ya ce, Littafi Mai Tsarki ya ce da babbar murya: “Iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka.”—Zabura 1:3.
Idan haka ne, me ya sa yawancin mutane ba sa yin nasara, farin ciki, da kuma rayuwa mai gamsarwa? Bincika wannan sashen na zabura zai ba mu amsar kuma zai nuna mana yadda za mu yi nasara.
“Shawarar Miyagu”
Mai zabura ya yi gargaɗin haɗarin da ke tattare da bin “shawarar miyagu.” (Zabura 1:1) Babban “Mugun” shi ne Shaiɗan Iblis. (Matta 6:13) Nassosi ya gaya mana cewa shi ne “sarkin duniyan nan” kuma “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (Yohanna 16:11; 1 Yohanna 5:19) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa yawancin shawarar da ake ji a duniya a yau tana nuna tunanin mugun.
Wane irin shawara ce miyagun mutane suke ba da wa? Gabaki ɗaya, miyagu suna rena Allah. (Zabura 10:13) Shawararsa wadda ta yi watsi ko kuwa ta rena Allah, duk ta kewaye mu. Mutanen zamani suna ɗaukaka “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi.” (1 Yohanna 2:16) Hanyoyin watsa labarai suna ta cusa mana ra’ayin “ka sami abin da za ka iya samu a rayuwa.” A duka duniya, kamfanoni suna kashe fiye da dala biliyan 500 a kowace shekara don yin tallar da za ta motsa mutane su sayi kayansu, ko da masu sayayya suna bukata ko ba sa bukata. Wannan tallar ta canja halayen mutane game da yin sayayya. Ta canja ra’ayin mutane game da yin nasara.
A sakamakon haka, yawancin mutanen da suka sami abubuwan da ba su taɓa mafarkin samu ba a dā, sun ci gaba da neman ƙarin abin duniya. Ra’ayin shi ne idan ba ka da waɗannan abubuwan, ba za ka taɓa yin farin ciki ko nasara ba. Wannan ra’ayin ƙarya ne kuma “ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.”—1 Yohanna 2:16.
Mahaliccinmu ya san abin da zai sa mu yi nasara. Shawararsa ta bambanta da “shawarar miyagu.” Saboda haka, idan mutum yana neman albarkar Allah amma kuma yana bin hanyar duniya ta yin nasara, kamar mutumin yana tafiya ne a kan hanyoyi biyu a lokaci ɗaya. Kuma hakan ba zai yiwu ba. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Kada ku biye wa zamanin nan”!—Romawa 12:2.
Kada ka Bari Duniya ta Mulmula Ka
Wannan duniyar da take ƙarƙashin ikon Shaiɗan tana nuna cewa ta damu da lafiyarmu. Amma, muna bukatar mu mai da hankali. Amma, ka tuna cewa Shaiɗan ya ruɗi mace ta farko Hauwa’u domin son kansa. Kuma ya yi amfani da ita ta ruɗi Adamu ya yi zunubi. A yau, Shaiɗan yana yin amfani da mutane su sanar da mugun shawararsa.
Alal misali, David yana ba da ƙarin lokaci a wurin aikinsa kuma yana yawan tafiya na kasuwanci. “Ina barin gida da sassafen Litinin kuma in dawo ranar Alhamis da yamma,” in ji David. Ganin cewa yana bukatar ya yi waɗannan sadaukarwa idan yana son ya yi nasara a wannan duniyar, abokansa na kud da kud, ’yan’uwansa, da kuma abokan aikinsa sun umurci David: “Ka yi waɗannan abubuwan domin iyalinka.” Suna tunanin cewa zai yi waɗannan abubuwan ne kawai na ɗan shekaru har ya yi nasara. David ya ce: “Suna faɗin cewa hakan zai fi biyan bukatar iyalina domin zan samu kuɗi mai yawa, kuma hakan zai iya sa in yi nasara. Ko da yake ba na tare da iyalina, abokai na sun sa na yarda cewa ina ba iyalina abubuwan da suke bukata.” Shi ya sa yawancin mutane kamar David suke aiki tuƙuru don su ba iyalinsu duk abin da suke bukata. Amma bin irin wannan shawarar zai iya kawo nasara? Menene ainihin abin da iyali take bukata?
David ya sami amsar wannan tambayar sa’ad da ya yi wata tafiya ta kasuwanci. “Ina magana da ɗiyata Angelica a kan waya, sai ta ce mini: ‘Baba, me ya sa ba ka son ka zauna tare da mu a gida?’ Hakan ya sa ni baƙin ciki ƙwarai,” in ji David. Abin da ɗiyarsa ta ce ya ƙarfafa shi ya yi murabus daga aikinsa. David ya yanke shawarar ba iyalinsa ainihin abin da suke bukata, wato lokaci, da kuma kasancewa tare da su.
Bin Shawarar Allah Yana Kawo Nasara
Ta yaya za ka iya yin rigakafin bayanai masu ruɗarwa da suka zama ruwan dare a wannan duniyar? Mai zabura ya gaya mana cewa mutum mai nasara kuma mai farin ciki shi ne wanda yake ‘marmarin shari’a ta Ubangiji; kuma a cikin shari’arsa ya kan riƙa tunani dare da rana.’—Zabura 1:2.
Sa’ad da Allah ya naɗa Joshua ya zama shugaban al’ummar Isra’ila, an gaya masa: “Za ka riƙa bincikensa [Kalmar Allah] dare da rana.” Hakika, karanta da kuma yin bimbini a kan Kalmar Allah na da muhimmanci, amma Joshua na bukatar ya ‘kiyaye ya kuma aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki.’ Karanta Littafi Mai Tsarki kawai ba shi ne zai sa ka yi nasara ba. Dole ne ka yi amfani da abin da ka karanta. Jehobah ya gaya wa Joshua: “Da hakanan za ka sa hanyarka ta yi albarka, da hakanan kuma za ka yi nasara.”—Joshua 1:8.
Ka yi tunanin ɗan ƙaramin yaron da ke zaune a kan cinyar babansa sa’ad da suke karanta wani labari mai daɗi tare. Ko sau nawa ne suka taɓa karanta labarin tare, za su dinga tuna wannan lokacin. Hakazalika, mutumin da ke ƙaunar Allah zai dinga marmarin karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana, wannan lokaci ne mai kyau da ya keɓe da Ubansa na samaniya. Ta wajen bin shawara da ja-gorar Jehobah, wannan mutumin zai zama “kamar itacen da aka dasa a magudanan ruwaye, wanda yana bada ’ya’yansa a cikin kwanakinsa; ganyensa ba ya yi yaushi ba; kuma cikin iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka.”—Zabura 1:3.
Icen da mai zabura ya ambata ba wai ya fito hakan nan ba ne kawai. An dasa shi ne kusa da magudanar ruwa kuma mai shi na kula da shi. Hakazalika, Ubanmu na sama yana gyara da kuma daidaita tunaninmu ta shawarar da ke cikin Nassosi. A sakamakon haka, muna nuna halayen da suka jitu da shawarar Allah.
Amma, “ba hakanan miyagu su ke ba.” Ko da yake sukan bayyana kamar suna da arziki, sakamakonsu na zama abin tausayi. “Ba za su tsaya a cikin ranar shari’a ba.” Maimakon haka, “hanyar miyagu za ta lalace.”—Zabura 1:4-6.
Saboda haka, kada ka bari duniya ta mulmula makasudinka da darajarka. Ko da kana da baiwar da za ta sa ka yi nasara a wannan duniyar, ka mai da hankali da yadda kake yin amfani da baiwarka ko yadda duniya take amfani da ita. Biɗan abubuwan duniya marar amfani na iya sa mutum ya yi “yaushi.” A wani ɓangare kuma, kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah na kawo nasara da farin ciki na gaskiya.
Yadda Za Ka Iya Yin Nasara
Me ya sa idan mutum ya bi shawarar Allah zai yi nasara a duka abin da yake yi? Ba wai mai zabura na magana ba ne game da yin nasara a wannan duniyar. An haɗa nasarar mutum mai ibada da yin nufin Allah, kuma nufin Allah na yin nasara a kowane lokaci. Bari mu ga yadda bin mizanan Littafi Mai Tsarki zai iya sa mu yi nasara.
Iyali: Nassosi ya aririci maza “su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu,” kuma an umurci mace Kirista ta “ga kwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:28, 33) An ƙarfafa iyaye su kasance tare da ’ya’yansu, su yi dariya tare, kuma su koya musu abubuwa masu muhimmanci a rayuwa. (Kubawar Shari’a 6:6, 7; Mai-Wa’azi 3:4) Kalmar Allah ta shawarci iyaye: “Kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi.” Idan aka bi wannan shawarar, zai yi wa yara sauƙi su “yi biyayya da waɗanda suka haife” su, kuma su ‘girmama ubansu da uwarsu.’ (Afisawa 6:1-4) Bin wannan hurarriyar shawarar zai iya kawo nasara a rayuwar iyali.
Abokai: Yawancin mutane suna son abokai. Muna ƙaunar mutane kuma muna son su ƙaunace mu. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su “yi ƙaunar juna.” (Yohanna 13:34, 35) A cikin mabiyan, muna samun abokai da muke ƙauna da kuma waɗanda muka amince da su, waɗanda za mu iya gaya wa sirrin mu. (Misalai 18:24) Mafi muhimmanci shi ne, idan muka yi amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki, za mu iya “kusato ga Allah,” kuma kamar Ibrahim, za a iya kiranmu “abokin Allah.”—Yaƙub 2:23; 4:8.
Manufa a Rayuwa: Maimakon mu kasance marar manufa a rayuwa, waɗanda suka yi nasara suna samun ma’ana da manufa a rayuwa. Rayuwarsu ba ta dangana a kan yanayi marar kan gado na wannan zamanin ba. Makasudinsu na sa su sami gamsuwa na dindindin, sa’ad da suka mai da hankali ga ainihin manufa ta rayuwa. Menene zai sa rayuwar mutum ta kasance da manufa? “Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.”—Mai-Wa’azi 12:13.
Bege: Yin abota da Allah na ba mu bege don nan gaba. Manzo Bulus ya aririci Kiristoci kada “su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah.” Da haka, “suna ajiye wa kansu tushe mai-kyau domin wokaci mai-zuwa, da za su ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.” (1 Timothawus 6:17-19) Wannan rayuwa ta ainihi za ta zo nan ba da daɗewa ba sa’ad da Mulkin Allah na samaniya zai kawo Aljanna a duniya.—Luka 23:43.
Ba wai ba za ka fuskanci matsaloli ba idan ka yi amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki, amma za ka guje wa yawancin baƙin ciki da damuwa da miyagu suke jawo wa kansu. David da aka ambata a baya, da kuma mutane da yawa kamarsa sun koyi muhimmancin yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki a rayuwarsu. Bayan ya sami aikin da zai ba shi isashen lokaci, David ya ce: “Ina godiya sosai domin dangantakar da ke tsakanina da matata da ’ya’yana da kuma gatar da nike da ita na yi wa Jehobah Allah hidima a matsayin dattijo.” Babu shakka, shi ya sa mai zabura ya ce game da mutumin da ya mai da hankali ga shawarar Allah: “Cikin iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka”!
[Taswira a shafi na 5]
MATAKAI BIYAR DON YIN NASARA
1 Ka guje wa barin abubuwan duniyar nan su mulmula ka.
Zabura 1:1; Romawa 12:2
2 Ka karanta Kalmar Allah a kowace rana kuma ka yi bimbini a kanta.
Zabura 1:2, 3
3 Ka yi amfani da shawarar Littafi Mai Tsarki a rayuwarka.
Joshua 1:7-9
4 Ka bari Allah ya zama abokinka.
5 Ka ji tsoron Allah, kuma ka kiyaye dokokinsa.
Mai-Wa’azi 12:13
[Hotuna a shafi na 6]
Kana bin matakan da za su sa ka yi nasara?