Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 12/1 pp. 25-27
  • Darussa Daga Littafin Waƙar Waƙoƙi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Waƙar Waƙoƙi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “KADA KU TADA ƘAUNA” A ZUCIYATA
  • (Waƙar Waƙoƙi 1:1–3:5)
  • “DON MI KU KE SO KU DUBI YAR SHULEM?”
  • (Waƙar Waƙoƙi 3:6–8:4)
  • “HARSHEN WUTA MAI-TSANANI NA UBANGIJI”
  • (Waƙar Waƙoƙi 8:5-14)
  • Ƙauna ta Gaskiya Za Ta Yiwu Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Yi Koyi da Bashulammiya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Shi Misali Mai Kyau Ne A Gare Ka Ko Kuma Kashedi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 12/1 pp. 25-27

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Waƙar Waƙoƙi

“KAMAR lily cikin ƙayayuwa, Hakanan masoyiyata cikin yan mata ta ke.” “Kamar itacen apple a cikin itatuwan jeji, Hakanan ƙaunatacena ya ke a ciki ’ya’ya maza.” “Wace ce wannan mai-leƙe kamar safiya, Kyakyawa ce kamar wata, Garai kamar rana?” (Waƙar Waƙoƙi 2:2, 3; 6:10) Waɗannan surori ne masu kyau daga littafin Waƙar Waƙoƙi na Littafi Mai Tsarki! Littafin na cike da waƙa da ke da ma’ana da kayatarwa da ake kira waƙa mafi daɗi.

Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā ne ya rubuta littafin, wataƙila a shekara ta 1020 K.Z., a farkon sarautarsa ta shekara 40, wannan waƙar labarin soyayya ce tsakanin wani makiyayi saurayi da wata budurwa mai suna ’yar Shulem. Wasu kuma da aka ambata a cikin waƙar sune uwar yarinyar da yayyenta, “yan matan Urushalima,” da kuma “yan matan Sihiyona.” (Waƙar Waƙoƙi 1:5; 3:11) Zai yi wuya mai karanta Littafi Mai Tsarki ya gano duka waɗanda suka yi magana a cikin Waƙar Waƙoƙi, amma hakan zai yiwu ta wajen tattauna abin da suka ce ko kuwa abin da aka faɗa game da su.

Da yake sashe ne na Kalmar Allah, saƙon da ke cikin Waƙar Waƙoƙi na da muhimmanci sosai domin dalilai biyu. (Ibraniyawa 4:12) Na ɗaya, ya koya mana abin da ƙauna ta gaskiya take nufi tsakanin mace da namiji. Na biyu, waƙar ta bayyana irin ƙaunar da ke tsakanin Yesu Kristi da kuma ikilisiyar shafaffun Kiristoci.—2 Korinthiyawa 11:2; Afisawa 5:25-31.

“KADA KU TADA ƘAUNA” A ZUCIYATA

(Waƙar Waƙoƙi 1:1–3:5)

“Shi yi mani sumba da sumbobin bakinsa: Gama ƙaunarka ta fi gaban ruwan anab.” (Waƙar Waƙoƙi 1:2) Kalaman da ke cikin Waƙar Waƙoƙi sun soma ne da kalaman wata budurwa mai tawali’u wadda aka kawo cikin tantin sarauta na Sulemanu. Ta yaya ta shiga wurin?

“Yan’uwana sun yi fushi da ni,” in ji ta. “Suka sa ni in lura da gonakin anab.” Yayyen ta sun yi fushi da ita domin makiyayin da take so ya gayyace ta su fita tare. Don su hana ta fita, sun umurce ta ta kula da “ƙananan yanyawan nan, masu-ɓatan gonakin anab.” Wannan aikin ya kai ta kusa da gidan Sulemanu. An lura cewa kyakkyawa ce sa’ad da ta je “wurin gonar gyaɗa,” sai aka kai ta gidan.—Waƙar Waƙoƙi 1:6; 2:10-15; 6:11.

Sa’ad da budurwar ta soma ɗokin ganin makiyayin da take ƙauna, ’yan matan Urushalima sun gaya mata ta ‘tashi ta bi sawun garke’ don nemansa. Amma Sulemanu ya ƙi ya yarda ta tafi. Sa’ad da yake yaba wa kyaun surarta, ya yi mata alkawarin “tubkar zinariya . . . da ado na azurfa.” Hakan bai burge ta ba. Saurayin makiyayi ya shiga cikin gidan Sulemanu, sa’ad da ya ganta, ya ce: “Kyakyawa ce ke, masoyiyata, i, kyakyawa ce.” Budurwar ta ce wa ’yan matan Urushalima su rantse: “Kada ku tada ƙauna, kada ku falkadda ita, sai ta yarda tukuna.”—Waƙar Waƙoƙi 1:8-11, 15; 2:7; 3:5.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:2, 3—Me ya sa tuna kalaman soyayya na makiyayin ya yi kama da ruwan anab kuma sunansa kamar man ƙamshi? Kamar yadda ruwan anab ke wartsakar da zuciyar mutum da kuma yadda man da ake shafawa a kai ke wartsakarwa, tuna ƙaunar da saurayin ke yi mata da kuma sunansa na ƙarfafa budurwar. (Zabura 23:5; 104:15) Kiristoci na gaskiya, musamman shafaffu, suna samun ƙarfafa sa’ad da suka yi bimbini a kan ƙaunar da Yesu Kristi ya nuna musu.

1:5—Me ya sa budurwar ta ce ita baƙa ce kamar “tents na Kedar”? Gashin akuya da aka yi yadi da shi, yana da amfani mai yawa. (Litafin Lissafi 31:20) Alal misali, ana yin amfani da “turkuɗa na gashin awaki” a yi “tent [na] marufin mazauni.” (Fitowa 26:7) Kamar tantin makiyaya Larabawa a yau, wataƙila an yi tantin Kedar ne da gashin baƙar akuya.

1:15—Menene saurayi makiyayi yake nufi sa’ad da ya ce:“Idanunki na kurciya ne”? Saurayin yana nufin cewa idanun budurwarsa suna da taushi, kamar na kurciya.

2:7; 3:5—Me ya sa aka ce ’yan matan Urushalima su rantse da “bareyi da batsiyoyi na jeji”? Bareyi da batsiyoyi suna da nagari da kyau. Da haka, budurwa ’yar Shulem ta ce ’yan matan Urushalima su rantse da duk wani abu mai nagari da kyau, don su guje wa ta da ƙauna a cikin zuciyarta.

Darussa Dominmu:

1:2; 2:6. Kalaman da suke nuna ƙauna suna da kyau a lokacin zawarci. Amma, waɗanda suke zawarci su mai da hankali sosai cewa kalamansu ta ƙauna ce ta gaskiya ba sha’awa marar kyau ba, wadda za ta sa su yin lalata.—Galatiyawa 5:19.

1:6; 2:10-15. Yayyen ’yar Shulem ba su ƙyale ƙanwarsu ta bi masoyinta zuwa cikin duwatsu inda babu kowa ba, amma hakan ba ya nufin cewa ba ta da ɗabi’a mai kyau ko manufar da ta dace ba. Amma, sun yi haka ne don su hana ta faɗawa cikin yanayin da zai iya sa su cikin gwaji. Darassi ga waɗanda suke zawarci shi ne su guje wa wuraren da babu kowa.

2:1-3, 8, 9. Ko da yake tana da kyau, budurwa ’yar Shulem ta kwatanta kanta da “rose [wani fure] na filin jeji.” Domin kyaunta da kuma amincinta ga Jehobah, saurayin makiyayi ya ɗauke ta “kamar lily cikin ƙayayuwa.” Saurayin kuma fa? Domin kyakkyawa ne, a gareta ya yi kama da “barewa.” Kuma mutum ne mai bangaskiya da aminci ga Jehobah. “Kamar itacen apple [da ke ba da inuwa da ’ya’ya] a cikin itatuwan jeji, Hakanan ƙaunatacena ya ke a ciki ’ya’ya maza,” in ji ta. Bangaskiya da ba da kai ga Allah sune halayen da ya kamata mutum ya duba a cikin wadda zai aura.

2:7; 3:5. Wannan budurwar ba ta so Sulemanu ba. Kuma ta ce ’yan matan Urushalima su rantse cewa ba za su sa ta ƙaunaci wani in ba saurayi makiyayi ba. Bai dace ba a soma soyayya da kowane irin mutum ba. Kirista marar aure da ke son ya ko ta yi aure ya kamata ya ko ta auri amintaccen bawan Jehobah.—1 Korinthiyawa 7:39.

“DON MI KU KE SO KU DUBI YAR SHULEM?”

(Waƙar Waƙoƙi 3:6–8:4)

Wani abu na “tasowa daga jeji kamar umudan hayaƙi.” (Waƙar Waƙoƙi 3:6) Menene ’yan matan Urushalima suka gani sa’ad da suka fita su yi kallo? Sulemanu ne da bayinsa suke shigowa cikin birni! Kuma sarkin ya taho da budurwar ’yar Shulem.

Saurayin makiyayi ya bi budurwar kuma ya nemi hanyar ganinta. Sa’ad da ya tabbatar mata da ƙaunarsa, ta bayyana muradinta na barin birnin, tana cewa: “Har rana ta yi sanyi, inuwa kuma ta shude, Zan tan abina wurin dutsen myrrh, Da tudun lubban.” Ta gayyaci makiyayin ya “shigo gonatasa, Shi ci abincinsa, ’ya’yan daɗi.” Sai ya ce: “Ga shi, na zo cikin gonata, ya ƙanuwata, amaryata.” Sai ’yan matan Urushalima suka ce musu: “Ku ci, ya abokai; Ku sha, I, ku sha ƙauna a yalwace.”—Waƙar Waƙoƙi 4:6, 16; 5:1.

Bayan ta faɗi mafarkin da ta yi ga ’yan matan Urushalima, budurwa ’yar Shulem ta ce musu: “Raina ya gundura da ƙauna.” Sun yi tambaya: “A ina ƙaunatacenki ya fi wani ƙaunatace?” Sai ta ce: “Ƙaunatacena fari ne lafiyayye ne, Mafifici ne a cikin zambar goma.” (Waƙar Waƙoƙi 5:2-10) Ga kirarin da Sulemanu ya yi mata, ta amsa cikin tawali’u: “Don mi ku ke so ku dubi yar Shulem.” (Waƙar Waƙoƙi 6:4-13) Ganin cewa wannan dama ce mai kyau na shawo kanta, sarkin ya ci gaba da yi mata kalamai masu daɗi. Amma, budurwar ta manne wa ƙaunar da take yi wa saurayin makiyayi. Daga baya, Sulemanu ya ƙyale ta ta tafi.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

4:1; 6:5—Me ya sa aka kwatanta gashin budurwar da na “garken awakai”? Kwatancin ya nuna cewa gashinta yana ƙyalƙyali kuma yana da kauri kamar baƙin gashin akuya.

4:11—Menene ma’anar laɓɓan ’yar Shulem da ke ɗigar da saƙar zuma da kuma ‘zuma da nono da ke ƙarƙashin harshenta’? Saƙar zuma ta fi zumar da ta sha iska daɗi. Kwatancin nan zuma da madara da ke ƙarƙashin harshen budurwar na nanata nagarta da kuma kyaun kalaman da suka fito daga bakin ’yar Shulem.

5:12—Menene ma’anar kalmar “idanunsa kamar kurciyoyi a bakin rafufuka; Wankakku ne da madara”? Budurwar tana magana ne game da idanun saurayinta masu kyau. Wataƙila tana kwatanta baƙaƙe da kuma fararen kwayoyin idanunsa ne da kurciyoyin da suke wanka a cikin madara.

5:14, 15—Me ya sa aka kwatanta hannuwa da kafafuwan makiyayin kamar haka? Budurwar tana kiran yatsun makiyayin finjalin zinariya, farcensa kuma topaz. Ta kamanta kafafuwansa da “umudan marble” domin suna da kwari da kuma kyau.

6:4—Me ya sa aka kwatanta budurwar da Tirzah? Joshua ya kame wannan birni na Ka’anan, kuma bayan zamanin Sulemanu, ya zama birnin tarayya na masarautar ƙabilu goma na arewacin Isra’ila. (Joshua 12:7, 24; 1 Sarakuna 16:5, 6, 8, 15) Wani littafi ya ce: “Kamar birnin yana da kyau sosai, shi ya sa aka ambata shi a nan.”

6:13—Menene “rawan Mahanaim”? Za a kuma iya juya wannan furcin ya zama “rawan sansani biyu.” Birnin da ke amsa sunan nan na gabashin Rafin Urdun kusa da kwazazzabon Jabbok. (Farawa 32:2, 22; 2 Samuila 2:29) “Rawan sansani biyu” wataƙila yana nuni ne ga wata rawa da ake yi a wannan birnin a wani biki.

7:4—Me ya sa Sulemanu ya kwatanta wuyan ’yar Shulem da “hasumiya ta hauren giwa”? A dā, budurwar ta sami wannan yabon daga wurin Sulemanu: “Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda ne.” (Waƙar Waƙoƙi 4:4) Hasumiya tana da tsawo kuma ba ta da faɗi, hauren giwa kuwa sumul yake. Wuyan budurwar marar kauri da kuma kyaunsa ne ya burge Sulemanu.

Darussa Dominmu:

4:1-7. Ta wajen ƙin maganganu masu daɗi da Sulemanu ya yi mata, ko da yake ajiza ce, ’yar Shulem ta kasance da aminci. Amincinta ya ƙara mata kyaun sura. Ya kamata mata Kiristoci na gaskiya su kasance haka a yau.

4:12. Kamar lambu mai kyau da aka shinge da itatuwa ko bango wanda za a iya shigarsa ne kawai ta rufaffen kofa, budurwa ’yar Shulem ta nuna soyayyarta ne kawai ga mijin da za ta aura. Wannan misali ne mai kyau ga Kiristoci maza da mata da ba su yi aure ba!

“HARSHEN WUTA MAI-TSANANI NA UBANGIJI”

(Waƙar Waƙoƙi 8:5-14)

“Wacece wannan mai-fitowa daga cikin jeji, Tana dogara ga ƙaunatacenta?” in ji yayun ’yar Shulem sa’ad da suka ganta tana dawowa gida. A dā wani a cikinsu ya ce: “Idan bango ta zama, Mu a rufe ta da ginin azurfa: Idan ƙofa ce, Sai mu kewaye ta da kātākan cedar.” Tun da an riga an gwada ƙaunar ’yar Shulem kuma an ga cewa tana da aminci, ta ce: “Ni a dā bango ne, mamana kuma kamar hasumiyansa: Sa’annan a gareshi na zama mai-samun tagomashi.”—Waƙar Waƙoƙi 8:5, 9, 10.

Ƙauna ta gaskiya “harshen wuta mai tsanani na Ubangiji” ne. Me ya sa? Domin Jehobah ne tushen irin wannan ƙaunar. Shi ne ya sa muradin nan na yin ƙauna a cikinmu. Wuta ce da ba za a iya kashewa ba. Waƙar Waƙoƙi ta ce ƙaunar da ke tsakanin mace da namiji tana da “ƙarfi kamar mutuwa.”—Waƙar Waƙoƙi 8:6.

Wannan waƙar ta Sulemanu ta ƙara haske a kan gamin da ke tsakanin Yesu Kristi da kuma ‘amaryarsa’ na samaniya. (Ru’ya ta Yohanna 21:2, 9) Ƙaunar da ke tsakanin Kiristoci shafaffu ta wuce ƙaunar da ke tsakanin mace da namiji. Wannan rukuni na amarya sun manne wa bautarsu. Cikin ƙauna, Yesu ya ba da rayuwarsa ga “waɗansu tumaki.” (Yohanna 10:16) Duka masu bauta ta gaskiya, suna iya yin koyi da misalin ’yar Shulem na ƙaunarta marar jijjiga da ba da kai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba