Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 10/1 p. 31
  • Ka Sa Yin Bimbini Ya Zama Abin Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sa Yin Bimbini Ya Zama Abin Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 10/1 p. 31

Ka Sa Yin Bimbini Ya Zama Abin Farin Ciki

GA WASU mutane yin bimbini mai yiwuwa ya zama da ban tsoro. Suna ganin yin bimbini hakki ne mai sa sanyin gwiwa, mai bukatar a mai da hankali sosai. Waɗannan mai yiwuwa za su ji kunya saboda yadda suka yi banza da yin bimbini, musamman idan sun karanta muhimmancin sa. (Filibbiyawa 4:8) Amma dai, yin bimbini bisa gaskiya da muka koyo game da Jehobah, halayensa masu kyau, abin da ya cim ma, farillansa, da kuma manufarsa, za su iya zama hanya mafi kyau na yin amfani da lokaci. Me ya sa?

Jehobah Allah ne Masaraucin sararin samaniya kuma yana aiki sosai don ya cika manufarsa mafi girma. (Yohanna 5:17) Duk da haka, yana kula da tunanin kowane mai bauta masa. Mai zabura Dauda ya san da haka shi ya sa ya rubuta da taimakon Allah: “Ya Ubangiji, kā bincike ni, kā kuwa san ni. Zamana da tashina ka sani, kā fahimci tunanina tun daga nesa.”—Zabura 139:1, 2.

Da farko, wani zai iya tunanin cewa kalmar mai zabura na kashe gwiwa. Zai iya yin tunani, ‘Ko da yake Allah “yana nesa,” amma zai iya sanin kowane mummunan tunani da ke cikin zuciya ta.’ Hakika, irin wannan tunanin na da amfani idan muka sani cewa yana kula da mummunan tunaninmu. Zai iya taimakonmu mu yi yaƙi da tunanin da ba daidai ba ne, kuma yayin da muka yi irin wannan tunani, muka faɗi zunubanmu ga Allah da gabagaɗi zai gafarta mana saboda bangaskiyarmu ta wurin fansar Yesu. (1 Yohanna 1:8, 9; 2:1, 2) Duk da haka mu tuna cewa Jehobah yana lura da masu binsa a hanya mai kyau. Zai kula da mu sosai idan muka yi tunani game da shi.

Mai yiwuwa za ka yi tambaya, “Jehobah yana kula da dukan kyawawan tunanin miliyoyin mutane masu bauta masa kuwa?” Babu shakka yana kulawa. Yesu ya maimaita sha’awar Jehobah a gare mu yayin da ya ce Jehobah yana kula har da ƙananan gwarare, ya kuma daɗa: “Kun fi gwarare masu-yawa daraja.” (Luka 12:6, 7) Gwarare ba za su iya yin tunani game da Allah ba. Saboda haka, idan yana kula da su, zai kula da mu, ya kuma yi farin ciki idan muka bauta masa! Kamar Dauda, da gabagaɗi za mu iya yin addu’a: “Bari . . . tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.”—Zabura 19:14.

An kafa wani tabbaci da ya nuna cewa Jehobah yana kula da bimbinin masu bauta masa cikin aminci a hurarriyar kalmar annabi Malachi. Game da lokacinmu, ya ce: ‘Sa’annan su waɗanda suka ji tsoron Ubangiji suka yi zance da junansu; Ubangiji kuma ya kasa kunne, ya ji, aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda su ke jin tsoron Ubangiji, masu-tunawa da sunansa.’ (Malachi 3:16) Idan muka tuna cewa Jehobah yana “kasa kunne” idan muka yi tunani a kansa, zai iya sa mu sa bimbini na ibada ya zama abin farin ciki. Saboda haka, bari mu yarda da kalmar mai zabura Dauda wanda ya rubuta: “Zan yi ta bimbinin dukan aikinka, in yi maganar zuci a kan aike aikenka.”—Zabura 77:12.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba