Za Ka Iya Rayuwa Har Abada
YAWANCIN mutane masu bin addinai a duniya suna fatan samun rai na har abada a hanyoyi dabam dabam. Kowane addini na da nasa bayani game da rai na har abada, amma suna da bege ɗaya, wato rayuwa cikin yanayi mai kyau ba tare da tsoron mutuwa ba. Abin da kake sha’awa ke nan? Ta yaya za a ba da bayanin tasirin irin wannan koyarwa? Za a taɓa cim ma begen rai na har abada kuwa?
Nassosi sun nuna cewa Mahalicci ya saka sha’awar rai madawwami a cikin zuciyar ’yan adam tun farkon lokacin da ya halicci ma’aurata na fari. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Allah] ya kuma sa madawaman zamanai a cikin zuciyarsu.”—Mai-Wa’azi 3:11.
Don su biya bukatar wannan sha’awa ta rayuwa ta har abada, dole ne ma’aurata na farkon su amince da ikon Allah na tsai da abin da ke nagarta da abin da ke mugunta. Da a ce sun yi hakan, da Jehobah ya sa sun cancanci “rai har abada” a cikin lambun Adnin, gidan da ya shirya musu.—Farawa 2:8; 3:22.
An Yi Hasarar Rai Madawwami
Labarin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya shuka “itace na sanin nagarta da mugunta” a cikin lambun, ya hana Adamu da Hauwa’u su ci ’ya’yan kuma idan suka ci za su mutu. (Farawa 2:9, 17) Idan Adamu da Hauwa’u suka ƙi cin wannan ’ya’yan itace za su nuna wa Allah cewa sun amince da ikonsa. Idan kuma suka ci ’ya’yan itacen, wannan zai nuna cewa sun ƙi ikon Allah. Adamu da Hauwa’u sun ƙi bin umurnin Jehobah kuma suka bi Shaiɗan, halitta ta ruhu da ya yi tawaye ga ikon Allah. Domin haka, Allah ya ƙuduri aniya cewa Adamu da Hauwa’u ba su dace su rayu har abada ba.—Farawa 3:1-6.
Allah ya ba su damar rai ko mutuwa, wanzuwa ko rashin wanzuwa. Sakamakon rashin biyayya shi ne mutuwa da ƙarshen wanzuwarsu gaba ɗaya. Bai zai yiwu ba Adamu da Hauwa’u ko kuma wani cikin tsaransu ya ci gaba da rayuwa ta wani dabo ko kuma kurwa da ba ta mutuwa.a
Dukan ’ya’yan Adamu sun sha wahala domin tawayensa. Manzo Bulus ya ba da bayanin sakamakon hakan. Ya rubuta: “Ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da shi ke duka sun yi zunubi.”—Romawa 5:12.
Rai na Har Abada Zai Yiwu Kuma
Manzo Bulus ya kwatanta yanayin tsaran Adamu ta wajen kamanta shi da bawa na ƙarni na farko. Domin zunubi da suka gada, an haifi ’ya’yan Adamu da Hauwa’u “bayi ne na zunubi” da dole su mutu. (Romawa 5:12; 6:16, 17) Da a ce ba su tsira wa wannan ba da Jehobah bai magance matsalar ba ta wajen sayan ’yancin irin wannan bayin. Bulus ya ba da bayani: “Hakanan fa kamar yadda shari’a ta zo bisa dukan mutane zuwa koyarwa ta wurin takar shari’a ɗaya [na Adamu]; hakanan kuma ta wurin aiki guda ɗaya mai-adalci kyautan ta zo ga dukan mutane zuwa kuɓutar rai.” Wannan ‘aiki mai-adalci’ ya sa Yesu ya yi hadayar nasa kamiltaccen rai don “fansar dukan mutane.” Jehobah ya amince da ikon fansar don a saki ’yan adam daga “hukuncin” “takar shari’a.”—Romawa 5:16, 18, 19; 1 Timothawus 2:5, 6.
Shi ya sa masana kimiyya ba za su taɓa sanin abin da ke hana rayuwa ta har abada a tsarin ƙwayoyin hali na ’yan adam ba, amma za a iya sanin wannan a wani waje. Littafi Mai Tsarki ya ce, ’yan adam suna mutuwa don batun ɗabi’a da yin gaskiya, ba na tsarin ƙwayoyin hali ba. Wannan yana nufin cewa don a maido da rai na har abada, ana bukatar hadayar fansa ta Yesu. Fansar ta nuna cewa Allah mai adalci ne da kuma ƙauna ta alheri. To, su waye ne fansar za ta amfana kuma su sami rai na har abada?
Kyautar Rai na Har Abada
Jehobah Allah “tun fil’azal . . . ne Allah har abada.” Ba ya mutuwa. (Zabura 90:2) Yesu Kristi ne mutum na farko da Jehobah ya ba kyautar rai na har abada. Manzo Bulus ya ba da bayani: “Kristi da shi ke ya tashi daga matattu ba shi koma mutuwa ba; nan gaba mutuwa ba ta da sauran mulki a kansa.” (Romawa 6:9) Hakika, da yake kwatanta Yesu da aka ta da daga matattu da sarakunan duniya, Bulus ya kwatanta cewa shi kaɗai ne a cikinsu ba ya mutuwa. Yesu zai “dawama har abada.” Ransa “marar-matuƙa” ne.—Ibraniyawa 7:15-17, 23-25; 1 Timothawus 6:15, 16.
Ba Yesu kaɗai ba ne ya samu irin wannan kyautar. Kiristoci da aka shafa da ruhu da aka zaɓe su su yi sarauta ta samaniya mai ɗaukaka sun sami irin wannan tashin matattu na Yesu. (Romawa 6:5) Manzo Yohanna ya nuna cewa an ba wa mutane 144,000 wannan gatar. (Ru’ya ta Yohanna 14:1) Su ma sun sami madawwamin rai. Game da tashinsu daga matattu, Bulus ya ce: “Nama da jini ba su da iko su gāji mulkin Allah ba . . . ƙaho za shi yin ƙara, matattu kuma za su tashi marasa-ruɓuwa, mu kuma za mu sāke. Gama dole sai wannan mai-ruɓuwa za shi yafa rashin ruɓa, wannan mai-mutuwa kuwa zai yafa rashin mutuwa.” Mutuwa ba ta da iko a kan waɗanda suka sami irin wannan tashi daga matattu.—1 Korinthiyawa 15:50-53; Ru’ya ta Yohanna 20:6.
Wannan wahayi daga Allah abin ban al’ajabi ne. Mala’iku ma za su mutu, ko da su halittu ne na ruhu. Wannan gaskiya ne domin za a halaka halittu na ruhu da suka bi Shaiɗan wajen tawaye. (Matta 25:41) A wata sassa kuma, abokan sarautar Yesu sun sami kyautar madawwamin rai, da ya nuna cewa Jehobah ya amince da su sosai domin amincinsu.
Wannan yana nufin cewa mutane 144,000 ne kaɗai za su yi rayuwa har abada, idan aka gwada da ’yan adam biliyoyi da suka taɓa rayuwa? A’a. Bari mu ga abin da ya sa.
Rai Madawwami a Cikin Aljanna a Duniya
Littafin Ru’ya ta Yohanna a cikin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta taro da ba a iya ƙirgawa da aka ba wa kyautar rai madawwami a cikin aljanna a duniya. Waɗanda suka mutu amma aka tashe su kuma aka mai da musu ƙuruciyarsu da kuma ƙarfinsu suna cikin taron mutanen. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; 20:12, 13; 21:3, 4) An shigar da su “kogin ruwa na rai, mai-sheƙi kamar crystal, yana fitowa daga cikin kursiyin Allah.” A bakin kogin “akwai itace na rai . . . ganyayen itacen kuma domin warkarwar al’ummai.” Gayyatar Jehobah Allah ita ce: “Mai-jin ƙishi kuma, bari shi zo: wanda ya ke so, bari shi ɗiba ruwa na rai kyauta.”—Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2, 17.
Waɗannan itatuwa da ruwaye ba maganin ɗaurin rai ba ne kamar waɗanda masana magani da ’yan tonan ƙasa suke nema a dā ba. Maimakon haka, suna wakiltar tanadin Allah ta wurin Yesu Kristi don mai da ’yan adam zuwa kamilta da ya kasance a dā.
Allah bai canja nufinsa ya ba wa ’yan adam masu biyayya rai madawwami ba. Zai cika wannan nufin, don Jehobah mai aminci ne. Zabura 37:29 ta ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” Wannan alkawarin ya motsa mu tare da waɗanda aka ba wa madawwamin rai a samaniya, muna cewa: “Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai. Wanene za ya rasa jin tsoro, ya rasa ɗaukaka sunanka, ya Ubangiji? gama kai kaɗai mai-tsarki ne.”—Ru’ya ta Yohanna 15:3, 4.
Kana sha’awar kyautar rai madawwami mai tamani? Idan haka ne, dole ne ka nuna kai mai aminci ne kuma kana biyayya ga “Sarkin zamanai.” Kana bukatar ka koya game da Jehobah da kuma wanda ta wurinsa irin wannan rai zai yiwu, wato, Yesu Kristi. Za a ba kyautar “rai na har abada” ga waɗanda suke a shirye su amince da mizanan Allah na nagarta da mugunta.—Yohanna 17:3.
[Hasiya]
a Don cikakken bayani game da koyarwa ta kurwa da ba ta mutuwa, don Allah ka dubi mujallar nan Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu? da Shaidun Jehobah suka wallafa.
[Box/Hoto a shafi na 4]
Sha’awa ta Dindindin
Littafin Gilgamesh, wani labarin ɗan Mesofotamiya da ake ganin an rubuta a alif na biyu K.Z., ya kwatanta yadda jarumin ya nemi zama matashi har abada. Masarawa na dā suna ajiye gawa, da ra’ayin cewa kurwa da suka gaskata ba ta mutuwa za ta yi amfani da jikinta kuma. Shi ya sa ake cika wasu kaburbura na Masarawa da dukan abubuwa da mamacin zai bukata a rayuwansa bayan mutuwa.
A tsakanin masana ƙwayoyin rai na Sin, an soma imani a rai marar mutuwa a ƙarni na takwas K.Z., da kuma cewa zai yiwu a hana jiki mutuwa ta wurin maganin dabo har zuwa ƙarni na huɗu K.Z. ’Yan tarihin Turai na dā da masana ƙwayoyin rai na Larabawa sun nemi su yi nasu magani na rai. Wasu abubuwa da suka haɗa ya ƙunshi gubar gishiri, zaiba, da farar wuta. Ba a san ko mutane nawa ne suka sha gubar ba, da suke ƙoƙari su yi magungunan!
Wani lokaci an yaɗa labari game da Ruwan Ƙuruciya, wato, rafi da aka ce yana mai da kuzari ga waɗanda suka sha ruwansa.
[Box/Hotuna a shafi na 5]
Rayuwa Har Abada Za ta Gajiyar da Mutane Ne?
Wasu suna musu cewa rai na har abada zai gajiyar da mutane, wai za a “yi zaman banza ne” har abada. Wataƙila rai na har abada da suke tunaninsa shi ne irin salon rayuwa da yanayi na zamani, ga mutane da yawa irin wannan rayuwa tana gajiyarwa kuma ba ta da ma’ana. Amma, a cikin Aljanna da Allah zai kawo, ya yi wa ’yan adam alkawari “za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” (Zabura 37:11) Irin wannan rayuwar za ta ba ’yan adam zarafin samun ilimi na halittar Jehobah kuma su ba da lokaci wajen faɗaɗa iyawarsu, nazari, da ayyuka masu kyau da yanzu muna fatansu ne kawai.
Dokta Aubrey de Grey, wani masanin ƙwayoyin hali a Jami’an Cambridge da ya yi bincike game da yadda za a ƙara tsawon rayuwar mutane, ya ce: “Mutane masu ilimi sosai da suke da lokacin yin amfani da iliminsu ba sa gajiya a yau, kuma ba sa taɓa tunanin rashin sababbin abubuwa da suke son su yi ba.” Duk da haka, hurarriyar Kalmar Allah ta ce, “mutum ba za ya bincike aikin Allah ba da ya yi tun farko, har ƙarshe kuma.”—Mai-Wa’azi 3:11.