Cika Farillan Baftisma Na Kirista
“Me za ya hana a yi mini baftisma?”—AYUKAN MANZANNI 8:36.
1, 2. Ta yaya ne Filibus ya soma tattaunawa da wani ma’aikaci na Habasha, kuma menene ya nuna cewa mutumin yana son bauta ta gaskiya?
SHEKARA ɗaya ko biyu bayan mutuwar Yesu, wani babban ma’aikaci na gwamnati ya yi kudu kan hanyarsa daga Urushalima zuwa Gaza. Yana da sauran tafiya mai gajiyarwa na kusan mil dubu ɗaya da zai yi a cikin karusarsa. Wannan mutumin mai ibada ya zo Urushalima daga Habasha don ya bauta wa Jehobah. A kan doguwar hanyarsa ta komawa gida, ya yi amfani da lokacinsa cikin hikima wajen karanta Kalmar Allah. Bangaskiyarsa tana da yawa. Jehobah ya lura da wannan sahihin mutumin, kuma ta mala’ikansa, ya ja-goranci almajiri Filibus ya yi masa wa’azi.—Ayukan Manzanni 8:26-28.
2 Bai yi wa Filibus wuya ba ya soma tattaunawa da wannan mutumin, domin ma’aikacin daga ƙasar Habasha ya ɗaga murya ne yana karatu, al’adarsu ke nan a dā. Hakan ya ba Filibus zarafin jin abin da mutumin yake karantawa daga littafin Ishaya. Wata tambaya mai sauƙi da Filibus ya yi wa mutumin ce ta ta da marmarinsa: “Ka fahimci abin da ka ke karantawa?” Hakan ya sa suka tattauna Ishaya 53:7, 8. A ƙarshe, Filibus “ya yi masa wa’azin Yesu.”—Ayukan Manzanni 8:29-35.
3, 4. (a) Me ya sa Filibus ya yi wa mutumin Habasha baftisma ba tare da ɓata lokaci ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna yanzu?
3 A cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, mutumin Habashan ya fahimci matsayin Yesu wajen cika manufar Jehobah, da kuma bukatar ya zama almajirin Kristi da ya yi baftisma. Sa’ad da ya ga wani ruwa mai kyau, ya tambayi Filibus, “me za ya hana a yi mini baftisma?” Hakika, wannan yanayi ne mai muhimmanci. Wannan mutumin ya riga ya ba da gaskiya kuma ya riga yana bauta wa Allah a matsayin shigaggen Bayahude. Wataƙila sai an daɗe kafin ya sake samun wani zarafi na yin baftisma. Mafi muhimmanci ma, wannan mutumin ya fahimci abin da Allah yake bukata a gare shi, kuma yana son ya yi haka da zuciya ɗaya. Da farin ciki, Filibus ya yarda da roƙonsa, kuma bayan mutumin Habashan ya yi baftisma, “ya kama tafiyassa yana murna.” Babu shakka, ya zama mai wa’azin bishara mai ƙwazo a ƙasarsu.—Ayukan Manzanni 8:36-39.
4 Ko da yake bai kamata a ɗauki matakai na keɓe kai da kuma baftisma da wasa ko cikin hanzari ba, misalin ma’aikaci na ƙasar Habasha ya nuna cewa akwai lokatai da wasu mutane suka yi baftisma bayan wani ɗan ƙanƙanin lokaci da suka ji gaskiyar Kalmar Allah.a Don haka, yana da muhimmanci mu tattauna waɗannan tambayoyin da suke gaba: Wane irin shiri ne ya kamata a yi kafin a yi baftisma? A wane lokaci ne ya kamata a yi la’akari da shekaru? Wane irin ci gaba na ruhaniya ne ya kamata ya bayyana kafin mutum ya yi baftisma? Mafi muhimmanci, me ya sa Jehobah ya bukaci bayinsa su ɗauki wannan matakin?
Yarjejeniya ta Gaske
5, 6. (a) Ta yaya ne mutanen Allah a dā suka amsa ƙaunar Jehobah? (b) Wace dangantaka ce ta kud da kud da Allah za mu mora sa’ad da muka yi baftisma?
5 Bayan da ya ceci Isra’ilawa daga Masar, Jehobah ya yarda su zama ‘keɓaɓiyar taskarsa,’ wanda yake ƙauna, ya kāre su, kuma ya maida su “al’umma mai-tsarki.” Domin su sami waɗannan albarkatun, mutanen suna bukatar su yi na’am ga ƙaunar Allah a hanya ta musamman. Sun yi haka sa’ad da suka yarda su yi ‘dukan abin da Jehobah ya faɗi’ kuma suka kafa alkawari da shi. (Fitowa 19:4-9) A ƙarni na farko, Yesu ya umurci mabiyansa su almajirtar da mutanen dukan al’ummai, kuma su yi wa waɗanda suka yi imani da koyarwarsa baftisma. Samun dangantaka mai kyau da Allah ya dangana ne a kan ba da gaskiya ga Yesu Kristi da kuma yin baftisma.—Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 2:38, 41.
6 Waɗannan labaran na Nassi sun nuna cewa Jehobah yana wa waɗanda suka yi kuma suka manne wa alkawarin da suka yi na bauta masa albarka. Ga Kiristoci, keɓe kai da kuma baftisma matakai ne masu muhimmanci da ke kawo albarkar Jehobah. Mun ƙuduri aniyar bin hanyoyinsa da kuma neman ja-gorarsa. (Zabura 48:14) Saboda haka, a alamance Jehobah yana riƙe da hannunmu kuma yana yi mana ja-gora zuwa hanyar da yake so mu bi.—Zabura 73:23; Ishaya 30:21; 41:10, 13.
7. Me ya sa mutum ne da kansa ya kamata ya yanke shawarar keɓe kai da kuma baftisma?
7 Abubuwan da ya kamata su motsa mu mu ɗauki waɗannan matakan su ne ƙaunarmu ga Jehobah da muradinmu na bauta masa. Kada wani ya yi baftisma domin wani ya gaya masa cewa ya riga ya yi nazari na dogon lokaci ko kuwa domin abokansa suna yin baftisma. Iyaye da wasu ƙwararrun Kiristoci suna iya ƙarfafa mutum ya yi tunani game da keɓe kai da kuma baftisma. Manzo Bitrus ya ƙarfafa waɗanda suka saurare shi a Fentakos su yi “baftisma.” (Ayukan Manzanni 2:38) Duk da haka, keɓewarmu batu ne na kai, kuma babu wani da zai iya yi mana shi. Ya kamata mu da kanmu mu yanke shawarar yin nufin Allah.—Zabura 40:8.
Shiri da Kyau don Baftisma
8, 9. (a) Me ya sa Nassi bai amince da yi wa jarirai baftisma ba? (b) Waɗanne ci gaba na ruhaniya matasa za su samu kafin su yi baftisma?
8 Yara ƙanana za su iya keɓe kansu kuwa? Nassosi ba su ba da ainihin shekarar da za a kai kafin a yi baftisma ba. Duk da haka, jarirai ba sa iya zama masu bi ba, ba sa iya ba da gaskiya, ko kuwa su keɓe kansu ga Allah. (Ayukan Manzanni 8:12) Game da Kiristoci na ƙarni na farko, ɗan tarihi, Augustus Neander ya ce a cikin littafinsa General History of the Christian Religion and Church: “Manya ne kawai ake yi wa baftisma, domin sun fahimci dangantaka na kud da kud da ke tsakanin baftisma da bangaskiya.”
9 Game da matasa kuma, wasu suna fahimtar abubuwa na ruhaniya sa’ad da suke yara, wasu kuma yana ɗaukansu dogon lokaci. Kafin ya yi baftisma, ya kamata matashi ya kasance da dangantaka na kud da kud da Jehobah, ya fahimci muhimman abubuwa da ke cikin Nassosi, kuma kamar manya, ya fahimci abin da keɓe kai ya ƙunsa.
10. Waɗanne matakai ne za a ɗauka kafin a keɓe kai da kuma baftisma?
10 Yesu ya umurci almajiransa su koyar da sababbi dukan abin da ya umurce su. (Matta 28:20) Da farko, sababbi suna bukatar su sami cikakken sani na gaskiya, wanda hakan zai sa su ba da gaskiya ga Jehobah da kuma Kalmarsa. (Romawa 10:17; 1 Timothawus 2:4; Ibraniyawa 11:6) Bayan gaskiyar da ke cikin Nassi ta motsa zuciyar mutum, hakan zai motsa shi ya tuba ya kuma ƙyale hanyar rayuwarsa na dā. (Ayukan Manzanni 3:19) A ƙarshe, mutum zai kai lokacin da yake son ya keɓe kansa ga Jehobah ya kuma yi baftisma, kamar yadda Yesu ya ba da umurni.
11. Me ya sa yake da muhimmanci mu saka hannu a aikin wa’azi a kai a kai kafin mu yi baftisma?
11 Wani mataki mai muhimmanci da ke kai wa ga baftisma shi ne yin wa’azin bishara na Mulki. Wannan shi ne ainihin aikin da Jehobah ya ba mutanensa a wannan zamani na ƙarshe. (Matta 24:14) Da haka, masu shela da ba su yi baftisma ba, za su iya su more farin cikin gaya wa wasu game da imaninsu. Saka hannu a wannan aikin na shirya su su kasance masu ƙwazo kuma masu zuwa hidimar fage a kai a kai bayan sun yi baftisma.—Romawa 10:9, 10, 14, 15.
Akwai Abin da ke Hana Ka Yin Baftisma Ne?
12. Me ya sa wasu suke ƙin yin baftisma?
12 Wasu suna iya ƙin yin baftisma domin ba sa son su karɓi hakkin da ke tattare da hakan. Sun fahimci cewa idan suna son su bi mizanan Jehobah, suna bukatar su yi muhimman canji a rayuwarsu. Ko kuwa suna jin tsoro cewa zai yi musu wuya su bi abubuwan da Allah yake bukata bayan sun yi baftisma. Wasu ma suna iya tunani, “Wataƙila wata rana zan yi laifi kuma za a yi mini yankan zumunci a cikin ikilisiya.”
13. A zamanin Yesu, menene ya hana wasu su zama mabiyansa?
13 A zamanin Yesu, wasu sun ƙyale son kai da kuma gami na iyali ya hana su su zama almajiran Yesu. Wani marubuci ya gaya wa Yesu cewa zai bi shi zuwa ko’ina. Amma Yesu ya bayyana masa cewa a yawancin lokaci ba shi da inda zai kwana. Sa’ad da Yesu ya gayyaci wani mai sauraronsa ya zama mabiyinsa, wannan mutumin ya ce sai ya “bizne” ubansa tukuna. Wataƙila ya fi son ya zauna a gida ya jira har sai ubansa ya rasu maimakon ya bi Yesu, ya dawo ya cika wannan hakkin idan ubansa ya rasu. A ƙarshe, mutumi na uku ya ce sai ya “yi sallama” tukuna da iyalinsa kafin ya bi Yesu. Yesu ya kwatanta irin wannan jinkiri da “duba baya.” Hakan ya nuna cewa dukan waɗanda suke son su ɓata lokaci sukan ba da wasu dalilai da zai sa su kawar da hakkinsu na Kirista.—Luka 9:57-62.
14. (a) Menene Bitrus, Andarawus, Yakubu, da Yahaya suka yi sa’ad da Yesu ya gayyace su su zama masuntan mutane? (b) Me ya sa bai dace ba mu ɓata lokaci wajen karɓar karkiyar Yesu?
14 Misalin Bitrus, Andarawus, Yakubu, da Yahaya ya bambanta. Sa’ad da Yesu ya gayyace su su bi shi don su zama masuntan mutane, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nan da nan suka bar tarori, suka bi shi.” (Matta 4:19-22) Domin sun yanke wannan shawarar da kansu, sun shaida abin da Yesu ya gaya musu daga baya: “Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma marar-nauyi.” (Matta 11:29, 30) Ko da yake baftisma na sa mu ɗauki karkiya na hakki, Yesu ya ba mu tabbacin cewa mai sauƙi ce wadda za mu iya ɗauka kuma za ta wartsakar da mu sosai.
15. Ta yaya ne misalan Musa da Irmiya suka nuna cewa za mu iya samun taimako daga wurin Allah?
15 Jin cewa ba mu isa ba, abu ne da ke shafan kowa. Da farko, Musa da Irmiya sun ji cewa ba za su iya yin aikin da Jehobah ya ba su ba. (Fitowa 3:11; Irmiya 1:6) Ta yaya ne Allah ya ba su tabbaci? Ya gaya wa Musa, “zan kasance tare da kai.” Ya kuma yi wa Irmiya alkawari, “ina tare da kai domin in cece ka.” (Fitowa 3:12; Irmiya 1:8) Muna iya kasancewa da tabbaci cewa za mu iya samun taimako daga Allah. Ƙaunar Allah da kuma dogara a gare shi, zai iya taimaka mana mu sha kan yin shakkar ba za mu iya aikata daidai da keɓe kanmu ba. Manzo Yahaya ya rubuta: “Babu tsoro wurin ƙauna: amma cikakkiyar ƙauna tana fitarda tsoro.” (1 Yohanna 4:18) Ɗan ƙaramin yaro yana iya jin tsoro sa’ad da yake tafiya shi kaɗai, amma zai kasance da gaba gaɗi sa’ad da yake tafiya da ubansa. Hakazalika, idan muka dogara da Jehobah da dukan zuciyarmu, ya yi mana alkawarin cewa ‘za ya daidaita hanyoyinmu,’ idan muka bi shi.—Misalai 3:5, 6.
Lokaci ne Mai Daraja
16. Me ya sa baftisma ya ƙunshi nitsar da dukan jikin mutum a cikin ruwa?
16 Kafin a yi baftisma, ana ba da jawabi daga Nassi da ke bayyana muhimmancin baftismar Kirista. A ƙarshen wannan jawabin, ana umurtar waɗanda za su yi baftisma su shaida bangaskiyarsu a fili ta wajen amsa tambayoyi biyu na baftisma. (Romawa 10:10; duba akwatin da ke shafi na 23.) Bayan haka, za a nitsar da wanda zai yi baftismar a cikin ruwa, don bin misalin da Yesu ya kafa. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa bayan da Yesu ya yi baftisma, “ya fita nan da nan daga cikin ruwa.” (Matta 3:16; Markus 1:10) Hakika, Yahaya Mai Yin Baftisma ya nitsar da Yesu cikin ruwa.b Nitsar da dukan jikinmu a cikin ruwa na nuna irin canjin da muka yi a rayuwarmu, a alamance, mun mutu a tafarkin rayuwarmu ta dā, kuma a yanzu mun soma sabuwar rayuwa a hidimar Allah.
17. Ta yaya ne waɗanda za su yi baftisma da kuma ’yan kallo za su iya daraja wannan aukuwa?
17 Baftisma lokaci ne mai muhimmanci kuma na farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu yana addu’a sa’ad da Yahaya ya nitsar da shi cikin Kogin Urdun. (Luka 3:21, 22) Daidai da wannan misalin, ya kamata waɗanda za su yi baftisma a yau su nuna hali mai kyau. Tun da yake Littafi Mai Tsarki ya umurce mu mu dinga sanya tufafin da suka dace a kullum, ya kamata mu bi wannan shawarar sosai a ranar da za mu yi baftisma! (1 Timothawus 2:9) ’Yan kallo suna iya nuna daraja ta wajen sauraron jawabin baftismar su kuma lura da abubuwan da ke faruwa a hanyar da ta dace.—1 Korinthiyawa 14:40.
Albarkar da Almajiran da Suka Yi Baftisma Suke Mora
18, 19. Waɗanne gata da kuma albarkatu ne baftisma ke kawowa?
18 Sa’ad da muka keɓe kanmu ga Allah kuma muka yi baftisma, mun shiga cikin iyalinsa na musamman. Na farko, Jehobah zai zama Ubanmu da kuma Abokinmu. A dā bare muke ga Allah kafin mu yi baftisma, amma yanzu mun sulhunta da shi. (2 Korinthiyawa 5:19; Kolossiyawa 1:20) Ta wurin hadayar Kristi, mun kusanci Allah, shi ma ya kusance mu. (Yaƙub 4:8) Annabi Malakai ya kwatanta yadda Jehobah ke mai da hankali da kuma sauraron waɗanda suke amfani kuma suke ɗauke da sunansa, kuma ya rubuta sunansu a cikin littafin tunawa. “Za su zama nawa,” in ji Allah, “zan kuwa keɓe su, kamar yadda mutum ya kan keɓe ɗansa da ke bauta masa.”—Malachi 3:16-18.
19 Baftisma na sa mu shiga cikin ’yan’uwanci na dukan duniya. Sa’ad da manzo Bitrus ya tambayi Kristi albarkar da za su samu domin sadaukarwar da suka yi, Yesu ya yi musu alkawari: “Kowanene ya bar gidaje, ko ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uba, ko uwa, ko ’ya’ya, ko ƙasashe, sabili da sunana, za ya sami riɓi ɗari; za ya kuma gāji rai na har abada.” (Matta 19:29) Shekaru bayan haka, Bitrus ya rubuta game da “ ’yan’uwanci” da ya yaɗu “cikin duniya.” Bitrus da kansa ya shaida taimako da kuma albarkar ƙauna ta ’yan’uwanci, mu ma muna iya shaida hakan.—1 Bitrus 2:17; 5:9.
20. Wane bege mai albarka ne baftisma ke bayarwa?
20 Bugu da ƙari, Yesu ya bayyana cewa waɗanda suka bi shi za su sami “rai na har abada.” Hakika, keɓe kai da kuma baftisma na ba da begen “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai,” wato rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah. (1 Timothawus 6:19) Akwai tushe mai kyau na nan gaba da za mu iya samar wa kanmu da kuma iyalinmu da ya fi wannan? Wannan bege mai albarka na ba mu zarafin yin “biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”—Mikah 4:5.
[Hasiya]
a An yi wa Yahudawa da kuma shigaggu dubu uku da suka saurari jawabin Bitrus baftisma babu ɓata lokaci. Hakika, kamar Habashi bābā, su ma sun riga sun fahimci ainihin koyarwa da kuma mizanan Kalmar Allah.—Ayukan Manzanni 2:37-41.
b Kalmar nan ta Helenanci baʹpti·sma (baftisma) na nufin nitsarwa gabaki ɗaya, da kuma tasowa,” in ji Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Ta yaya ne kuma don me ya kamata mu amsa ƙaunar Jehobah?
• Wane ci gaba na ruhaniya ya kamata ya bayyana kafin baftisma?
• Me ya sa bai kamata mu ƙyale tsoron kasawa ko na ɗaukan hakki ya hana mu yin baftisma ba?
• Waɗanne albarkatu ne mabiyan Yesu Kristi da suka yi baftisma za su iya mora?
[Hoto a shafi na 27]
“Me za ya hana a yi mini baftisma?”
[Hoto a shafi na 30]
Baftisma lokaci ne mai muhimmanci da kuma farin ciki