Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 3/1 pp. 14-18
  • Tafiya A Hanya Da Ke Ƙara Haskaka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tafiya A Hanya Da Ke Ƙara Haskaka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙarin Haske ya Kai ga Yin Gyara a Ƙungiya
  • Ƙarin Haske na Nufin Ƙarin Gyara
  • Jehobah ya Haskaka Hanyar Koyarwa ta Addini
  • Ka Ci Gaba da Tafiya Cikin Hanyar da ke Ƙara Haskaka
  • Ka Ci Gaba Da Yin Tafiya Tare Da Ƙungiyar Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ɗaukakar Jehovah Ta Haskaka Mutanensa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Haske Daga Allah Na Korar Duhu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • ‘Ya Allah, Ka Aiko Da Haskenka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 3/1 pp. 14-18

Tafiya A Hanya Da Ke Ƙara Haskaka

“Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda yake haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.”—MISALAI 4:18.

1, 2. Menene mutanen Allah suka samu a sakamakon yadda Jehobah yake haskaka su a ruhaniya?

WANENE zai iya kwatanta yadda rana take shafar duhun dare fiye da Jehobah Allah wanda shi ne Tushen haske? (Zabura 36:9) ‘Sa’ad da hasken safiya ta kama iyakan duniya,’ Allah ya ce, “ta sāke kamar ɗanyar ƙasa da aka buga mata hatimi, ta fito a fili sai ka ce launin riga.” (Ayuba 38:12-14) Saboda ƙarin hasken rana, abubuwan duniya suna yin kyau, kamar yadda yumɓu yake sake kamani bayan an buga masa tambari.

2 Jehobah shi ne Tushen haske na ruhaniya. (Zabura 43:3) Sa’ad da mutanen duniya suke cikin duhu, Allah na gaskiya yana ci gaba da haskaka mutanensa. Menene sakamakon haka? Littafi Mai Tsarki ya amsa: “Amma tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir wanda yake haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” (Misalai 4:18) Ƙarin haske daga wurin Jehobah yana ci gaba da haskaka hanyoyin mutanensa da kuma gyara su wajen tsare-tsaren ƙungiya, koyarwa ta addini, da ɗabi’a.

Ƙarin Haske ya Kai ga Yin Gyara a Ƙungiya

3. Menene aka yi alkawari a Ishaya 60:17?

3 Ta wurin annabi Ishaya, Jehobah ya annabta: “Maimakon janganci zan kawo zinariya, maimakon baƙin ƙarfe kuma in kawo azurfa, maimakon itace kuma janganci, maimakon duwatsu kuma baƙin ƙarfe.” (Ishaya 60:17) Kamar yadda a kan canja munanan kaya da kaya masu kyau, hakan nan Shaidun Jehobah suna fuskantar wasu tsare-tsare da ke ci gaba a ƙungiya a cikin wannan “cikar zamani,” ko kuma “kwanaki na ƙarshe.”—Matta 24:3; 2 Timothawus 3:1.

4. Wane gyara ne aka yi a shekara ta 1919 , kuma ta yaya ya zama da amfani?

4 A farkon kwanakin ƙarshe, ikilisiyar ɗaliban Littafi Mai Tsarki, yadda ake kiran Shaidun Jehobah a dā, suna zaɓan dattawa da dikonawa ta hanyar dimokuraɗiyya. Amma, wasu dattawan ba sa son fita wa’azi. Wasu suna jinkirin yin wa’azi kuma suna hana wasu yin wa’azi. Saboda haka, a shekara ta 1919 aka ƙafa sabon ofishi a kowace ikilisiya, wato ofishin darekta na hidima. Amma, ba mutanen ikilisiyar ne suka zaɓi darektan hidiman ba, an naɗa shi ne daga ofishin reshe na mutanen Allah. Aikin darektan da aka naɗa ya haɗa da tsara yin wa’azi, ba da yankuna, da kuma ƙarfafa mutane don su fita wa’azi. A shekarun da suka biyo baya, aikin wa’azi ya ƙaru sosai.

5. Wane gyara ne ya zama da amfani a shekara ta 1920?

5 A taron guduma na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a shekara ta 1922 a Cedar Point Ohio, an ƙarfafa dukan ikilisiyar da wannan gargaɗin “Ku sanar, ku sanar, ku sanar da Sarkin da kuma mulkinsa.” A shekara ta 1927 an tsara hidimar fage har ta kai ga keɓe ranar Lahadi ta zama ranar zuwa wa’azi na gida gida. Me ya sa aka zaɓi wannan ranar? Saboda a ranar Lahadi yawancin mutane ba sa zuwa wurin aiki. A yau, Shaidun Jehobah suna ƙoƙari wurin ziyarartar mutane a lokacin da za su same su a gidajensu, a ƙarshen mako, ko kuma da yamma.

6. A shekara ta 1931, wane alkawari ne aka ɗauka, kuma ta yaya wannan ya shafi aikin shelar Mulki?

6 An yi wani babban ƙari a aikin shelar Mulkin Allah a ranar Lahadi da rana, 26 ga watan Yuli a shekara ta 1931, sa’ad da aka ɗauki alkawari a taron guduma ta farko a Columbus, Ohio, a Amirka, daga baya kuma a duniya gabaki ɗaya. Alkawarin ya ce: “Mu bayin Jehobah ne an umurce mu, mu yi aiki a cikin sunansa, kuma cikin biyayya ga dokarsa, mu gaya wa mutane game da Yesu Kristi, kuma mu gaya wa mutane cewa Jehobah shi ne Maɗaukaki kuma shi ne Allah na gaskiya; saboda haka mun rungumi kuma mun yi na’am da sunan da Allah da kansa ya ambata, muna kuma son a san mu da wannan suna a kuma kira mu da shi, wato, Shaidun Jehobah.” (Ishaya 43:10) Hakika wannan sabon sunan ya bayyana ainihin aikin da dukan mutanen da suke ɗauke da wannan sunan su ke yi! Babu shakka, Jehobah ya ba da aiki ga dukan bayinsa. Hakika yadda suka ɗauki aikin ya nuna cewa sun yarda da alkawarin!

7. Wane canji ne aka yi a shekara ta 1932, kuma me ya sa?

7 Dattawa da yawa cikin tawali’u sun ba da kansu ga yin aikin wa’azi. A wasu wurare, dattawan da aka zaɓa ba su yarda da alkawarin da aka ɗauka ba, cewa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya su yi aikin wa’azi. Amma, an kusa samun ƙarin bayyani. A shekara ta 1932, ikilisiyoyi sun sami umurni ta hanyar Hasumiyar Tsaro cewa su daina zaɓan dattawa da dikonawa. Maimakon haka, an umurce su su zaɓi kwamitin hidima waɗanda mutane ne masu ruhaniya da suke yin wa’azi. Bayan haka, an ba da aikin kula ga waɗanda suke yin hidima sosai, kuma aikin ya ci gaba.

Ƙarin Haske na Nufin Ƙarin Gyara

8. Wane gyara ne aka yi a shekara ta 1938?

8 Hasken yana “haskakawa gaba gaba.” A shekara ta 1938 an share zancen zaɓe gabaki ɗaya. Ana naɗa dukan bayi a ikilisiya ta tsarin Allah a ƙarƙashin ja-gorar “bawa mai aminci mai hikima.” (Matta 24:45-47) Kusan dukan ikilisiyoyin Shaidun Jehobah sun yarda da canjin da aka yi, kuma aikin shaida ya ci gaba da ba da ’ya’ya.

9. A shekara ta 1972, wane gyara ne aka yi, kuma me ya sa gyaran yake da amfani?

9 A ranar ɗaya ga watan Oktoba a shekara ta 1972, an yi wani gyara game da masu ja-gorar ikilisiya. An shirya rukunin dattawa da za su yi ja-gora a ikilisiyoyin Shaidun Jehobah a dukan duniya, maimakon bawa ɗaya a ikilisiya ko kuma mutum ɗaya mai yin ja-gora. Wannan sabon tsari ya ƙarfafa maza su yi ƙoƙari don su kai ga yin ja-gora a cikin ikilisiya. (1 Timothawus 3:1-7) A sakamakon haka, ’yan’uwa da yawa sun sami koyarwa a kan yadda za su kula da harkokin ikilisiya. Sun kasance da mahimmanci wajen kiwon sababbi waɗanda suka ƙarbi gaskiyar Littafi Mai Tsraki.

10. Wane tsari ne aka yi a shekara ta 1976?

10 An tsara waɗanda suke cikin Hukumar Mulki zuwa kwamiti shida, sa’an nan a ranar ɗaya ga watan Janairu shekara ta 1976, dukan aikin rukunoni da ikilisiyoyi da ke dukan duniya suka kasance a ƙarƙashin kwamitin. Kasancewar dukan aikin Mulki a ƙarƙashin ja-gorancin “taro masu-shawara” albarka ce!—Misalai 15:22; 24:6.

11. Wane gyara ne aka gabatar a shekara ta 1992, kuma me ya sa?

11 A shekara ta 1992 an yi wani gyara, wanda yake kama da abin da ya faru bayan da Isra’ilawa da wasu suka koma ƙasarsu bayan zaman bauta a ƙasar Babila. A lokacin nan babu isassun Lawiyawa da za su kula da aikin haikali. Shi ya sa aka ƙara wa Isra’ilawa masu aiki a haikali aiki sosai don su taimaka wa Lawiyawa. Saboda su taimaki bawa mai-aminci kula da aikin da yake ƙaruwa, a shekara ta 1992 an ƙara wa “waɗansu tumaki” aiki a hidima. An naɗa su don taimakon kwamitin Hukumar Mulki.—Yohanna 10:16.

12. Ta yaya Jehobah ya sa salama ta zama mai mulkinmu?

12 Menene sakamakon waɗannan? Jehobah ya ce “Zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” (Ishaya 60:17) A yau akwai “salama” tsakanin bayin Jehobah, kuma ƙaunar “adalci” ta zama ‘mahukuncinsu,’ wato, abin da yake motsa su su bauta wa Allah. A shirye suke su tafiyar da wa’azin Mulki da kuma aikin almajirantarwa.—Matta 24:14; 28:19, 20.

Jehobah ya Haskaka Hanyar Koyarwa ta Addini

13. Ta yaya ne Jehobah ya haskaka hanyar mutanensa ta wurin gyara koyarwa ta addini a shekarun 1920?

13 Jehobah yana haskaka hanyar koyarwa ta addini na mutanensa. Littafin Ru’ya ta Yohanna 12:1-9 sun ba da misali. Labarin ya ba da tarihin alamu uku na “mace” da ke da ciki, kuma ta haifi “dragon” [babban maciji] da kuma “ɗa, na miji.” Ka san wanda kowanne cikin waɗannan abubuwa ke wakilta? An bayyana a cikin talifin Hasumiyar tsaro na 1 ga watan Maris shekara ta 1925, mai suna “Birth of the Nation.” Talifin ya sa mutanen Allah sun fahimci annabce-annabce game da haifar Mulkin, suka fahimci cewa akwai ƙungiyoyi dabam dabam guda biyu, wato, ta Jehobah da ta Shaiɗan. A shekara ta 1927 da 1928, mutanen Allah sun fahimci cewa yin bikin Kirsimati da bikin ranar haihuwa ba koyarwar nassosi ba ne sai suka daina yin su.

14. Waɗanne koyarwa na gaskiya ne aka gyara a shekara ta1930?

14 A shekara ta 1930 an ƙara haske sau uku a kan koyarwa ta gaskiya. A shekaru da suka wuce, daliɓan Littafi Mai Tsraki sun fahimci cewa babban garke, ko kuma “taro mai-girma,” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9-17, sun bambanta da mutane 144,000 da za su yi sarauta da Yesu. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1-5) Amma, ba su fahimci ko su wanene ne taro mai-girma ba. Kamar yadda ƙarin haske da safe yakan sa abubuwa da ba a ganin siffarsu da kyau su fito sarai, haka ma a shekara ta 1935 an fahimci cewa mutane da ake kira taro mai-girma su ne waɗanda suka tsira daga “babban tsanani,” da suke da begen rayuwa har abada a duniya. Daga baya a wannan shekara kuma an ba da ƙarin bayani da ya shafi ’ya’yan Shaidun Jehobah masu tafiya makaranta a ƙasashe masu yawa. Ko da yake, kishin ƙasa yana da ƙarfi a duniya a lokacin, Shaidu sun fahimci cewa sara wa tuta wata irin bauta ce. A shekarar da ta biyo baya, an yi wani bayani game da koyarwa ta gaskiya cewa Yesu ya mutu a bisa gungume ne ba giciye shi aka yi ba.—Ayukan Manzanni 10:39.

15. Yaushe ne kuma ta yaya aka nanata tsarkakar jini?

15 A shekarar da ta bi bayan yaƙin duniya na II, an ƙara wa sojoji da suka ji rauni jini, amma daga baya aka sami ƙarin bayani game da tsarkakar jini. Hasumiyar tsaro ta 1 ga Yuli ta shekara ta 1945, ta ba da umurni ga “dukan masu bauta wa Jehobah da suke neman rai madawwami a cikin sabuwar duniya mai adalci, su yi biyayya ga tsarkakar jini su kuma bi tafarkin Allah na adalci game da wannan al’amari.”

16. Yaushe ne aka fito da New World Translation of the Holy Sriptures, kuma waɗanne abubuwa ne na musamman littafin ya ƙunsa?

16 A shekara ta 1946 an ga ya kamata a sami sabuwar fassarar Littafi Mai Tsraki da za ta ƙunshi ƙarin ilimi da aka samu wadda koyarwa bisa al’adun Kiristendom ba su gurɓata ta ba. Aikin fassarar ya fara ne a watan Disamba na shekara ta 1947. A shekara ta 1950 an fito da New World Translation of the Christian Greek Scriptures na Turanci. An fito da Nassosin Ibrananci na Turanci a jerin littatafai biyar, na farkon a shekara ta 1953. A shekara ta 1960 aka fito da na ƙarshen, wato, fiye da shekaru 12 ke nan tun da aka fara fassarar. A shekara ta 1961 aka fito da cikakken Littafi Mai Tsarki New World Translation of the Holy Scriptures. A yanzu ana iya samunsa a harsuna da yawa, kuma ya ƙunshi wasu abubuwa na musamman. Ya maido da hurarren sunan nan, Jehobah. Bugu da ƙari, yin amfani da ainihin kalmomin da ke cikin littafin ya buɗe hanyar ci gaba da fahimtar Kalmar Allah.

17. Wane ƙarin haske ne aka ba da a shekara ta 1962?

17 Ƙarin bayani da aka yi a kan “ikon masu-mulki” na Romawa 13:1 da yadda Kiristoci za su yi biyayya ga masu ikon mulki ya fito a shekara ta 1962. Yin nazari mai zurfi a cikin littafin Romawa sura 13 da kuma Nassosi kamar su Titus 3:1, 2 da 1 Bitrus 2:13, 17 sun nuna cewa “ikon masu mulki” yana nufin gwamnatin mutane ne ba ta Jehobah Allah da Yesu Kristi ba.

18. Waɗanne gaskiya ne aka bayyana a shekarun 1980?

18 A shekarun da suka wuce, hanyar adalci ta ci gaba da haskaka. A shekara ta 1985 an bayyana ma’anar kuɓuta ta “rai” da adalcin zama abokin Allah. (Romawa 5:18; Yaƙub 2:23) A shekara ta 1987 an bayyana ma’anar shekarar ’yanci ta Kirista.

19. Ta yaya Jehobah ya yi tanadin haske ta ruhaniya ga mutanensa a shekarun da suka wuce?

19 A shekara ta 1995 an fahimci abin da ake nufi da rarraba “tumaki” da “awaki.” A shekara ta 1998 aka bayyana wahayin haikalin da Ezekiel ya gani, wanda ya kusa cika. A shekara ta 1999 aka yi bayyani game da yadda ‘ƙyamar lalata ta tsaya a cikin tsatsarkan wuri.’ (Matta 24:15, 16; 25:32) A shekara ta 2002 aka ƙara fahimtar ma’anar bauta wa Allah “cikin ruhu da cikin gaskiya.”—Yohanna 4:24.

20. A waɗanne wurare ne kuma mutanen Jehobah suka sake yin gyara?

20 Bayan da aka yi gyara a tsarin ƙungiya da koyarwa ta addini, an yi gyara a kan halin Kirista. Alal misali, a shekara ta 1973 an fahimci cewa shan taba sigari yana “ƙazamta jiki” kuma laifi ne mai tsanani. (2 Korinthiyawa 7:1) Bayan shekaru goma, a cikin Hasumiyar Tsaro ta shekara ta1983, an ƙara bayyana matsayinmu game da amfani da bindiga. Waɗannan su ne misalai da aka ƙara masu haske a zamaninmu.

Ka Ci Gaba da Tafiya Cikin Hanyar da ke Ƙara Haskaka

21. Kasancewa da wane irin hali ne zai taimake mu mu ci gaba da bin tafarkin haske?

21 Wani dattijo da ya daɗe yana hidima ya ce: “Amince wa canji idan aka sami canji, da kuma saba wa da shi ya kan yi wuya.” Menene ya taimake shi ya amince da gyare-gyaren da ya fuskanta a shekaru 48 da ya yi yana shailar Mulki? Ya ce: “Kasancewa da hali da ya dace yana da muhimmanci. Idan mutum ya ƙi yin gyara shi za a bari a baya sa’ad da ƙungiyar ta yi gaba. Idan na sami kaina cikin yanayin da yin gyara yake da wuya, ina tuna abin da Bulus da ya gaya wa Yesu: ‘Ubangiji a wurin wa za mu tafi? Kai ne da maganar rai na har abada.’ Sai in tambayi kaina, ‘To, ina za ni, tun da ba zan shiga cikin duhun duniya ba?’ Wananna ne ya taimake ni na riƙe ƙungiyar Allah da karfi.”—Yohanna 6:68.

22. Ta yaya muka amfana daga bin tafarkin haske?

22 Babu shakka duniyar da ta kewaye mu tana cikin duhu. Yayin da Jehobah ya ci gaba da haskaka mutanensa, za a ci gaba da ganin banbanci tsakaninsu. Menene wannan haske yake yi mana? Idan aka haska rami a kan hanya da ke da duhu hasken ba zai rufe ramin ba, haka nan ma haske daga Kalmar Allah ba zai kawar da abubuwa masu sa faɗuwa ba. Amma, haske daga Kalmar Allah zai taimake mu mu guje wa waɗannan abubuwa saboda mu ci gaba da bin tafarki mai haske. Bari mu ci gaba da sauraran kalmomi annabci na Jehobah, waɗanda suke kama “da fitilla mai-haskakawa cikin wuri mai-duhu.”—2 Bitrus 1:19.

Ka Tuna?

• Wane gyara na ƙungiyar ne Jehobah ya kawo wa mutanensa?

• Wane gyara ne na koyarwa ta adini ƙarin haske ya kawo?

• Waɗanne gyare-gyare ne kai da kanka ka shaida, kuma menene ya taimake ka ka amince da su?

• Me ya sa ka ke son ka ci gaba da bin tafarkin haske?

[Hotuna a shafi na 15]

Taron shekara ta 1922 a Cedar Point, Ohio, ya karfafa Ɗaliban Littafi Mai Tsraki su yi aikin Allah

[Hoto a shafi na 17]

N. H. Knorr ya fitar da “New World Translation of the Christian Greek Scriptures” a shekara ta 1950

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 14]

© 2003 BiblePlaces.com

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba