Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 4/1 pp. 8-13
  • ‘Ya Allah, Ka Aiko Da Haskenka’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ya Allah, Ka Aiko Da Haskenka’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Hasken Yana Ci Gaba da Haskakawa
  • Hasken Yana Ƙara Haskakawa a Hankali
  • An Bayyana—Amma a Lokacin da Allah Ya So
  • Kasance a Shirye Ka Gyara Ra’ayinka
  • “Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 4/1 pp. 8-13

‘Ya Allah, Ka Aiko Da Haskenka’

“Ka aiko da haskenka da gaskiyarka; su bishe ni.”—ZABURA 43:3.

1. Ta yaya ne Jehovah yake bayyana nufe-nufensa?

JEHOVAH yana kula sosai a yadda yake sanar da nufe-nufensa wa bayinsa. Maimakon ya bayyana gaskiyar gabaɗaya farat ɗaya, a walƙawar haske a lokaci ɗaya, yana wayar da mu a hankali. Za a iya gwada tafiyar da muke yi a kan hanyar rai da wani mai doguwar tafiya cikin daji. Ya tashi da asuba ba ya gani sosai. Yayin da rana take fitowa da kaɗan da kaɗan, mutumin yake ganin abubuwan da ke gefensa. Sauran ba ya iya ganinsu sosai. Amma yayin da rana ta fito sosai, zai iya ganin abin da ke nesa. Haka yake da haske na ruhaniya da Allah yake tanadarwa. Yana sa mu gane abubuwa kalilan ne a lokaci guda. A makamancin hanyar nan Ɗan Allah, Yesu Kristi ya tanadar da wayewa ta ruhaniya. Bari mu bincika yadda Jehovah ya wayar da mutanensa a lokuttan dā da kuma yadda yake yin haka a yau.

2. Ta yaya ne Jehovah ya tanadar da wayarwa a lokuttan da ya riga Kiristanci?

2 Waɗanda suka shirya Zabura ta 43, mai yiwuwa ’ya’yan Korah ne. Da shi ke su Lawiyawa ne, suna da gatar koyar da Dokar Allah wa mutanen. (Malachi 2:7) Babu shakka, Jehovah shi ne Mai-Koyarwa Mai-Girma nasu, kuma sun dogara gareshi, shi Tushen dukan hikima. (Ishaya 30:20) Mai-zabura ya yi addu’a haka: “Ya Allah . . . ka aiko da haskenka da gaskiyarka; su bishe ni.” (Zabura 43:1, 3) Muddin Isra’ilawa suna da aminci a gareshi, Jehovah ya koya masu hanyoyinsa. Ƙarnuka bayan haka, Jehovah ya albarkace su da haske da kuma gaskiya mafi girma. Allah ya yi haka yayin da ya aiko Ɗansa zuwa duniya.

3. Ta yaya koyarwar Yesu ya gwada Yahudawa?

3 Mutumin nan Yesu Kristi, Ɗan Allah, shi ne “hasken duniya.” (Yohanna 8:12) Ya koya wa mutanen sababbin “abu dayawa da misalai.” (Markus 4:2) Ya gaya wa Bilatus Babunti: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Yohanna 18:36) Wannan sabon ra’ayi ne ga mutumin Roma da kuma Yahudawa masu wariyar ƙabila, domin suna jin cewa Almasihu zai kawar da Daular Roma kuma ya maido da Isra’ila zuwa darajarta ta dā. Yesu ya nuna haske wanda daga Jehovah ne, amma kalmominsa ba su sa masarautan Yahudawa farin ciki ba, waɗanda “suka fi son girma wurin mutane da girman Allah.” (Yohanna 12:42, 43) Yawancin mutanen sun zaɓi su manne wa al’adunsu na mutane maimakon amincewa da haske na ruhaniya da kuma gaskiya daga wurin Allah.—Zabura 43:3; Matta 13:15.

4. Ta yaya muka sani cewa almajiran Yesu za su ci gaba da ƙaruwa a fahimta?

4 Amma dai, maza da mata kalilan masu zuciyar kirki sun karɓi gaskiya da Yesu ya koyar da farin ciki. Sun ci gaba cikin fahimtarsu na nufe-nufen Allah. Amma, yayin da ƙarshen lokacin rayuwa na Malaminsu a duniya ya kusa, har ila da akwai abubuwa da yawa da ba su koya ba tukuna. Yesu ya gaya masu: “Ina da sauran zance dayawa da zan yi maku tukuna, amma ba ku iya ku ɗauke su yanzu ba.” (Yohanna 16:12) Hakika, almajiransa za su ci gaba da fahimtar gaskiyar Allah.

Hasken Yana Ci Gaba da Haskakawa

5. Wace tambaya ce ta taso a ƙarni na farko, kuma su wa suke da nawayar warware ta?

5 Bayan mutuwar Yesu da kuma tashinsa, haske daga wurin Allah ya ƙara haskakawa fiye da dā. A wani wahayi da aka ba wa Bitrus, Jehovah ya bayyana cewa nan gaba Al’ummai marasa kaciya za su iya zama mabiyan Kristi. (Ayukan Manzanni 10:9-17) Lallai wannan bayyanuwa ce! Duk da haka, daga baya tambaya ta taso: Jehovah zai bukaci waɗannan Al’ummai su yi kaciya ne bayan sun zama Kiristoci? Babu amsar wannan tambayar a cikin wahayin, kuma al’amarin ya zama na jayayya ƙwarai a tsakanin Kiristoci. Idan ba a warware shi ba, zai lalata haɗin kansu. Saboda haka, a Urushalima “manzanni da dattiɓai suka tattaru garin su duba wannan al’amari.”—Ayukan Manzanni 15:1, 2, 6.

6. Wane mataki ne manzannin da dattiɓai suka bi yayin da suke bincika zancen yin kaciya?

6 Ta yaya ne waɗanda suke wurin taron nan za su san nufin Allah game da Al’ummai masu-bi? Jehovah bai aiko da mala’ika ya ba da jagabanci a kan zancen ba, ko kuwa ya ba wa waɗanda suke wurin wahayi. Duk da haka, ba a bar manzannin da dattiɓan kawai babu wata ja-gora ba. Sun bincika wasu shaida daga wasu Kiristoci Yahudawa da sun ga yadda Allah ya fara bi da mutane na al’ummai, yana zuba ruhu mai-tsarki nasa a kan Al’ummai marasa kaciya. Sun kuma bincika Nassosi don ja-gora. A sakamakon haka, almajiri Yaƙub ya ba da shawarar da ke bisa nassi da ya wayar da su. Yayin da suka yi bimbinin tabbacin, nufin Allah ya bayyana. Al’ummai ba sa bukatar yin kaciya don su sami tagomashin Jehovah. Manzannin da dattiɓan ba su ɓata lokaci ba a rubuta shawarar don ya yi ja-gora wa sauran Kiristoci ’yan’uwa.—Ayukan Manzanni 15:12-29; 16:4.

7. A wace hanya ce Kiristoci na ƙarni na farko suka ci gaba?

7 Yawancin Kiristoci Yahudawa sun yi murna lokacin da suka gane nufin Allah game da mutanen wasu al’ummai, ba kamar shugabannen addinin Yahudawa da suka manne wa al’adun kakaninsu ba, ko da yin na’am da abin da suka gane yana bukatan canja ra’ayi game da Al’ummai gabaɗaya. Jehovah ya albarkaci ruhunsu na tawali’u, kuma “ikklisiyai fa suka ƙarfafa cikin imani, yawansu yana ƙaruwa kowace rana.”—Ayukan Manzanni 15:31; 16:5.

8. (a) Ta yaya muka sani cewa za mu iya yin tsammanin ƙarin haske bayan ƙarni na farko ya ƙare? (b) Waɗanne tambayoyi na kan lokaci ne za mu bincika?

8 Haske na ruhaniya ya ci gaba da haskakawa a duk cikin ƙarni na farko. Amma Jehovah bai bayyana kowane fasalin nufe-nufensa ga Kiristoci na farko ba. Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwa masu-bi na ƙarni na farko: “Yanzu cikin madubi mu ke gani a zaurance.” (1 Korinthiyawa 13:12) Irin madubin ba shi da haske mai kyau. Don haka, farkon gane haske na ruhaniya kaɗan ne. Bayan mutuwar manzannin, hasken ya duhunta na ɗan lokaci, amma a baya bayan nan sani na Nassi ya yalwata. (Daniel 12:4) Ta yaya ne Jehovah yake wayar da mutanensa a yau? Kuma yaya ya kamata mu mayar da martani yayin da yake faɗaɗa ganewarmu na Nassosi?

Hasken Yana Ƙara Haskakawa a Hankali

9. Wace muhimmiyar hanya mai kyau na yin nazarin Littafi Mai-Tsarki ne Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki suka yi amfani da shi?

9 A lokuttan zamani, walƙawar haske na farko ya fara bayyana ne a kusan rabin ƙarni na 19 lokacin da rukunin Kiristoci maza da mata suka fara nazarin Nassosi sosai. Suka shirya hanya mai kyau na yin nazarin Littafi Mai-Tsarki. Wani zai yi tambaya; sai kuma rukunin su bincika mahallin Nassi da ke alaƙa da shi. Sa’anda wata ayar Littafi Mai-Tsarki kamar ta saɓa da wata, waɗannan sahihan Kiristoci sukan yi ƙoƙari su daidaita biyun. Ba kamar shugabannen addinai a lokacin ba, Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki (yadda aka san Shaidun Jehovah a lokacin) a shirye suke su mai da Nassosi Masu-Tsarki, su yi masu ja-gora, ba al’adu ko kuma dokokin mutane ba. Bayan sun yi nazarin dukan tabbaci na Nassi da ake da su, sai su rubuta yadda suka kammala. Ta haka ne suka sami gane muhimman koyarwa na Littafi Mai-Tsarki da yawa.

10. Wane abubuwan nazari masu taimakawa Charles Taze Russell ya rubuta?

10 Wani musamman tsakanin Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki shi ne Charles Taze Russell. Ya rubuta jerin abubuwan yin nazarin Littafi Mai-Tsarki mai-jigo Studies in the Scriptures. Ɗan’uwa Russell ya yi niyyar ya rubuta kundi na bakwai, wanda zai yi bayani a kan littattafan Littafi Mai-Tsarki na Ezekiel da Ru’ya ta Yohanna. “Duk lokacin da na samu bayani,” in ji shi, “zan rubuta Kundi na Bakwai.” Amma, ya daɗa: “Idan Ubangiji ya ba wani bayanin, zai iya rubuta shi.”

11. Wane alaƙa ce take tsakanin lokaci da kuma gane nufe-nufen Allah?

11 Furcin nan da C. T. Russell ya yi, ya misalta wani muhimmin abu game da iyawarmu na gane wasu sashe na Littafi Mai-Tsarki—lokaci. Ɗan’uwa Russell ya sani cewa, ba zai iya tilasta ƙarin haske ya haskaka a kan Ru’ya ta Yohanna yadda wani mai doguwar tafiya ba zai tilasta wa haske ya wanzu kafin lokacinsa ba.

An Bayyana—Amma a Lokacin da Allah Ya So

12. (a) Yaushe ne ake gane annabcin Littafi Mai-Tsarki sarai? (b) Wane misali ne ya nuna cewa iyawarmu na gane annabcin Littafi Mai-Tsarki ya dangana bisa ma’ajin lokaci na Allah? (Duba hasiya.)

12 Kamar yadda manzanni suka gane annabce-annabce da yawa game da Almasihu bayan mutuwarsa da kuma tashinsa, Kiristoci a yau suna gane annabcin Littafi Mai-Tsarki filla-filla bayan sun cika ne. (Luka 24:15, 27; Ayukan Manzanni 1:15-21; 4:26, 27) Ru’ya ta Yohanna, littafin annabci ne, don haka ya kamata mu yi zaton za mu gane shi sarai yayin da aukuwan da aka kwatanta a ciki suke bayyana. Alal misali, da C. T. Russell bai gane ma’anar bisa ja wur ta alama da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 17:9-11 sarai ba, domin ƙungiyoyin da bisan take hotonsu, watau, Haɗin Kan Al’ummai da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya, ba su wanzu ba sam har sai bayan mutuwarsa.a

13. Menene yake faruwa wasu lokutta da haske ke walƙawa game da wasu zance na Littafi Mai-Tsarki?

13 Lokacin da Kiristoci na ƙarni na farko suka gano cewa Al’ummai marasa kaciya za su iya zama masu-bi, juyin nan ya tada tambaya game da ko za a bukaci mutanen al’ummai su yi kaciya. Wannan ya sa manzanni da dattiɓai su sake bincika zancen kaciyar gabaɗaya. Haka ma yake a yau. Walƙawar haske a kan zancen Littafi Mai-Tsarki wasu lokutta yana sa shafaffun bayin Allah, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” su sake bincika makamantar mahawara, kamar yadda misali na baya na yanzun nan ya nuna.—Matta 24:45.

14-16. Yaya gyara ra’ayinmu da aka yi game da haikali na ruhaniya ya taɓa ganewarmu na Ezekiel surori 40 zuwa 48?

14 An buga fassara game da annabcin Ezekiel a cikin littafin nan “The Nations Shall Know That I Am Jehovah”—How? a 1971. Wani babi cikin littafin ya tattauna wahayin Ezekiel na haikali a taƙaice. (Ezekiel, surori 40-48) A lokacin, manufar, game da yadda wahayin Ezekiel na haikalin zai cika ne a sabuwar duniya.—2 Bitrus 3:13.

15 Amma, talifofi biyu da aka buga cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Disamba, 1972, ya shafe yadda muka gane wahayin Ezekiel. Sun tattauna haikali mai girma na ruhaniya da manzo Bulus ya kwatanta a Ibraniyawa sura 10. Hasumiyar Tsaro ɗin ta bayyana cewa wuri Mai-Tsarki da kuma farfajiya ta ciki na haikali na ruhaniya yana da alaƙa da yanayin shafaffu yayin da suke duniya. Da aka sake maimaita Ezekiel surori 40 zuwa 48 wasu shekaru daga baya, an gano cewa kamar yadda haikali na ruhaniya yake aiki a yau, haka ma haikalin da Ezekiel ya gani a cikin wahayi zai zama yana aiki a yau. Ta yaya?

16 A cikin wahayin Ezekiel, ana ganin firistoci suna yawo cikin farfajiyar haikali sa’in da suke yin hidima ga ƙabilu da ba firistoci ba. Waɗannan firistoci suna wakiltan ‘tsarin firistoci ba-sarauci,’ shafaffun bayin Jehovah. (1 Bitrus 2:9) Amma, ba za su dinga hidima a cikin farfajiyar waje na haikali na duniya duk cikin Sarautar Shekara Dubu na Kristi ba. (Ru’ya ta Yohanna 20:4) A yawancin lokacin, im ma ba duka ba, shafaffun za su ci gaba da hidima ga Allah cikin Mafi-Tsarki na haikali na ruhaniya, “sama kanta.” (Ibraniyawa 9:24) Tun da shi ke ana ganin firistoci suna yawo cikin farfajiyar haikali na Ezekiel, lallai wahayin yana cika a yau, yayin da wasu cikin shafaffun suna duniya har ila. Daidai da haka, fitar wannan jaridar ta 1 ga Maris, 1999, ta nuna gyara da aka yi game da wannan zance. Da haka, tun lokacin, zuwa ƙarshen ƙarni na 20, an walƙa haske na ruhaniya a kan annabcin Ezekiel.

Kasance a Shirye Ka Gyara Ra’ayinka

17. Waɗanne gyare-gyare ne ka yi game da ra’ayinka tun da ka zo ga sanin gaskiya, kuma ta yaya wannan ya amfane ka?

17 Kowa da ke da niyyar ya zo ga sanin gaskiya tilas ne ya kasance a shirye don ya komo “da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kristi.” (2 Korinthiyawa 10:5) Ba kullum ne wannan yake da sauƙi ba, musamman ma idan ya daɗe ana da wani ra’ayi. Alal misali, kafin ka koyi gaskiyar Allah, ƙila kana jin daɗin yin wasu bukukuwa na ranakun hutu na addini da iyalinka. Bayan da ka fara nazarin Littafi Mai-Tsarki, ka gano cewa waɗannan bukukuwa da gaske asalinsa daga arna ne. Da farko, kana iya yin sanyin gwiwa a yin amfani da abin da ka ke koyo. Amma, daga baya ƙauna ga Allah ya fi so na addini ƙarfi, sai kuma ka daina yin bukukuwan da ke baƙanta wa Allah rai. Jehovah bai albarkaci shawararka ba ke nan?—Gwada da Ibraniyawa 11:25.

18. Yaya ya kamata mu yi yayin da an fassara gaskiyar Littafi Mai-Tsarki?

18 Muna amfana ko da yaushe idan muka yi abubuwa ta hanyar Allah. (Ishaya 48:17, 18) Saboda haka, yayin da aka fassara wani ra’ayi game da wani mahallin Littafi Mai-Tsarki, bari mu yi farin ciki a yaɗa gaskiyar! Hakika, cin gaba da samun haske da muke yi yana tabbatar da cewa muna kan tafarki da ke daidai. “Tafarkin mai-adilci,” wanda “yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” (Misalai 4:18) Gaskiya, a yanzu muna ganin wasu fasalolin nufe-nufen Allah a “zaurance.” Amma yayin da lokaci na Allah ya kai, za mu ga gaskiya a kyaunta gabaɗaya, muddin dai ƙafafunmu sun kafu sosai bisa “tafarkin.” A yanzu dai, bari mu ɗaukaka gaskiya da Jehovah ya fassara, mu jira fassarar waɗanda ba mu gane su sosai ba tukuna.

19. Ta wace hanya ce za mu nuna cewa muna ƙaunar gaskiya?

19 Ta yaya za mu iya nuna ƙaunarmu don haske yadda ake gani? Hanya ɗaya ita ce ta karanta Kalmar Allah a kai a kai—idan zai yiwu kowace rana. Shin kana bin wani tsari na karanta Littafi Mai-Tsarki kullum? Jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! ma suna ba mu abinci na ruhaniya da yawa mai kyau don mu more. Ka tuna da littattafai, mujallai, da kuma wasu littattafai da aka shirya don amfaninmu. Me kuma za a ce game da rahotanni na aikin wa’azin Mulki da ake bugawa cikin Yearbook of Jehovah’s Witnesses?

20. Wace alaƙa ke tsakanin haske da gaskiya daga Jehovah da kuma halartan taronmu na Kirista?

20 I, Jehovah ya amsa addu’ar da aka furta a Zabura 43:3 a hanya mai girma. A ƙarshen ayar, mu karanta: “Su [haskenka da gaskiya] kawo ni cikin tudunka mai-tsarki, wurin mazaunanka.” Kana zaton za ka bauta wa Jehovah tare da wasu da yawa? Koyarwa na ruhaniya da ake yi a taronmu muhimmiyar hanya ce da Jehovah yake tanadin wayarwa a yau. Menene za mu iya yi don mu daɗa godiyarmu ga taro na Kirista? Muna gayyatar ka ka yi la’akari da wannan zance tare da addu’a cikin talifi na gaba.

[Hasiya]

a Bayan mutuwar C. T. Russell, aka shirya wani littafi da aka ce shi ne kundi na bakwai na jerin Studies in the Scriptures da ya yi ƙoƙarin ba da fassarar littattafan Ezekiel da Ru’ya ta Yohanna. Kundin, rabinsa furcin da Russell ya yi ne a kan waɗannan littattafan Littafi Mai-Tsarki. Amma, lokacin bayyana waɗancan annabce-annabce bai kai ba tukuna, kuma a gabaɗayanta, bayani da aka bayar cikin Studies in the Scriptures ɗin a zaurance ne. Da wucewar shekaru, alherin Jehovah da kuma aukuwa na duniya sun sa Kiristoci sun fahimci ma’anar waɗannan littattafai na annabci sarai.

Za Ka Iya Amsawa?

• Me ya sa Jehovah yake bayyana nufe-nufensa a hankali?

• Ta yaya manzannin da dattiɓai a Urushalima suka warware mahawarar yin kaciya?

• Wane irin matakin nazarin Littafi Mai-Tsarki ne Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki na farko suka bi, kuma me ya sa wannan ya bambanta?

• Ka ba da misalin yadda ake bayyana haske na ruhaniya a lokacin da Allah ya so.

[Hoto a shafi na 10]

Charles Taze Russell ya sani cewa haske zai haskaka a kan littafin Ru’ya ta Yohanna a lokacin da Allah ya so

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba