Mutane Daga “Kowane Harshe” Sun Ji Bishara
“Mutum goma daga kowace al’umma da kowane harshe za su . . . ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ” —Zakariya 8:23.
1. Ta yaya ne Jehobah ya yi tanadin lokaci da kuma yanayi mafi kyau na soma wa’azi ga mutanen al’ummai da harsuna dabam dabam?
LOKACI da kuma yanayi sun dace. Ranar Fentikos ce a shekara ta 33 A.Z. Makonni kafin bikin, Yahudawa da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci daga kusan jihohi 15 na Daular Roma da kuma wajenta sun cika Urushalima maƙil, domin su yi Idin Ƙetarewa. A wannan ranar, dubban mutane sun saurara ba cikin ɗimaucewa ba kamar yadda ya kasance a Babila ta dā, amma sun fahimci abubuwan da mutane da aka cika da ruhu mai tsarki da suke shelar bishara a harsuna dabam dabam na daular suke cewa. (Ayyukan Manzanni 2:1-12) Wannan shi ne farkon ikilisiyar Kirista da kuma yin amfani da harsuna dabam dabam wajen aikin koyarwa na dukan duniya wanda ke ci gaba har wa yau.
2. Ta yaya ne almajiran Yesu suka ba wa masu sauraronsu al’ajabi a ranar Fentakos 33 A.Z.?
2 Almajiran Yesu wataƙila suna yin Helenanci, wanda shi ne ake yi a lokacin. Kuma suna Ibrananci, wanda shi ne ake yi a haikali. Amma, a ranar Fentakos sun ba mutanen da ke wajen “al’ajabi” ta wajen yin yaren mutanen. Menene sakamakon haka? Hakan ya motsa zuciyar masu sauraro domin sun ji gaskiyar a yarensu. A ƙarshen wannan ranar, ƙaramin rukunin almajiran ya ƙaru zuwa mutane fiye da 3000!—Ayyukan Manzanni 2:37-42.
3, 4. Ta yaya ne aikin wa’azi ya yaɗu sa’ad da almajiran suka bar Urushalima, Yahudiya, da kuma Galili?
3 Bayan wannan muhimmiyar aukuwar, babban tsanani ya auku a Urushalima, “waɗanda aka warwatsan nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin bishara.” (Ayyukan Manzanni 8:1-4) Alal misali, a Ayyukan Manzanni sura 8, mun karanta game da Filibus wanda mai wa’azi ne da Helenanci. Filibus ya yi wa Samariyawa wa’azi. Ya kuma yi wa wani Bahabashe mai babban matsayi wa’azi, wanda shi ma ya yi na’am da saƙon game da Kristi.—Ayyukan Manzanni 6:1-5; 8:5-13, 26-40; 21:8, 9.
4 Yayin da Kiristocin suke neman inda za su ci gaba da zama a wajen Urushalima, Yahudiya, da Galili, sun sadu da ƙabilu da kuma harsuna dabam dabam. Wataƙila, wasu a cikinsu Yahudawa ne kaɗai suka taɓa yi wa wa’azi. Amma, almajiri Luka ya ba da rahoto: “Akwai waɗansunsu, mutanen Kubrus da na Kurane, waɗanda da isowarsu Antakiya suka yi wa al’ummai magana, suna yi musu bisharar Ubangiji Yesu.”—Ayyukan Manzanni 11:19-21.
Allah Marar Sonkai Yana da Saƙo ga Kowa
5. Ta yaya ne muka ga rashin sonkai na Jehobah a batun bishara?
5 Irin waɗannan cin gaba sun jitu da hanyoyin Allah, wanda ba ya nuna sonkai. Bayan Jehobah ya taimaka wa manzo Bitrus ya daidaita tunaninsa game da mutanen al’ummai, ya yi godiya yana cewa: “Hakika na gane lalle Allah ba ya tara, amma a kowace al’umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.” (Ayyukan Manzanni 10:34, 35; Zabura 145:9) Sa’ad da manzo Bulus wanda a dā yana tsananta wa Kiristoci, ya ce Allah yana “son dukkan mutane su sami ceto,” Bulus ya tabbatar da cewa Allah ba ya nuna bambanci. (1 Timoti 2:4) Mun ga rashin sonkai na Mahalicci a yadda ya buɗe hanyar samun begen Mulki ga dukan jinsi, ƙabilu, ƙasashe, da kuma harsuna.
6, 7. Waɗanne annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki ne suka annabta cewa bishara za ta yaɗu a harsuna dabam dabam na dukan duniya?
6 Ƙarnuka da yawa da suka shige an annabta cewa wannan ci gaba na dukan duniya zai faru. In ji annabcin Daniyel, “aka kuwa danƙa masa [Yesu] mulki, da ɗaukaka, da sarauta, domin dukan jama’a, da al’ummai, da harsuna su bauta masa.” (Daniyel 7:14) Wannan jaridar da ake wallafawa a harsuna 151 kuma ake rarrabawa a dukan duniya, wanda hakan ya sa kake karatu game da Mulkin Jehobah, ya nuna cewa wannan annabcin na Littafi Mai Tsarki yana cika.
7 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa lokaci na zuwa da mutane daga harsuna dabam dabam za su ji saƙonsa mai ba da rai. Sa’ad da yake kwatanta yadda bauta ta gaskiya za ta jawo hankalin mutane masu yawa, Zakariya ya annabta: ‘A waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al’umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude [Kiristoci shafaffu, wato “Isra’ilan gaske na Allah”] su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ (Zakariya 8:23; Galatiyawa 6:16) Sa’ad da yake faɗin abin da ya gani a wahayi, manzo Yahaya ya ce: ‘Duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al’umma, da kabila, da jama’a, da harshe, suna tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon.’ (Wahayin Yahaya 7:9) Mun ga cewa waɗannan annabce-annabcen suna cika!
Kai wa ga Dukan Ire Iren Mutane
8. Wane dalili ne na zamani ya sa muke bukatar yin gyara a aikinmu na wa’azi?
8 A yau, mutane da yawa suna ƙaurace-ƙaurace. Cuɗanya tsakanin ƙasashe ta buɗe hanyar ƙaurace-ƙaurace. Ɗarurruwan mutane daga yankunan da ake yaƙi da kuma wuraren da babu tattalin arziki sun ƙaura zuwa wuraren da ake da kwanciyar hankali, don su sami abin biyan bukata. Mutanen da suka ƙaura zuwa wata ƙasa da kuma waɗanda suka yi gudun hijira sun sa a sami yankunan da ake wasu yare. Alal misali, ana fiye da yare 120 a Finland, adadin ya fi 200 a Ostareliya. A birnin San Diego da ke Amirka, ana fiye da yare 100.
9. Yaya ya kamata mu ɗauki mutanen da suke wani yare a yankinmu?
9 Mu masu hidima ta Kirista muna ɗaukan waɗannan mutanen da suke wasu yare dabam a madadin mahani ne ga hidimarmu? Ko kaɗan! Maimakon haka, muna ɗaukar wannan wata hanya ce ta faɗaɗa yankin hidimarmu, wato, ‘gonakin da sun nuna kuma sun isa girbi.’ (Yahaya 4:35) Muna ƙoƙarin kula da mutanen da suka san talaucinsu na ruhu, ko da daga wace ƙasa ko yare suka fito. (Matiyu 5:3) A sakamakon haka, a kowace shekara, mutane masu yawa daga kowace “kabila” suna zama mabiyan Kristi. (Wahayin Yahaya 14:6) Alal misali, a watan Agusta, shekara ta 2004, a Jamus ana wa’azi ne a kusan harsuna 40. Haka nan kuma a ƙasar Ostereliya wa’azin bishara ya ƙaru daga harsuna 18 shekaru goma da suka shige zuwa harsuna 30. A Girka, Shaidun Jehobah suna yi wa mutane wa’azi a harsuna dabam dabam kusan 20. Kusan kashi 80 na Shaidun Jehobah a dukan duniya suna wani yare da ba Turanci ba.
10. Menene matsayin kowane mai shela a wajen almajirtar da mutanen “dukkan al’ummai”?
10 Hakika, ana tafiyar da umurnin Yesu na ‘almajirtar da dukkan al’ummai.’ (Matiyu 28:19) Domin sun yi maraba da wannan umurnin, Shaidun Jehobah suna wa’azi a ƙasashe 235, kuma suna rarraba littattafai a harsuna fiye da 400. Ko da yake ƙungiyar Jehobah ce ke tanadin abubuwan da ake bukata don a kai ga mutane, kowane mai shelar Mulki na bukatar ya ɗauki matakin sanar da saƙon Littafi Mai Tsarki ga “kowa” a yaren da zai iya fahimta. (Yahaya 1:7) Wannan haɗin kai ya sa miliyoyin mutane daga harsuna dabam dabam su amfana daga bisharar. (Romawa 10:14, 15) Hakika, kowanenmu na saka hannu a muhimmiyar hanya!
Fuskantar Ƙalubalen
11, 12. (a) Waɗanne ƙalubale ne muke fuskanta, kuma ta yaya ne ruhu mai tsarki ke taimaka mana? (b) Me ya sa yi wa mutane wa’azi a yarensu yake da muhimmanci?
11 A yau, yawancin masu shelar Mulki suna son su koyi wani yare, amma ba su da kyauta ta mu’ujiza ta ruhun Allah don yin wani yare. (1 Korantiyawa 13:8) Koyon wani yare ba ƙaramin aiki ba ne. Waɗanda suke fiye da yare ɗaya dole ne su daidaita tunaninsu da kuma dabararsu, saboda saƙonsu na Littafi Mai Tsarki ya kasance da sha’awa ga mutanen da suke wannan yaren da suka fito daga wurare da al’adu dabam. Sababbin mutanen da suka ƙaura zuwa wata ƙasa suna yawan fargaba; saboda haka, fahimtar yadda suke tunani ba ƙaramin aiki ba ne.
12 Duk da haka, ruhu mai tsarki yana aiki a tsakanin bayin Jehobah a ƙoƙarinsu su taimaka wa mutanen da suke wani yare. (Luka 11:13) Maimakon ya sa mu yi wani yare ta hanyar mu’ujiza, ruhu mai tsarki na iya ƙarfafa muradinmu na yin magana da mutanen da ba sa jin yarenmu. (Zabura 143:10) Yin wa’azi ko kuma koyar da saƙon Littafi Mai Tsarki ga mutane a yaren da ba nasu ba na iya motsa tunaninsu. Amma, domin mu motsa zuciyar masu sauraronmu, ya fi kyau mu yi amfani da yarensu, wato, yaren da suke so kuma wanda ke motsa su.—Luka 24:32.
13, 14. (a) Menene ke motsa wasu su soma hidima da wani yare? (b) Ta yaya muke ganin ruhun sadaukar da kai?
13 Masu shelar Mulki da yawa sun soma hidima a yankunan da ake wasu yare sa’ad da suka ga yadda mutane ke maraba da gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Wasu suna samun ƙarfafa sa’ad da hidimarsu ta zama mai wuya kuma mai ban sha’awa. “Yawancin mutanen da suka zo daga Gabashin Turai suna ƙishin gaskiya,” in ji wani ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke kudancin Turai. Abin farin ciki ne a taimaka wa mutane masu zuciyar kirki!—Ishaya 55:1, 2.
14 Muna bukatar mu ƙuduri aniya kuma ba da kai domin mu shagala a wannan aikin. (Zabura 110:3) Alal misali, yawancin iyalan shaidu Japanisawa sun ƙyale gidajensu masu kyau da ke cikin birni, sun koma ƙauyuka domin su taimaka wa ’yan Sin da suka bar ƙasarsu su fahimci Littafi Mai Tsarki. A gaɓar teku ta yamma a Amirka, masu shela suna tuƙi zuwa wurare masu nisan awa ɗaya ko biyu don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen da suke yaren Filifino. A ƙasar Norway, wasu ma’aurata suna yin nazari da wata iyali da ta fito daga Afghanistan. Ma’auratan sun yi amfani da mujallar nan Menene Allah Yake Bukata a Garemu?a bugun Turanci da ta yaren Norway. Iyalin tana karanta sakin layin a yaren Farisa, yaren da ya yi kusa da nasu, wato, yaren Dari. Suna tattaunawa da Turanci da kuma yaren Norway. Irin wannan ruhun na sadaukarwa da kuma daidaituwa na kawo sakamako mai kyau sa’ad da baƙi suka karɓi gaskiya.b
15. Ta yaya ne dukanmu za mu iya saka hannu a aikin wa’azi a harsuna dabam dabam?
15 Za ka iya saka hannu a wannan aikin wa’azi na harsuna da yawa? Me ya sa ba za ka soma ba, ta wajen lura da harsuna na ƙasashen waje da ake yi a yankinka? Kuma ka dinga tafiya da warƙoƙi ko mujallu na waɗannan yaren. Ƙasidar nan, Good News for People of All Nations, da aka fito da ita a shekara ta 2004, ta taimaka sosai wajen yaɗa begen Mulki, domin saƙon da take ɗauke da ita a harsuna dabam dabam suna da sauƙi kuma suna da kyau.—Ka duba talifin nan “Bishara ga Dukan Mutane” da ke shafi na 32.
“Ku Ƙaunaci Baƙo”
16. Ta yaya ne ’yan’uwa da suke da hakki za su iya nuna rashin sonkai wajen taimaka wa mutanen da suke wani yare?
16 Ko mun koyi wani yare ko ba mu koya ba, dukanmu na iya taimakawa wajen koyar da baƙin da suke yankinmu a ruhaniya. Jehobah ya umurci mutanensa su “ƙaunaci baƙo.” (Maimaitawar Shari’a 10:18, 19) Alal misali, a wani babban birni da ke Amirka ta Arewa, ikilisiyoyi biyar suna amfani da Majami’ar Mulki ɗaya. Kamar a yawancin majami’o’i, kowace shekara ana sake lokacin taro wanda hakan zai sa taron yaren Sin ya zama Lahadi da yamma. Hakan zai sa yawancin baƙin da suke aiki a inda ake sayar da abinci ba za su iya halartar taro ba. Dattawan da suke sauran ikilisiyoyin suka yarda a yi gyara saboda lokacin taron yaren Sin ya kasance safiyar Lahadi.
17. Yaya ya kamata mu ji sa’ad da wasu suka ƙaura domin su taimaka wa rukunin wani yare?
17 Dattawa masu ƙauna suna yaba wa ’yan’uwa maza da mata da suka ƙware kuma suke son su je su taimaki rukunonin wasu yare. Ko da yake ikilisiyoyin waɗannan ƙwararrun malamai na Littafi Mai Tsarki za su yi kewarsu, amma masu kular sun ji kamar yadda dattawan Listira da na Ikoniya suka ji. Waɗannan dattawan ba su hana Timoti yin tafiya da Bulus ba, ko da yake Timoti yana da tamani a ikilisiyarsu. (Ayyukan Manzanni 16:1-4) Bugu da ƙari, waɗanda suke yin ja-gora a aikin wa’azi ba sa ƙyale tunani, al’adu, da kuma halayen baƙin da suka ƙaura daga wata ƙasa ya kashe musu gwiwa. Maimakon haka, suna rungumar bambancin kuma suna neman hanyoyin da za su gina dangantaka mai kyau saboda bishara.—1 Korantiyawa 9:22, 23.
18. Wace hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani ne ke buɗe ga kowa?
18 Kamar yadda aka annabta, ana wa’azin bishara a “kowane harshe.” Har yanzu za a iya samun ƙaruwa a yankunan wasu yare. Dubban masu shela sun bi wannan “hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani.” (1 Korantiyawa 16:9) Duk da haka, akwai ƙarin bukatu don a nome irin waɗannan yankunan, kamar yadda talifi na gaba zai nuna.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Don ƙarin misalai, ka duba “Small Sacrifices Brought Us Great Blessings,” (“Ɗan Sadaukar da Kai da Muka Yi Ya Kawo Mana Albarka Mai Girma”) da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2004, shafuffuka na 24-28 na Turanci.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Ta yaya ne za mu iya yin koyi da Jehobah wajen nuna rashin sonkai ga dukan mutane?
• Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi game da mutanen da suke wani yare a yankinmu?
• Me ya sa yake da kyau mu yi wa mutane wa’azi a yarensu?
• Ta yaya za mu iya nuna damuwa ga baƙin da suke tsakaninmu?
[Hoto a shafi na 21]
Alamar Majami’ar Mulki a harsuna biyar