Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 11/1 pp. 9-14
  • Ka Mai Da Hankali Kada Ka Zama Mai Girman kai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Mai Da Hankali Kada Ka Zama Mai Girman kai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Ya Yi Maganin Masu Girmankai
  • “Zuciyarka ta Yi Alfarma”
  • Ka Tsare Zuciyarka Daga Girmankai
  • Za Ku Ga Bambancin da Ke Tsakanin Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Za Ka Iya Yin Tsayayya da Shaidan Kuma Ka Yi Nasara!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • ‘Ku Yafa Zuciya ta Tawali’u’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 11/1 pp. 9-14

Ka Mai Da Hankali Kada Ka Zama Mai Girman kai

“Allah na gāba da masu girmankai.”—YAKUBU 4:6.

1. Ka ba da misalin alfahari da ya dace?

WANI abu ya taɓa sa ka alfahari? Yawancinmu mun taɓa jin haka. Ba laifi ba ne wani lokaci mu yi ɗan alfahari. Alal misali, sa’ad da ma’aurata Kirista suka ji rahoto daga makaranta cewa ’yarsu tana da halin kirki kuma tana aiki tuƙuru, suna farin ciki matuƙa game da wannan. Manzo Bulus da abokansa sun yi alfahari don sun taimaka wajen kafa sabuwar ikilisiya wadda ’yan’uwan cikinta suka jimre wa tsanantawa cikin aminci.—1 Tasalonikawa 1:1, 6; 2:19, 20; 2 Tasalonikawa 1:1, 4.

2. Me ya sa yin fahariya ba shi da kyau?

2 Daga waɗannan misalai na baya, mun ga cewa alfahari zai iya zama yin farin ciki domin wani abin da aka cim ma ko kuma dukiya da aka mallaka. Amma sau da yawa, alfahari na nuna ɗaga kai da bai dace ba, mutum ya ji ya fi wasu domin iyawarsa, surarsa, dukiyarsa, ko kuma matsayinsa. Sau da yawa ana nuna irin wannan fahariya ta wurin halin girmankai. Irin wannan fahariya ce ya kamata mu Kiristoci mu mai da hankali game da ita. Me ya sa? Domin mun gaji halin sonkai daga kakanmu Adamu. (Farawa 8:21) Saboda haka, zuciyarmu na iya yaudararmu da sauƙi mu yi fahariya don dalilai da ba su dace ba. Alal misali, dole ne Kiristoci su kauce wa yin fahariya don ƙasarsu, dukiyarsu, iliminsu, iyawarsu, da kuma gwada ayyukansu da na wasu. Yin fahariya game da irin waɗannan abubuwa bai dace ba kuma yana ɓata wa Jehobah rai.—Irmiya 9:23; Ayyukan Manzanni 10:34, 35; 1 Korantiyawa 4:7; Galatiyawa 5:26; 6:3, 4.

3. Menene girmankai, menene Yesu ya faɗa game da girman kai?

3 Da wani dalili kuma da ya sa za mu ƙi fahariya da ba ta dace ba. Idan muka ƙyale irin wannan fahariya a zuciyarmu, za ta iya zama fahariya na reni da ake kira girmankai. Menene girmankai? Ban da jin ya fi wasu, mai girman kai na rena mutane, waɗanda yake ko take ɗaukan cewa ta fi su. (Luka 18:9; Yahaya 7:47-49) Yesu ya haɗa “girmankai” da wasu mugun halaye da ke “fita daga mutum” kuma ya “ƙazanta shi.” (Markus 7:20-23) Kiristoci sun fahimci muhimmancin kauce wa girmankai.

4. Ta yaya yin la’akari da misalan Littafi Mai Tsarki game da girman kai zai taimake mu?

4 Za ka sami taimako ka guje wa girmankai ta wajen yin la’akari da wasu labaran masu girman kai da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Hakan zai taimake ka ka fahimci fahariya da ba ta dace ba da kake yi ko kuma da za ka soma nan gaba. Wannan zai taimake ka ka ƙi tunani da zai sa ka zama mai girmankai. Da haka, ba zai shafe ka ba sa’ad da Allah ya aikata daidai da alkawarinsa: “Zan fitar da masu girmankai da masu fankama daga cikinta, ba za ka ƙara yin alfarma ba a dutsena tsattsarka.”—Zafaniya 3:11.

Allah Ya Yi Maganin Masu Girmankai

5, 6. Ta yaya Fir’auna ya nuna girmankai, kuma menene sakamakon haka?

5 Za ka ga ra’ayin Jehobah game da girmankai a yadda ya yi maganin sarakuna masu iko kamar Fir’auna. Babu shakka, Fir’auna mai girmankai ne. Da yake ya ɗauki kansa shi ma allah ne abin bauta, ya rena bayinsa Isra’ilawa. Ka yi la’akari da yadda ya aikata da aka ce ya ƙyale Isra’ilawa su tafi domin “su yi idi” ga Jehobah cikin jeji. Fir’auna ya amsa da girmankai: “Wanene Ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar Isra’ilawa su tafi?”—Fitowa 5:1, 2.

6 Bayan da aka harbi Fir’auna da annoba shida, Jehobah ya gaya wa Musa ya tambayi sarkin Masar: “Har yanzu kana fariya a kan jama’ata, ba ka sake su ba.” (Fitowa 9:17) Sai Musa ya sanar da annoba ta bakwai, wato, ƙanƙara da ta halaka ƙasar. Nan da nan ya saki Isra’ilawa bayan annoba ta goma, amma sai Fir’auna ya canja ra’ayinsa ya bi su. Bayan haka, Bahar Maliya ta yi wa Fir’auna da rundunarsa tarko. Ka yi tunanin yadda Masarawan suka ji sa’ad da ruwan ya koma ya rufe su! Menene sakamakon girmankan Fir’auna? Sojojinsa ƙwararru suka ce: “Mu guje wa Isra’ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”—Fitowa 14:25.

7. Ta yaya sarakunan Babila suka nuna girmankai?

7 Jehobah ya kunyantar da wasu sarakuna masu girman kai. Ɗaya shi ne Sennakerib sarkin Assuriya. (Ishaya 36:1-4, 20; 37:36-38) Bayan haka, Babiloniyawa suka ci Assuriyawa, amma an kunyantar da sarakunan Babiloniyawa biyu masu girmankai. Ka tuna bikin da Sarki Belshazzar ya yi, shi da baƙinsa suka sha ruwan inabi da tasoshi da aka ɗauko daga haikalin Jehobah, suna yabon allolin Babila. Nan da nan yatsar mutum ta fito kuma ta rubuta saƙo a kan bango. Da ya bayyana masa ma’anar rubutun, annabi Daniyel ya tuna wa Belshazzar: “Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta . . . amma sa’ad da ya kumbura . . . yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. . . . Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba.” (Daniyel 5:3, 18, 20, 22) A wannan daren, sojojin Mediya da Farisa suka ci Babila kuma aka kashe Belshazzar.—Daniyel 5:30, 31.

8. Ta yaya Jehobah ya hukunta mutane dabam dabam masu girmankai?

8 Ka tuna da wasu masu girmankai da suka rena mutanen Jehobah: Goliyat gwarzo Bafilisti, Haman Firiyam Minista na Farisa, da Sarki Hirudus Agaribas, wanda ya yi sarautar lardin Yahudiya. Domin girman kansu, waɗannan maza uku sun yi mutuwar kunya a hannun Allah. (1 Sama’ila 17:42-51; Esta 3:5, 6; 7:10; Ayyukan Manzanni 12:1-3, 21-23) Yadda Jehobah ya kunyantar da waɗannan mutane masu girmankai ya nanata wannan gaskiya: “Girmankai ja-gora ne zuwa ga halaka, fariya kuwa zuwa ga fāɗuwa.” (Karin Magana 16:18) Babu shakka cewa “Allah na gāba da masu girmankai.”—Yakubu 4:6.

9. Ta yaya sarakunan Taya suka zama maciya amana?

9 Ba kamar sarakunan Masar, Assuriya, da Babila masu girmankai ba, da akwai wani lokaci da sarkin Taya ya taimaki mutanen Allah. A lokacin sarautar Dauda da Sulemanu, sarkin ya yi tanadin gwanayen masassaƙa da kuma kayan gina gidajen sarauta da haikalin Allah. (2 Sama’ila 5:11; 2 Tarihi 2:11-16) Abin baƙin ciki, daga baya ’yan Taya suka soma gāba da mutanen Jehobah. Me ya sa suka yi hakan?—Zabura 83:3-7; Yowel 3:4-6; Amos 1:9, 10.

“Zuciyarka ta Yi Alfarma”

10, 11. (a) Wa za a gwada da sarakunan Taya? (b) Menene ya canja halin ’yan Taya game da Isra’ila?

10 Jehobah ya hure annabinsa Ezekiyel ya fallasa kuma ya hukunta sarakunan Taya. Wannan saƙon da aka idar wa “Sarkin Taya” ya ƙunshi furci da ya kwatanta sarakunan Taya da kuma maci amana na asali da kyau, wato, Shaiɗan wanda “bai zauna kan gaskiya ba.” (Ezekiyel 28:12; Yahaya 8:44) A dā Shaiɗan ruhu ne mai aminci a ƙungiyar Jehobah na ’ya’yansa na samaniya. Jehobah Allah ta bakin Ezekiyel ya faɗi ainihin dalilin da ya sa sarakunan Taya da Shaiɗan suke gāba:

11 “Kana cikin Aidan, gonar Allah. An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja . . . Na keɓe ka ka zama mala’ika mai tsaro . . . Daga ranar da aka halicce ka ba ka da laifi cikin al’amuranka, sai ran da aka iske mugunta a cikinka. A wurin yawan kasuwancinka, ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi. Na hallaka ka . . . Kai mala’ikan tsaro . . . Zuciyarka ta yi alfarma saboda kyanka, ka lalatar da hikimarka ta wurin nuna darajar kanka.” (Ezekiyel 28:13-17) Hakika, girman kai ya sa sarakunan Taya suka yi wa mutanen Jehobah mugunta. Taya cibiyar kasuwanci ce kuma ta yi arziki domin an san ta da kaya masu kyau. (Ishaya 23:8, 9) Sarakunan Taya suka zama masu girman kai kuma suka soma zaluntar mutanen Allah.

12. Me ya sa Shaiɗan ya bi tafarkin cin amana, kuma me ya ci gaba da yi?

12 Hakanan ma, halittar ruhu da ya zama Shaiɗan, a dā yana da hikima da ake bukata don ya cika kowane aiki da Allah ya ba shi. Maimakon ya yi godiya, sai ya zama mai “ɗaga kai” kuma ya soma rena yadda Allah yake sarauta. (1 Timoti 3:6) Da yake ya ɗauki kansa da muhimmanci sai ya soma son Adamu da Hauwa’u su bauta masa. Wannan mugun buri ya cika kuma ya haifi zunubi. (Yakubu 1:14, 15) Shaiɗan ya rinjayi Hauwa’u ta ci ’ya’yan itace da Allah ya ce kada su ci. Sai Shaiɗan ya yi amfani da ita ya sa Adamu ya ci ’ya’yan itace da aka hana su. (Farawa 3:1-6) Da haka mutane biyu na farko suka ƙi sarautar Allah, wato, suka zama masu bauta wa Shaiɗan. Girman kansa ba shi da iyaka. Ya yi ƙoƙari ya rinjayi dukan halittu masu basira a sama da kuma duniya har da Yesu Kristi su bauta masa su ƙi ikon mallakar Jehobah.—Matiyu 4:8-10; Wahayin Yahaya 12:3, 4, 9.

13. Waɗanne ’ya’ya ne girman kai yake ba da wa?

13 Da haka ka ga cewa Shaiɗan ne ya soma girmankai; girman kai ne ya kawo zunubi, wahala, da ɓatanci na duniya a yau. Da yake shi ne “sarkin zamanin nan,” Shaiɗan ya ci gaba da ɗaukaka fahariya da girman kai da ba su dace ba. (2 Korantiyawa 4:4) Ya san cewa lokacinsa ya ƙure, saboda haka yana yaƙi da Kiristoci na gaskiya. Burinsa shi ne ya sa su juya wa Allah baya, su zama masu son kansu, masu ruba da masu girman kai. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa irin waɗannan halaye na son kai za su zama ruwan dare gama gari a wannan “zamanin ƙarshe.”—2 Timoti 3:1, 2; Wahayin Yahaya 12:12, 17.

14. Bisa wace ƙa’ida ce Jehobah yake sha’ani da halittunsa masu basira?

14 Yesu Kristi da gaba gaɗi ya fallasa mugun sakamako da girman kan Shaiɗan ya kawo. Sau uku a gaban magabtansa masu adalcin kai, Yesu ya faɗi ƙa’idar da Jehobah yake bi a sha’aninsa da ’yan adam: “Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”—Luka 14:11; 18:14; Matiyu 23:12.

Ka Tsare Zuciyarka Daga Girmankai

15, 16. Me ya sa Hajaratu ta zama mai girmankai?

15 Wataƙila ka lura cewa misalan girmankai da aka nuna a baya game da sanannun mutane ne. Wannan yana nufin cewa talakawa ba za su iya zama masu girmankai ba? A’a. Ka lura da abin da ya faru a iyalin Ibrahim. Uban iyalin ba shi da ɗa da zai zama magajinsa, kuma matarsa Saratu ta wuce shekarun haihuwa. A lokacin, al’ada ce mutum da ke cikin yanayin Ibrahim ya auri mace ta biyu don ya sami yara. Allah ya ƙyale irin wannan aure domin bai kai lokacin da zai sake kafa ƙa’idarsa ta asali game da aure ba a tsakanin masu bauta ta gaskiya.—Matiyu 19:3-9.

16 Da matarsa ta aririce shi, Ibrahim ya yarda ya haifi magaji ta Hajaratu Bamasariya, baiwar Saratu. Da yake ta zama matar Ibrahim ta biyu, Hajaratu ta yi ciki. Ya kamata ta yi godiya sosai don ta sami matsayi na ɗaukaka. Maimakon haka, ta ƙyale zuciyarta ta sa ta zama mai girmankai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine.” Irin wannan halin ya kawo jayayya a iyalin Ibrahim da ya sa Saratu ta kori Hajaratu. Amma an yi maganin matsalar. Mala’ikan Allah ya gargaɗi Hajaratu: “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.” (Farawa 16:4, 9) Hajaratu ta bi wannan gargaɗin, ta gyara halinta wurin Saratu, kuma ta zama kakar jama’a.

17, 18. Me ya sa ya kamata dukanmu mu mai da hankali game da girman kai?

17 Labarin Hajaratu ya nuna cewa sa’ad da matsayin mutum ya kyautata yana iya zama mai girmankai. Darassin shi ne Kirista da yake da halin kirki a hidimarsa ga Allah zai iya zama mai girmankai idan ya sami arziki ko kuma iko. Yana iya soma wannan halin idan mutane suka yaba masa don abin da ya cim ma, hikimarsa, ko kuma iyawarsa. Hakika, ya kamata Kirista ya kasance a faɗake don kada ya soma girmankai. Zai yi hakan musamman idan ya cim ma wani abu ko kuma ya sami ƙarin hakki.

18 Ainihin dalili na kauce wa girman kai shi ne yadda Allah yake ɗaukan wannan halin. Kalmarsa ta ce: “Girmankai da fariya ke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.” (Karin Magana 21:4) Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi Kiristoci, musamman “masu dukiyar duniyan nan” kada su zama masu “nuna alfarma” ko girmankai. (1 Timoti 6:17; Maimaitawar Shari’a 8:11-17) Ya kamata Kiristoci marasa arziki su kauce wa “kishi” kuma su tuna cewa kowa zai iya soma girman kai, mai arziki ko kuma matalauci.—Markus 7:21-23; Yakubu 4:5.

19. Ta yaya Azariya ya ɓata halin kirkinsa?

19 Girman kai da wasu mugayen halaye za su iya ɓata dangantaka mai kyau da Jehobah. Alal misali, ka yi la’akari da lokacin da Sarki Azariya ya soma sarauta da farko: “Ya yi abin da ke daidai saboda Ubangiji . . . Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji . . . Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.” (2 Tarihi 26:4, 5) Amma, Sarki Azariya ya ɓata halin kirkinsa domin “ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa halaka.” Ya soma ɗaukan kansa da muhimmanci ainun, sai ya shiga haikali don ya ƙona turare. Sa’ad da firistoci suka yi masa kashedi kada ya yi wannan aiki na girman kai, “Azariya ya yi fushi.” Saboda haka, Jehobah ya harbe shi da kuturta, sai ya mutu da rashin tagomashin Allah.—2 Tarihi 26:16-21.

20. (a) Ta yaya halin kirki na Sarki Hezekiya ya shiga haɗari? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?

20 Za ka ga bambancin wannan a misalin Sarki Hezekiya. A wani lokaci, halin kirki na wannan sarkin yana cikin haɗari saboda “girman kai.” Abin farin ciki, “Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda girmankan da ya yi” kuma ya sake samun tagomashin Allah. (2 Tarihi 32:25, 26) Ka lura cewa abin da ya kawar da girman kan Hezekiya shi ne tawali’u. Hakika, tawali’u kishiyar girman kai ne. Saboda haka, a talifi na gaba za mu yi la’akari da yadda Kirista zai koya kuma ya ci gaba da kasancewa da tawali’u.

21. Menene Kiristoci masu tawali’u za su saurara?

21 Amma, kada mu manta da dukan mummunan sakamakon girman kai. Da yake “Ubangiji na hukunta masu girmankai,” bari mu ƙuduri aniya mu ƙi fahariya da ba ta dace ba. Yayin da muke ƙoƙari mu zama Kiristoci masu tawali’u, muna iya sauraro mu tsira wa babbar rana na Allah, sa’ad da za a kawar da masu girman kai da sakamakon girman kansu daga duniya. Sa’annan “girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fariyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa’ad da wannan rana ta yi.”—Ishaya 2:17.

Darussa don Bimbini

• Ta yaya za ka kwatanta mai girman kai?

• Menene tushen girman kai?

• Menene zai iya sa mutum ya zama mai girman kai?

• Me ya sa za mu mai da hankali game da girman kai?

[Hoto a shafi na 11]

An kunyatar da Fir’auna don girman kansa

[Hoto a shafi na 12]

Hajaratu ta zama mai girman kai domin ta sami matsayi mai kyau

[Hoto a shafi na 13]

Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa kuma ya sake samun tagomashin Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba