Jehobah Yana Kāre Waɗanda Suke Begensa
“Ƙaunarka da amincinka za su kiyaye lafiyata kullum.”—ZABURA 40:11.
1. Menene Sarki Dauda ya roƙa daga wurin Jehobah, kuma ta yaya a yanzu ake biya masa wannan bukata?
SARKI DAUDA na Isra’ila ta dā ya ce: “Na yi ta jiran taimakon Ubangiji” kuma ya motsa ya ce Jehobah “ya kasa kunne gare [shi], ya ji kukan [shi].” (Zabura 40:1) Sau da yawa ya ga yadda Jehobah yake kāre waɗanda suke ƙaunarsa. Saboda haka, Dauda a kullum yana roƙon Jehobah ya kāre shi. (Zabura 40:11) Yana tsakanin mutane maza da mata masu aminci da aka yi musu alkawari za a “tashe su su rayu da rayuwa mafi kyau,” a yanzu Dauda yana cikin tunanin Jehobah kuma yana sauraron lada. (Ibraniyawa 11:32-35) Hakika rayuwarsa ta nan gaba tabbatacciya ce a hanya mafi kyau. Sunansa yana rubuce a “littafin tarihi” na Jehobah.—Malakai 3:16.
2. Ta yaya Nassosi suka taimake mu mu fahimci abin da kāriya ta Jehobah take nufi?
2 Ko da yake amintattu da aka ambata a Ibraniyawa sura 11 sun rayu kafin Yesu Kristi ya zo duniya, duk da haka sun rayu cikin jituwa da abin da Yesu ya koyar sa’ad da ya ce: “Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami.” (Yahaya 12:25) Saboda haka, kāriya ta Jehobah ba ta nufin tsaro daga wahala ko kuma tsanantawa. Yana nufin kāriya a hanya ta ruhaniya domin kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah.
3. Wane tabbaci muke da shi cewa Jehobah ya kāre Yesu Kristi, kuma menene sakamakon haka?
3 Yesu kansa ya sha tsanani kuma an wulakanta shi, kuma abokan gabansa sun yi nasara wajen yi masa kisan wulakanci mai akuba. Duk da haka, wannan bai saɓa wa alkawarin da Allah ya yi na kāre Almasihu ba. (Ishaya 42:1-6) Tashin Yesu daga matattu bayan mutuwarsa ta wulakanci ya tabbatar da cewa Jehobah ya saurari kukansa na neman taimako—kamar yadda Jehobah ya saurari na Dauda. Jehobah ya ba wa Yesu ƙarfin ya riƙe amincinsa. (Matiyu 26:39) Bayan an kāre shi Yesu ya sami rai marar mutuwa a samaniya, kuma mutane miliyoyi da suka ba da gaskiya ga fansar sun shiga hanyar samun rai madawwami.
4. Wane tabbaci ne aka bai wa Kiristoci shafaffu da kuma “waɗansu tumaki”?
4 Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana da niyar kuma zai iya kāre bayinsa a yanzu kamar yadda ya yi a zamanin Dauda da Yesu. (Yakubu 1:17) ’Yan’uwan Yesu kalilan da suka rage a duniya za su iya dogara ga alkawarin Jehobah: “Mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama, wato ku da ikon Allah ke kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.” (1 Bitrus 1:4, 5) “Waɗansu tumaki” da suke da begen rayuwa a duniya, su ma za su iya dogara ga Allah da kuma alkawarinsa ta bakin mai Zabura: “Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama’arsa duka! Ubangiji yana kiyaye masu aminci.”—Yahaya 10:16; Zabura 31:23.
An Kāre Su a Ruhaniyance
5, 6. (a) Ta yaya aka kāre mutanen Allah a zamanin yau? (b) Wace dangantaka shafaffu suke da ita da Jehobah, kuma waɗanda suke da begen rayuwa a duniya fa?
5 A zamanin yau, Jehobah ya yi tanadi domin kāre mutanensa a hanya ta ruhaniya. Ko da yake ba ya kāre su daga tsanantawa ko kuma wahaloli da kuma masifu irin na rayuwa, cikin aminci ya ba su taimako da kuma ƙarfafa da suke bukata domin ya kāre dangantakarsu ta kusa da shi. Harsashi da suka gina dangantakarsu a kai shi ne bangaskiya bisa tanadin Allah na ƙauna na fansa. Wasu cikin waɗannan Kiristoci masu aminci, ruhu mai tsarki ya shafa su su zama abokan sarautar Kristi a samaniya. An ce da su masu adalci ’ya’yan Allah na ruhaniya, kuma waɗannan kalmomin domin su ne: “Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato gafarar zunubanmu.”—Kolosiyawa 1:13, 14.
6 Wasu miliyoyin Kiristoci masu aminci an tabbatar masu cewa su ma za su amfana daga tanadin fansa na Allah. Mun karanta: “Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” (Markus 10:45) Waɗannan Kiristoci suna saurarar more “ ’yancin nan na ɗaukaka na ’ya’yan Allah.” (Romawa 8:21) Amma a yanzu, suna ƙaunar abokantakarsu da Allah kuma suna ƙoƙari su kyautata wannan dangantakar.
7. Da me Jehobah a yau yake kāre ruhaniyar mutanensa?
7 Hanya ɗaya da Jehobah yake kāre ruhaniyar mutanensa ita ce ta wajen tanadin tsarin koyarwa mai ci gaba. Wannan yana sa su fahimci gaskiya ƙwarai. Jehobah kuma yana tanadin ja-gora ta wajen Kalmarsa, da ƙungiyarsa, da kuma ruhunsa mai tsarki. A ƙarƙashin ja-gorar “amintaccen bawan nan mai hikima,” mutanen Allah suna cikin iyali ta dukan duniya. Ajin bawan suna kula da bukatu na ruhaniya kuma idan ya wajaba bukatu na zahiri na iyalin bayin Jehobah—ko daga ina suka fito kuma ko yaya matsayinsu.—Matiyu 24:45.
8. Wane tabbaci ne Jehobah yake da shi ga amintattunsa, kuma menene ya tabbatar musu?
8 Kamar yadda Jehobah bai kāre Yesu a zahiri daga farmakin abokan gabansa ba, ba ya kāre Kiristoci haka a yau. Amma wannan ba ya nufin cewa Allah bai ji daɗinmu ba. Maimakon haka, ya nuna tabbacinsa cewa za su goyi bayansa a batun ikon mallaka. (Ayuba 1:8-12; Karin Magana 27:11) Jehobah ba zai taɓa yin watsi da waɗanda suke da aminci a gare shi ba, “gama Ubangiji yana ƙaunar abin da ke daidai, ba ya rabuwa da amintattun jama’arsa, yana kiyaye su koyaushe.”—Zabura 37:28.
An Kāre Su da Ƙauna ta Alheri da Aminci
9, 10. (a) Ta yaya gaskiyar Jehobah take kāre mutanensa? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana kāre amintattunsa ta wajen ƙaunarsa ta alheri?
9 A addu’arsa da take rubuce a Zabura ta 40, Dauda ya yi roƙo a kāre shi da ƙauna ta alherin Jehobah da kuma gaskiya. Gaskiya ta Jehobah da kuma ƙaunarsa ga adalci sun bukaci cewa ya tabbatar da mizanansa. Waɗanda suka rayu bisa waɗannan mizanan sun sami kāriya daga damuwa, tsoro, da kuma matsaloli da wasu waɗanda suka yi watsi da su suke fuskanta. Alal misali, za mu iya kāre kanmu da kuma waɗanda muke ƙauna daga matsaloli da yawa masu sa baƙin ciki idan muka guji miyagun ƙwayoyi da kuma maye, lalata, da kuma salon rayuwa na nuna ƙarfi. Har ma waɗanda suka kauce daga hanyar Jehobah ta gaskiya—kamar yadda Dauda ya yi wasu lokatai—suna da tabbacin cewa Allah zai kasance “maɓoya” ga masu laifi da suka tuba. Waɗannan za su iya cewa da farin ciki: “Za ka cece ni daga wahala.” (Zabura 32:7) Wannan lalle nuna ƙauna ce ta alheri!
10 Wani misali kuma na ƙauna ta alheri na Allah shi ne cewa Allah ya yi wa bayinsa gargaɗi su ware kansu daga muguwar duniya, wadda ba da daɗewa ba za ta halaka. Mun karanta: “Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da ke cikinta. Kowa ke ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da ke duniya, kamar su sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.” Ta wajen bin wannan gargaɗi, a zahiri za mu kāre ranmu har abada, domin nassin ya ci gaba: “Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.”—1 Yahaya 2:15-17.
An Kāre Su da Tunani, Fahimi, da Kuma Hikima
11, 12. Ka yi bayanin yadda tunani, fahimi, da kuma hikima za su iya kāre mu.
11 Ga waɗanda suke son su sami yardar Allah, an hure ɗan Dauda, Sulemanu ya rubuta: “Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka.” Sai kuma ya aririta: “Ka nemi hikima . . . Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka.”—Karin Magana 2:11; 4:5, 6.
12 Muna nuna mu masu tunani ne, idan muka yi bimbini a kan abin da muka koya daga Kalmar Allah. Bimbini yana sa mu koyi fahimi sosai saboda mu kafa abubuwa da suka fi muhimmanci. Wannan yana da muhimmanci, tun da yawancinmu mun sani—wataƙila daga abin da muka fuskanta—cewa matsala tana tasowa sa’ad da mutane suka bi abubuwa da ba su da kyau ko da gangan ko kuma ba da gangan ba. Duniyar Shaiɗan tana gabatar mana da abin duniya, ƙasaita, da iko, Jehobah kuma yana nanata mizanai na ruhaniya mafi muhimmanci. Kasa ɗora mizanan ruhaniya bisa dukiya da sauransu yana iya sa iyali ta rarrabe, abota ta ɓaci, kuma makasudai na ruhaniya su narke. Sakamakon haka, sai a waye gari mutum ba shi da kome sai baƙin cikin gaskiyar kalmomin Yesu: “Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa?” (Markus 8:36) Hikima ta nuna cewa muna bukatar mu bi gargaɗin Yesu: “Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.”—Matiyu 6:33.
Haɗarin Zama Mai Sonkai
13, 14. Menene sonkai yake nufi, kuma me ya sa yin haka rashin hikima ne?
13 Halin ’yan adam ne su damu da kansu, kuma hakan daidai ne. Amma sa’ad da muradi na kai da kuma damuwa da kai suka zama muhimman abubuwa a rayuwa, sai su jawo matsala. Saboda haka, domin mu kāre dangantakarmu da shi, Jehobah ya umurce mu mu guji sonkai. Wannan furcin tana nufin “damuwa da muradi da bukatu na kai kawai.” Wannan bai kwatanta yadda mutane da yawa suke ba a yau? Hakika, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa a ‘ƙarshen’ mugun zamani na Shaiɗan, “mutane za su zama masu sonkai.”—2 Timoti 3:1, 2.
14 Kiristoci sun fahimci hikimar kiyaye umurnin Littafi Mai Tsarki kada su kula da harkar kansu kawai, amma su ƙaunaci wasu kamar yadda suke ƙaunar kansu. (Luka 10:27; Filibiyawa 2:4) Galibin mutane za su ga wannan kamar ba mai yiwuwa ba ne, duk da haka yana da muhimmanci idan muna so mu sami nasara a aurenmu, dangantaka mai kyau ta iyali, da kuma abota mai gamsarwa. Saboda haka, bawan Jehobah na gaskiya ba zai taɓa ƙyale damuwa da yake yi wa kansa ya mallaki rayuwarsa ya yi watsi da muhimman abubuwa ba. Na farko, wannan yana nufin abin da Jehobah yake so, Allah da yake bauta wa.
15, 16. (a) Sonkai zai kai ga menene, kuma wa ya nuna alamar haka? (b) Hakikanin gaskiya, menene mutum yake yi sa’ad da yake hanzarin hukunta wasu?
15 Sonkai yana iya sa mutum ya zama mai adalcin kai, wanda zai iya kai mutum ya zama mai girman kai. Littafi Mai Tsarki ya faɗi gaskiya sa’ad da ya ce: “Ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wanene da kake ganin laifin wani. Yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.” (Romawa 2:1; 14:4, 10) Malaman addini a zamanin Yesu sun tabbatar wa kansu adalcinsu har suka ga za su iya hukunta Yesu da na mabiyansa. Ta wajen haka, suka mai da kansu alƙalai. Da yake makafi ne ga nasu kurakurai suka jawo wa kansu halaka.
16 Yahuza mabiyin Yesu wanda ya ci amanarsa, ya ƙyale kansa ya zama mutum mai hukunta wasu. A wani lokaci a Betanya sa’ad da Maryamu, ’yar’uwar Li’azaru, ta shafa wa Yesu turare, Yahuza ya yi fushi. Ya furta fushinsa yana cewa: “Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba gajiyayyu kuɗin?” Amma rahoton ya ci gaba da bayani: “Ya faɗi haka fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a’a, sai dai don shi ɓarawo ne, da ya ke kuma jakar kuɗinsu na hannunsa yakan riƙa taɓa abin da ke ciki.” (Yahaya 12:1-6) Kada mu taɓa zama kamar Yahuza ko kuma malaman addini da suke hanzarin hukunta wasu, kawai domin mu la’anta su.
17. Ka kwatanta haɗari da yake tattare da kasancewa mai alfarma da kai ko kuma mai dogara da kai.
17 Abin baƙin ciki, ko da yake wasu Kiristoci na fari, ba ɓarayi ba ne kamar Yahuza, sun faɗa cikin fahariya kuma suka zama masu alfarma da kansu. Game da su Yakubu ya rubuta: “Kuna fariya ta alfarmar banza.” Sai ya daɗa cewa: “Duk irin wannan fariya kuwa mugun abu ne.” (Yakubu 4:16) Ji da kai da kuma fahariya game da abin da muka cim ma ko kuwa gatar da muke da ita a hidimar Jehobah wawanci ne. (Karin Magana 14:16) Mun tuna abin da ya faru da manzo Bitrus, a lokacin da ya yi fahariya cewa: “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau . . . Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Hakika, babu wani dalilin fariya da kanmu. Dukan wani abin da muke morewa domin ƙauna ta alheri ta Jehobah ce. Tuna haka zai hana mu zama masu alfarma da kai.—Matiyu 26:33-35, 69-75.
18. Yaya Jehobah yake ji game da fariya?
18 “Girmankai ja-gora ne zuwa ga halaka, fariya kuma zuwa ga fāɗuwa,” aka gaya mana. Me ya sa? Jehobah ya ba da amsa: “Na ƙi girmankai, da fariya.” (Karin Magana 8:13; 16:18) Babu shakka da Jehobah ya fusata da “Sarkin Assuriya saboda dukan kurarinsa da girmankansa.” (Ishaya 10:12) Jehobah ya hukunta shi. Ba da daɗewa ba dukan duniyar Shaiɗan, tare da shugabanninta masu fariya, masu ganuwa da marasa ganuwa, za a hukunta su. Kada mu nuna irin halin abonkan gaban Jehobah!
19. A wace hanya ce mutanen Allah masu alfahari ne kuma duk da haka masu tawali’u ne?
19 Kiristoci na gaskiya suna da dalilin yin alfaharin su bayin Jehobah ne. (Irmiya 9:24) Amma kuma suna da dalilin kasancewa masu tawali’u. Me ya sa? Domin “ ’yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.” (Romawa 3:23) Saboda haka domin mu kāre matsayinmu a gaban Jehobah, dole ne mu kasance da irin halin manzo Bulus, wanda ya ce “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” kuma ya daɗa cewa “ni ne kuwa babbansu.”—1 Timoti 1:15.
20. Ta yaya Jehobah yake kāre mutanensa a yanzu, kuma ta yaya zai kāre su a nan gaba?
20 Tun da mutanen Jehobah da farin ciki suke komawa baya domin su saka bukatar Allah a gaba, muna iya tabbata cewa Jehobah zai ci gaba da kāre su a ruhaniya. Za mu iya kuma tabbata cewa sa’ad da ƙunci mai tsanani ta iso, Jehobah zai kāre mutanensa a ruhaniya da kuma a zahiri. Da zarar sun shiga sabuwar duniya ta Allah, za su iya farin ciki suna cewa: “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuma cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”—Ishaya 25:9.
Ka Tuna?
• Ta yaya aka kāre Sarki Dauda da kuma Yesu Kristi?
• Ta yaya ake kāre mutanen Jehobah a yau?
• Me ya sa ya kamata mu guji ɗaukaka kanmu?
• Me ya sa za mu zama masu alfahari kuma duk da haka masu tawali’u?
[Hoto a shafi na 17]
Ta yaya Jehobah ya kāre Dauda da Yesu?
[Hotuna a shafi na 19]
A waɗanne hanyoyi ne ake kāre mutanen Allah a ruhaniya a yau?
[Hotuna a shafi na 20]
Ko da yake muna alfahari mu bayin Jehobah ne, ya kamata mu kasance da tawali’u kullayaumi