Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 6/1 pp. 11-16
  • ‘Ka Zama Mai Haƙuri’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Zama Mai Haƙuri’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mai Wulakantarwa Domin An Yaudare Shi
  • Mai Tawali’u Amma Mai Gaba Gaɗi
  • A Iyali
  • Gargaɗi ga Dukan Kiristoci
  • Wadanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Yesu Ya Zabi Shawulu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • A Hanyar Zuwa Dimaska
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 6/1 pp. 11-16

‘Ka Zama Mai Haƙuri’

“Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, . . . mai haƙuri.”—2 TIMOTI 2:24.

1. Sa’ad da muke aiki na Kirista, me ya sa muke saduwa da mutanen da suke yi mana magana cikin fushi?

ME KAKE yi sa’ad da ka haɗu da mutane marasa zuciyar kirki? A cikin kwatancinsa na zamanin ƙarshe, manzo Bulus ya faɗi cewa mutane za su zama “masu zage-zage, . . . da masu yanke, da fajirai.” (2 Timoti 3:1-5, 12) Kana iya saduwa da irin waɗannan mutanen a hidimarka ko kuwa a wasu wurare.

2. Waɗanne nassosi ne za su iya taimaka mana mu aikata cikin hikima sa’ad da mutane suka yi mana magana cikin fushi?

2 Ba dukan mutanen da ke magana cikin fushi ba ne ba sa son abu mai kyau. Yawan wahala ko kuwa taƙaici na iya sa mutane su yi magana cikin fushi ga duk wanda suka gani. (Mai Hadishi 7:7) Wasu kuma suna yin haka ne domin suna da zama kuma suna aiki a mahallin da ake yawan zage-zage. Hakan ba zai sa mu Kiristoci mu riƙa faɗin irin waɗannan kalaman ba, amma hakan na taimaka mana mu san dalilin da ya sa wasu mutane suke irin waɗannan kalaman. Me ya kamata mu yi idan aka yi mana magana cikin fushi? Karin Magana 19:11 ta ce: “Mutum mai hankali ke danne fushinsa.” Kuma Romawa 12:17, 18 sun ba mu shawara: “Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. . . . In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.”

3. Ta yaya muke wa’azi da salama?

3 Idan muna zaman lafiya, hakan zai bayyana a irin halin da muke nunawa. Hakan kuma zai bayyana a abin da muka ce da kuma abin da muka yi, a fuskarmu da kuma muryarmu. (Karin Magana 17:27) Sa’ad da ya umurci manzaninsa su je su yi wa’azi, Yesu ya gargaɗe su: “In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaikun.’ In gidan na kirki ne, salamarku tā tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tā komo muku.” (Matiyu 10:12, 13) Saƙon da muke faɗi bishara ce. Littafi Mai Tsarki ya kira ta “bisharar salama,” “bisharar alherin Allah,” da kuma “bisharan nan ta Mulki.” (Afisawa 6:15; Ayyukan Manzanni 20:24; Matiyu 24:14) Ba wai muna so mu ƙaryata imanin mutum ko kuwa ra’ayinsa ba ne, amma manufarmu ita ce, mu gaya masa bishara daga Kalmar Allah.

4. Menene za ka iya cewa sa’ad da wani ya ce maka “ba na so” kafin ma ka gaya masa dalilin ziyararka?

4 Ba tare da ya saurara ba, cikin fushi, mai gida na iya cewa, “Ba na so.” A wasu yanayi kana iya cewa, “Ina so in karanta maka wannan ɗan kalamin ne daga Littafi Mai Tsarki.” Yana iya yarda da hakan. A wasu yanayi, zai fi dacewa ka ce: “Ina so in gaya maka game da lokacin da rashin gaskiya ba zai sake kasancewa ba, kuma mutane za su koyi su ƙaunaci juna.” Idan mutumin ba ya son ka ci gaba da bayani, kana iya daɗa cewa: “Amma ina ganin kamar ba ka da lokaci a yanzu.” Idan amsar da mai gidan ya ba mu tana da ban haushi, ya kamata mu kammala cewa mutumin ba “na kirki” ba ne? Kowane irin hali ne mutumin ya nuna, ka tuna gargaɗin da Littafi Mai Tsarki ya ba da, ka “zama salihi ga kowa . . . mai haƙuri.”—2 Timoti 2:24.

Mai Wulakantarwa Domin An Yaudare Shi

5, 6. Ta yaya Shawulu ya bi da mabiyan Yesu, kuma me ya sa ya aikata haka?

5 A ƙarni na farko, akwai wani mutum da aka sani da suna Shawulu wanda sananne ne wajen yin amfani da furci na rashin da’a har da halinsa na mugunta. Littafi Mai Tsarki ya ce “yana kan tsananta kashedi gāba da masu bin Ubangiji, cewa zai kashe su.” (Ayyukan Manzanni 9:1, 2) Daga baya ya yarda cewa a dā shi ‘saɓo yake yi, yana tsanantarwa, kuma yana wulakantarwa.’ (1 Timoti 1:13) Wataƙila wasu daga cikin ’yan’uwansa sun zama Kiristoci, ya ce game da hali da ya nuna wa mabiyan Kristi: “Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.” (Ayyukan Manzanni 23:16; 26:11; Romawa 16:7, 11) Babu wani tabbaci da ya nuna cewa almajiran sun yi jayayya da Shawulu sa’ad da yake nuna irin wannan hali.

6 Me ya sa Shawulu ya yi irin wannan abin? Shekaru da yawa bayan haka, ya rubuta: “Na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.” (1 Timoti 1:13) Shi Bafarisi ne, wanda ya karanta ‘tsanantacciyar hanyan nan ta Shari’ar kakanninsa.’ (Ayyukan Manzanni 22:3) Ko da yake malamin Shawulu, Gamaliyal, ba ya nuna wariya, amma babban firist Kayafa, wanda Shawulu ke tare da shi mai zafin hali ne. Kayafa ne ya ja-goranci ƙullin da ya sa aka kashe Yesu Kristi. (Matiyu 26:3, 4, 63-66; Ayyukan Manzanni 5:34-39) Bayan haka, Kayafa ya sa aka yi wa manzannin Yesu bulala, kuma ya kwaɓe su sosai kada su ƙara magana da sunan Yesu. Kayafa ne ya shugabanci Majalisa sa’ad da aka tafi da Istifanas don a jejjefe shi. (Ayyukan Manzanni 5:27, 28, 40; 7:1-60) Shawulu na nan sa’ad da aka jejjefe shi, kuma Kayafa ya ba shi umurni ya tsananta wa mabiyan Yesu kuma ya kamo waɗanda ke Dimashƙu. (Ayyukan Manzanni 8:1; 9:1, 2) Da irin wannan tunanin, Shawulu ya ɗauka cewa yana da himma ne domin Allah, amma ba shi da bangaskiya na ƙwarai. (Ayyukan Manzanni 22:3-5) A sakamakon haka, Shawulu ya kasa fahimtar cewa Yesu ne Almasihu na gaskiya. Amma Shawulu ya komo cikin hayyacinsa sa’ad da Yesu da aka ta da daga matattu ya yi masa magana ta mu’ujiza a kan hanyar Dimashƙu.—Ayyukan Manzanni 9:3-6.

7. Me ya sami Shawulu a sakamakon saduwarsa da Yesu a hanyarsa ta zuwa Dimashƙu?

7 Ba da daɗewa ba bayan wannan, aka aiki almajiri Hananiya ya je ya yi wa Shawulu wa’azi. Da kai ne za ka je? Hananiya ya yi shakka, amma ya yi wa Shawulu magana ta hanya mai kyau. Halin Shawulu ya canja domin saduwa ta mu’ujiza da ya yi da Yesu a hanyarsa ta zuwa Dimashƙu. (Ayyukan Manzanni 9:10-22) Daga baya an san shi da manzo Bulus, Kirista mai himma mai wa’azi a ƙasashen waje.

Mai Tawali’u Amma Mai Gaba Gaɗi

8. Ta yaya ne Yesu ya nuna irin halin Ubansa ga mutanen da suka yi zunubi?

8 Yesu mai shelar Mulki ne da himma kuma mai tawali’u ne, amma ya nuna gaba gaɗi a yadda yake bi da mutane. (Matiyu 11:29) Ya nuna irin halin Ubansa da ke sama, wanda ya umurci mugaye su daina mugunta. (Ishaya 55:6, 7) Sa’ad da yake sha’ani da masu zunubi, Yesu yana lura ko akwai alamar tuba, kuma yana ƙarfafa irin waɗannan mutanen. (Luka 7:37-50; 19:2-10) Maimakon shari’anta mutane da abin da ya gani da ido kawai, Yesu ya yi koyi da alheri na Ubansa, da haƙurinsa, da kuma jimirinsa, da tunanin cewa hakan zai sa su tuba. (Romawa 2:4) Nufin Jehobah ne cewa dukan mutane su tuba kuma su sami ceto.—1 Timoti 2:3, 4.

9. Menene za mu iya koya a yadda Ishaya 42:1-4 suka cika a kan Yesu?

9 Sa’ad da yake faɗin ra’ayin Jehobah game da Yesu Kristi, marubucin Linjila Matiyu ya yi ƙaulin waɗannan kalamai na annabci: “Ga barana wanda na zaɓa! Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al’ummai hanyar gaskiya. Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba, ba kuma wanda zai ji murya tasa a titi. Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba, fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, har ya sa gaskiya ta ci nasara. Al’ummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.” (Matiyu 12:17-21; Ishaya 42:1-4) Cikin jituwa da waɗannan kalamai na annabci, Yesu bai yi gardama ba. Har ma sa’ad da yake fuskantar matsi, ya faɗi gaskiya a hanyar da ta faranta wa masu zukatan kirki zuciya.—Yahaya 7:32, 40, 45, 46.

10, 11. (a) Ko da yake Farisiyawa suna cikin masu yin hamayya da Yesu, me ya sa ya yi wa wasu a cikinsu wa’azi? (b) A yawancin lokaci, wane irin amsa ne Yesu yake bai wa ’yan hamayya, amma menene bai yi ba?

10 A lokacin hidimarsa, Yesu ya yi wa Farisiyawa masu yawa magana. Ko da yake yawancinsu sun yi ƙoƙarin su kama shi ta wajen maganarsa, Yesu bai kammala ba cewa dukansu ne ke da muradi marar kyau. Saminu, wani Bafarisiye mai sūka, wanda wataƙila yana so ya binciki Yesu sosai, ya gayyace shi cin abinci. Yesu ya amsa gayyatar kuma ya yi wa waɗanda suke wurin wa’azi. (Luka 7:36-50) A wani lokaci kuma, wani babban Bafarishe mai suna Nikodimu ya zo wajen Yesu cikin dare. Yesu bai kunyatar da shi ba domin ya bari sai da dare ya yi zai zo wurinsa. Maimakon haka, ya yi wa Nikodimu wa’azi game da ƙaunar da Allah ya nuna ta wajen aiko da Ɗansa duniya domin ya buɗe hanyar ceto ga waɗanda za su ba da gaskiya. Kuma Yesu ya bayyana muhimmancin yin biyayya ga tsarin Allah. (Yahaya 3:1-21) Daga baya, Nikodimu ya yi magana a madadin Yesu sa’ad da Farisiyawa suka ƙasƙantar da rahoto mai kyau da aka ba da game da Yesu.—Yahaya 7:46-51.

11 Yesu yana sane da munafuncin waɗanda suke ƙoƙarin su kama shi. Bai ƙyale ’yan hamayya su sa shi ya yi mahawara marar amfani ba. A lokacin da ya dace, yana ba da jawabi, yana mai da martani da iko ta yin amfani da mizanai, yana amfani da misali, ko kuwa ya yi ƙaulin nassi. (Matiyu 12:38-42; 15:1-9; 16:1-4) A wani lokaci kuma, Yesu ba ya mai da martani idan ya ga cewa yin haka ba shi da amfani.—Markus 15:2-5; Luka 22:67-70.

12. Har ma sa’ad da aka yi masa kururuwa, ta yaya ne Yesu ya taimaka wa mutane?

12 A wani lokaci kuma, mutanen da suke ƙarƙashin ikon aljanu sun yi wa Yesu kururuwa. Sa’ad da hakan ya faru, ya nuna haƙuri kuma ya yi amfani da ikon da Allah ya ba shi ya warkar da su. (Markus 1:23-28; 5:2-8, 15) Idan wasu mutane suka yi fushi kuma suka yi mana kururuwa sa’ad da muke hidima, mu ma muna bukatar mu yi haƙuri, kuma mu yi ƙoƙari mu bi da irin wannan yanayin a hanyar da ya dace kuma cikin basira.—Kolosiyawa 4:6.

A Iyali

13. Me ya sa mutane a wasu lokaci suke yi wa wani a cikin iyali da ke nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah hamayya?

13 Bukatar kasancewa da haƙuri cikin iyali na da muhimmanci ƙwarai ga mabiyan Yesu. Mutumin da gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta motsa zuciyarsa, zai so hakan ya kasance cikin iyalinsa. Amma kamar yadda Yesu ya ce, waɗanda suke cikin iyali na iya nuna hamayya. (Matiyu 10:32-37; Yahaya 15:20, 21) Akwai dalilai masu yawa game da wannan. Alal misali, sa’ad da koyarwa ta Littafi Mai Tsarki za ta taimake mu mu zama masu gaskiya, masu ladabi, kuma mu manyanta, Nassosi sun koya mana cewa a kowane yanayi, hakkinmu mafi girma zai kasance ne ga Mahaliccinmu. (Mai Hadishi 12:1, 13; Ayyukan Manzanni 5:29) Wani a cikin iyali na iya yin fushi domin yana tunanin cewa amincinmu ga Jehobah zai rage tasirinsa. Sa’ad da muke fuskantar irin wannan yanayin, yana da muhimmanci mu bi misalin Yesu na yin haƙuri!—1 Bitrus 2:21-23; 3:1, 2.

14-16. Menene ya sa wasu da a dā suke hamayya da waɗanda suke cikin iyalinsu suka canja?

14 Yawancin mutanen da suke bauta wa Jehobah a yau suna da abokanan aure ko kuwa wasu a cikin iyali da aka yi wa hamayya domin canjin da suka yi sa’ad da suka fara nazarin Littafi Mai Tsarki. Wataƙila masu hamayya sun ji munanan maganganu game da Shaidun Jehobah, kuma suna tsoron cewa hakan zai ɓata sunan iyalinsu. Menene ya motsa su su canja halinsu? A yawancin lokatai, abu mafi muhimmanci shi ne misali mai kyau. Domin mai bin yana amfani da shawarar Littafi Mai Tsarki, yana halartar taro na Kirista a kai a kai, yana saka hannu a hidima yana kuma kula da hakkin iyali, yana nuna haƙuri duk da zage-zage, hakan na rage hamayya daga iyali a wasu lokatai.—1 Bitrus 2:12.

15 Ɗan hamayya na iya ƙin saurarar kowane irin bayani daga Littafi Mai Tsarki domin ƙiyayya ko fahariya. Haka ya kasance da wani mutum a Amirka wanda ya ce yana ɗaukaka ƙasarsa sosai. Wata rana da matarsa ta tafi taron gunduma, sai ya kwashe dukan tufafinsa ya bar gida. Wani lokaci kuma ya bar gida da bindiga yana barazanar zai kashe kansa. Ya ɗora wa addininta laifin duk wani abu marar kyau da ya aikata. Amma ta ci gaba da yin amfani da shawarar Littafi Mai Tsarki. Ya zama Mashaidin Jehobah bayan shekara ashirin da matarsa ta zama Mashaidiya. A Albaniya, wata mata ta yi fushi domin ’yarta ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma ta yi baftisma. Sau sha biyu, matar na halaka Littafi Mai Tsarki na ’yarta. Wata rana, matar ta buɗe sabon Littafi Mai Tsarki da ’yarta ta bari a kan teburi. Haka nan, sai Littafin ya buɗe zuwa Matiyu 10:36, sai uwar ta ga cewa abin da aka faɗa a wurin ya shafe ta. Duk da haka, domin ta damu da lafiyar ’yarta, uwar ta raka ta zuwa jirgin ruwan da zai kai ta da wasu Shaidu zuwa taron gunduma a Italiya. Sa’ad da uwar ta ga ƙauna, murmushi da kuma dariya na farin ciki na mutanen, sai tunaninta ya fara canjawa. Ba da daɗewa ba bayan haka, ta yarda ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki. A yau tana ƙoƙarin taimaka wa wasu da suke yin hamayya.

16 Wata rana wani riƙe da wuka ya fuskanci matarsa yana tuhumarta sa’ad da za ta shiga Majami’ar Mulki. A hankali ta ce: “Ka shigo cikin Majami’ar Mulkin ka gane da kanka.” Ya shiga, kuma daga baya ya zama dattijo Kirista.

17. Idan yanayi ya yi wuya a gidan Kirista, wace shawara ta Nassi ce za ta iya taimakawa?

17 Idan kowa a cikin iyalinka Kirista ne, akwai lokacin da yanayin zai zama mai wuya, har ma ana iya magana cikin fushi domin ajizanci. Abin lura ne cewa an gargaɗi Kiristoci da ke Afisa ta dā cewa: “Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta.” (Afisawa 4:31) Babu shakka, mahallin da ya kewaye Kiristoci da ke Afisa, ajizancinsu, a wani lokaci kuma, hanyar rayuwarsu ta dā, na rinjayarsu. Menene zai taimaka musu su canja? Suna bukatar su “sabunta ra’ayin hankalin[su].” (Afisawa 4:23) Sa’ad da suka yi nazarin Kalmar Allah, suka yi bimbini a kan yadda za ta yi tasiri a rayuwarsu, suka yi tarayya da ’yan’uwa Kiristoci, kuma suka yi addu’a sosai, ’yar ruhun Allah za ta bayyana sosai a rayuwarsu. Za su koyi su zama masu ‘yi wa juna kirki, suna tausayi, suna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe musu ta wurin Almasihu.’ (Afisawa 4:32) Ko menene wasu suka yi, muna bukatar mu kasance da haƙuri, masu alheri, tausayi, da gafartawa. Hakika, “kada [mu] rama muguntar kowa da mugunta.” (Romawa 12:17, 18) Nuna ƙauna ta gaskiya wajen koyi da Allah shi ne abin da ya dace.—1 Yahaya 4:8.

Gargaɗi ga Dukan Kiristoci

18. Me ya sa shawarar da ke 2 Timoti 2:24 ta dace ga dattijo a Afisa na dā, kuma ta yaya duka Kiristoci za su amfana?

18 Gargaɗin mu “zama mai haƙuri” ta shafi dukan Kiristoci. (2 Timoti 2:24) Timoti ne aka fara gaya wa, sa’ad da yake hidima a matsayin dattijo a Afisa. Wasu a cikin ikilisiyar suna sanar da ra’ayinsu a fili kuma suna koyar da ƙarya. Domin ba su gane manufar Dokar Musa ba sosai, sun ƙi su fahimci muhimmancin bangaskiya, ƙauna, da lamiri mai kyau. Fariya ta haddasa jayayya sa’ad da suke gardama, yayin da sun ƙi su fahimci muhimman koyarwa na Kristi da kuma muhimmancin ayyuka na ibada. Domin ya magance wannan matsalar, Timoti na bukatar ɗaukaka gaskiya ta Nassi, kuma yana bukatar ya bi da ’yan’uwan a hankali. Kamar dattawa na zamani, ya san cewa tumakin ba nasa ba ne kuma ya kamata ya bi da mutane a hanyar da za ta ɗaukaka ƙauna ta Kirista da haɗin kai.—Afisawa 4:1-3; 1 Timoti 1:3-11; 5:1, 2; 6:3-5.

19. Me ya sa yake da muhimmanci dukanmu mu “nemi . . . tawali’u”?

19 Allah ya aririci mutanensa su “nemi . . . tawali’u.” (Zafaniya 2:3) Furcin Ibrananci na “tawali’u” na nufin halin da zai sa mutum ya jimre wa mugunta cikin haƙuri, ba tare da ƙyama da ramuwa ba. Bari mu roƙi taimako daga Jehobah domin mu nuna haƙuri kuma mu wakilce shi yadda ya dace, har ma a yanayi mai wuya.

Menene Ka Koya?

• Sa’ad da aka gaya maka maganganu marar daɗi, waɗanne nassosi ne za su iya taimaka maka?

• Me ya sa Shawulu ya aikata cikin gāba?

• Ta yaya ne misalin Yesu ya taimaka mana mu bi da duka ire-iren mutane yadda ya dace?

• Wane amfani za a iya samu idan muka yi magana a gida yadda ya dace?

[Hoto a shafi na 12]

Duk da suna marar kyau da Shawulu ya yi, Hananiya ya bi da shi a hanya mai kyau

[Hoto a shafi na 15]

Kirista da ke kula da hakkinsa cikin aminci, hakan zai rage hamayya ta iyali

[Hoto a shafi na 16]

Kiristoci suna ɗaukaka ƙauna da haɗin kai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba