Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 4/1 pp. 3-6
  • Yadda Za a Gane Bisan da Kuma Shaidarsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Gane Bisan da Kuma Shaidarsa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sunayen Cikin Littafi Mai Tsarki —Ba Laƙabi Ba ne Kawai
  • An Gane Bisan
  • “Lamba Ce ta Wani Mutum”
  • Me Ya Sa Aka Rubuta Shida Har Sau Uku?
  • An Bayyana Shaidar
  • Mulkin Allah Shi ne Kaɗai Begen Mutane
  • Mene Ne Lambar Nan 666 Take Wakilta?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne Dabba Mai Kawuna Bakwai da Ke Littafin Ru’ya ta Yohanna Sura 13?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Ce Zai Faru da Maƙiyan Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Jehobah Ya Bayyana Al’amura Da Lallai “Za Su Faru Ba Da Daɗewa Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 4/1 pp. 3-6

Yadda Za a Gane Bisan da Kuma Shaidarsa

KANA jin daɗin warware wani gaibi kuwa? Don a yi haka, ka nemi wasu abubuwan taimako da za su sa ka iya samun bayanin. Allah ya yi tanadin abubuwan taimako cikin hurarriyar Kalmarsa game da lamba ta 666, sunan, ko kuma shaidar bisan na Ru’ya ta Yohanna sura 13.

A cikin wannan talifin za mu bincika dalilai huɗu—muhimman abubuwan taimakon—da za su bayyana ma’anar shaidar bisan ɗin. Za mu bincika (1) yadda ake ba da sunaye a Littafi Mai Tsarki, (2) yadda za a san bisan, (3) abin da ake nufi da lamba ta 666 da yake ‘lambar mutum,’ da kuma (4) ma’anar lamba ta 6 da dalilin da ya sa aka maimaita har sau uku, watau, 600 a tara da 60 a tara da 6, ko kuma 666.—Ru’ya ta Yohanna 13:18.

Sunayen Cikin Littafi Mai Tsarki —Ba Laƙabi Ba ne Kawai

Sau da yawa sunayen Littafi Mai Tsarki suna da muhimmanci musamman idan Allah ne ya ba da sunan. Alal misali, domin Abram zai zama uban al’ummai, Allah ya canja sunansa zuwa Ibrahim, da ke nufin “Uban Jama’ar Al’ummai.” (Farawa 17:5) Allah ya gaya wa Yusufu da Maryamu su kira sunan ɗan da za su haifa, Yesu, wanda ke nufin “Jehovah ne Ceto.” (Matta 1:21, hasiya ta NW; Luka 1:31) A jituwa da ma’anar sunan nan, Jehovah ya sa cetonmu ya yiwu ta wurin hidimar Yesu da kuma mutuwarsa.—Yohanna 3:16.

A jituwa da haka, shaida da kuma suna da Allah ya bayar lamba ta 666, lallai zai kasance da ma’anar halin bisan da Allah yake ganin sarai. Yadda yake, domin a fahimci waɗannan halayen, muna bukatar mu san bisan kansa kuma koya game da ayyukansa.

An Gane Bisan

Littafin Daniel na Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarin bayani game da ma’anar bisan ɗin na alama. Sura 7 tana ɗauke da bayani na sarai na kwatancin “manyan bisashe guda huɗu”—zaki, damisa, kura, da kuma bisa mai ban tsoro mai manyan haƙoran ƙarfe. (Daniel 7:2-7) Daniel ya gaya mana cewa waɗannan bisashe suna wakiltan “sarakuna,” ko kuma mulkokin siyasa, da suka yi mulki bi da bi a manyan dauloli.—Daniel 7:17, 23.

Game da bisan na Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2 littafin nan The Interpreter’s Dictionary of the Bible ya ce “an haɗa dukan halayen bisashe huɗu na wahayin Daniel . . . Haka nan, wannan bisan na farko [na Ru’ya ta Yohanna] na wakiltan duka ikoki na siyasa da suke adawa da Allah a duniya.” Ru’ya ta Yohanna 13:7 ta tabbatar da wannan binciken, da ta faɗi game da bisan: ‘Aka ba shi kuma hukunci bisa kowacce ƙabila da al’umma da kowane harshe da iri.’a

Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da bisashe a nuna alamun sarautar ’yan Adam? Aƙalla don dalilai biyu. Na farko, domin zubar da jini da gwamnati suka yi a tarihi cikin ƙarnuka da yawa. “Yaƙi abin da aka saba yi ne cikin tarihi,” in ji ’yan tarihi Will da Ariel Durant, “kuma ba a rage yin haka ba duk da wayewar kai ko kuma tsarin dimokuraɗiyya.” Gaskiya kam, “mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya cuce shi”! (Mai-Wa’azi 8:9) Dalili na biyu kuma shi ne cewa “dragon [Shaiɗan] kuma ya ba shi ikonsa da kursiyinsa da hukunci mai-girma.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 13:2) Saboda haka, sarautar ’yan Adam ƙagen Iblis ne, shi ya sa suke nuna halinsa na bisa, kuma irin na maciji.—Yohanna 8:44; Afisawa 6:12.

Amma wannan ba ya nufin cewa kowane mutum mai sarauta cewa Shaiɗan ne ke mallakarsa kai tsaye ba. Hakika, a wani azanci gwamnatocin mutane “masu-hidiman Allah” ne, da suke kula da jam’iyyar mutane, da idan babu su sai yamutsi. Wasu shugabanne suna kāre mana ’yancin kai, har da ’yancin yin bauta ta gaskiya—abin da Shaiɗan ba ya so. (Romawa 13:3, 4; Ezra 7:11-27; Ayukan Manzanni 13:7) Duk da haka, domin tasirin Iblis, babu mutumi ko kuma ƙungiyar ’yan Adam da ta iya kawo salama mai daɗewa da kuma kwanciyar rai ga mutane ba.b—Yohanna 12:31.

“Lamba Ce ta Wani Mutum”

Abu na uku da zai taimaka a fahimci ma’anar lamba ta 666 shi ne cewa “lamba ce ta wani mutum” yadda Littafi Mai Tsarki duk da Afokirifa ya ce. Wannan furcin ba ya nufin mutum guda, domin Shaiɗan ne—yake da iko a kan bisan—ba wani mutumi ba. (Luka 4:5, 6; 1 Yohanna 5:19; Ru’ya ta Yohanna 13:2, 18) Maimako, wannan bisan da yake da ‘lamba ta wani mutum’ ko kuma shaida, yana nuna ’yan Adam ne, ba ruhu ko kuma wani aljani ba, kuma yana da wasu halayen mutane. Menene waɗannan? Ga amsar Littafi Mai Tsarki: “Da shi ke dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Romawa 3:23) Saboda haka, bisan da yake da ‘lamba ta wani mutum’ yana nuna cewa gwamnatoci suna cikin yanayi na kasawa na ’yan Adam, halin zunubi da ajizanci.

Tarihi ya tabbatar da wannan gaskiya. “Kowane wayewar kai da aka taɓa samu ya kai ƙarshensa,” in ji wani Sakataren Ƙasa na Amirka, Henry Kissinger. “Tarihi ya zama labarin ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ba a iya cika su ba, fata da ba a samu ba . . . Saboda haka, ni ɗan tarihi dole na yarda da cewa ba za a iya kawar da bala’i ba.” Abin da Kissinger ya faɗi ya tabbatar da wannan gaskiyar Littafi Mai Tsarki: “Hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”—Irmiya 10:23.

Yanzu bayan mun san bisan kuma mun fahimci yadda Allah yake ɗaukansa, za mu iya bincika gaibi na ƙarshe—lambar nan shida da kuma abin da ya sa aka rubuta ta sau uku—watau, 666 ko kuma a tara da 600 a tara da 60 a tara da 6.

Me Ya Sa Aka Rubuta Shida Har Sau Uku?

A cikin Nassosi, wasu lambobi suna da ma’ana ta alama. Alal misali, lambar nan bakwai, ana yawan amfani da shi a nuna abin da yake cikakke, ko kuma kamiltacce a wurin Allah. Alal misali, makon halitta na Allah ya ci ‘kwanaki’ bakwai, ko kuma dogon lokaci, a lokacin Allah ya cika ƙudurinsa game da halittan duniya. (Farawa 1:3–2:3) “Kalmomin” Allah kama suke da azurfa da aka “tsarkake har so bakwai,” ta haka an yi shi sosai. (Zabura 12:6; Misalai 30:5, 6) An gaya wa kuturu Na’aman ya je ya yi wanka sau bakwai a Kogin Urdun kuma ya warke sarai.—2 Sarakuna 5:10, 14.

Shida sauran ɗaya ya cika bakwai. Bai dace a kwatanta ajizanci, ko kuma aibi a gaban Allah da wannan ba? Hakika! (1 Labarbaru 20:6, 7) Ban da haka, rubuta shida sau uku, watau 666, yana nanata ajizancin ne ƙwarai. Kamar yadda muka tattauna lambar nan 666 da take “ta wani mutum” ta tabbatar cewa wannan daidai ne. Saboda haka, tarihi na bisan, cewa “lamba ce ta wani mutum” tana nuna cewa lambar 666 ta kammala daidai—rashin cika da kuma kasawa a wurin Jehovah.

Nuna kasawar bisan ya tunasar mana da abin da aka ce game da Sarki Belshazzar na Babila na dā. Ta bakin Daniel Jehovah ya gaya wa masaraucin nan: “An auna ka cikin mizani, an iske ka ka gaza.” A daren ne aka kashe Belshazzar, kuma aka ci Daular Babila mai girma da yaƙi. (Daniel 5:27, 30) Haka nan ma hukuncin Allah zai kawo ƙarshen bisan na siyasa da waɗanda suke da shaidarsa. Amma a wannan azanci, ba kawai Allah za ya kawar da tsarin siyasa ba amma kowanne fannin sarautar ’yan Adam. (Daniel 2:44; Ru’ya ta Yohanna 19:19, 20) Saboda haka, yana da muhimmanci mu guje wa samun wani mugun shaidar bisan nan!

An Bayyana Shaidar

Nan da nan bayan an bayyana lamba ta 666, Ru’ya ta Yohanna ta ambata mabiya 144,000 na Ɗan ragon, Yesu Kristi, da suke da sunansa da sunan Ubansa, Jehovah a goshinsu. Waɗannan sunaye suna nuna cewa masu ɗauke da shi na Jehovah ne da Ɗansa da suke shelarsa da fahariya. Haka ma, waɗanda suke da shaidar bisan nan suna shela a fili suna hidima ga bisan. Saboda haka, shaidar ko a hannun dama ne ko a goshi ta alama, yana nuna wanda yake ɗauke da shi cewa yana bauta wa tsarin siyasa mai kama da bisan na duniya. Waɗanda suke ɗauke da shaidar suna ba wa “Kaisar” abin da ke na Allah. (Luka 20:25; Ru’ya ta Yohanna 13:4, 8; 14:1) Ta yaya suke haka? Suna bauta wa ƙasa ta siyasa, alamunsu, da kuma ikonsu, da suke danƙa begensu na samun ceto. Duk wata bauta da suke wa Allah na gaskiya a leɓa ce kawai.

Akasarin haka, Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Kada ku dogara ga sarakuna, ko kuwa ɗan adam, wanda babu taimako gareshi. Numfashinsa ya kan fita, ya kan koma turɓayarsa kuma; a cikin wannan rana shawarwarinsa su kan lalace.” (Zabura 146:3, 4) Waɗanda suke bin wannan gargaɗin hikima ba sa damuwa sa’ad da gwamnati ta kasa cika alkawarinsu ko kuma sa’ad da manyan shugabanne suka kasa.—Misalai 1:33.

Wannan ba ya nufin cewa Kiristoci na gaskiya sun zauna ba sa damuwa game da wahalar mutane ba. Akasarin haka, suna shelar gwamnati da zai magance matsalolin mutane—Mulkin Allah, da suke wakiltansa.—Matta 24:14.

Mulkin Allah Shi ne Kaɗai Begen Mutane

Lokacin da yake duniya, Yesu ya mai da Mulkin Allah ya zama jigon wa’azinsa. (Luka 4:43) A cikin addu’arsa, da a wasu lokatai ana kira Addu’a ta Uba, Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a don Mulkin ya zo kuma a yi nufin Allah a nan duniya. (Matta 6:9, 10) Mulkin, wata gwamnati ce da za ta yi sarautar dukan duniya, ba daga wasu jihohin duniya kawai ba, amma daga sama. Shi ya sa, Yesu ya kira shi “Mulkin sama.”—Matta 11:12.

Wa ya fi dacewa ya zama Sarkin Mulkin idan ba Yesu Kristi, wanda ya mutu domin talakawansa na nan gaba ba? (Ishaya 9:6, 7; Yohanna 3:16) Ba da daɗewa ba wannan kamiltaccen Masarauci, da yanzu babban ruhu ne, zai jefar da bisan, sarakunanta, da rundunarta cikin “ƙorama ta wuta mai-ci da ƙibiritu,” alamar halaka ta sarai. Amma ba ƙarshen ba ke nan. Yesu zai kuma kawar da Shaiɗan, abin da babu wani ɗan Adam da zai iya yi.—Ru’ya ta Yohanna 11:15; 19:16, 19-21; 20:2, 10.

Mulkin Allah zai kawo salama ga dukan talakawansa masu biyayya. (Zabura 37:11, 29; 46:8, 9) Har baƙin ciki, azaba, da mutuwa za su ƙare. Lallai zato ne mai girma ga waɗanda suka kasance babu shaidar bisan!—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

[Hasiya]

a Don tattauna waɗannan ayoyi, duba sura 28 na littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand!, da Shaidun Jehovah suka buga.

b Ko da yake mun sani cewa sarautar mutane sau da yawa tana kama da dabba, Kiristoci na gaskiya suna biyayya ga “ikon masu-mulki” na gwamnati yadda Littafi Mai Tsarki ya ce. (Romawa 13:1) Amma idan ikokin suka dokace su su yi abin da ya saɓa da dokar Allah, sukan “fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29.

[Akwati a shafi na 4]

Taimako don Sanin Ma’anar Lamba ta 666

1. Sau da yawa sunayen Littafi Mai Tsarki suna bayyana wani hali game da mai sunan ko kuma rayuwarsa, kamar Ibrahim, Yesu, da kuma wasu da yawa. Haka ma lambar sunan bisan ke wakiltar halinsa.

2. A cikin littafin Daniel na Littafi Mai Tsarki, bisashe da yawa suna wakiltar mulkokin mutane, ko kuma daula. Bisan na Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2 da ke haɗaɗɗe suna wakiltan dukan tsarin siyasa na duniya, da Shaiɗan yake ba su iko kuma yake mallakarsu.

3. Bisan da ke da “suna na mutum,” ko kuma “lamba ce ta wani mutum,” ya nuna cewa mutum ne, ba aljani ba. Shi ya sa, yake nuna kasawar mutum da ya kawo sakamakon zunubi da ajizanci.

4. A wurin Allah, lambar nan shida, da bai cika ba a azanci na Littafi Mai Tsarki, ko kuma bai kai bakwai ba, yana nufin ajizanci. Wannan lamba ta 666 yana nanata kasawar har sau uku.

[Hotuna a shafi na 5]

Sarautar ’yan Adam ta kasa, kuma lamba ta 666 ta wakilce ta daidai

[Inda aka Dauko]

Yaro mayunwaci: MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA/F. GRIFFING ne ya ɗauka hoton

[Hotuna a shafi na 6]

Yesu Kristi zai kawo kamiltacciyar sarauta ga duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba