Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 3/1 pp. 5-7
  • Kiristanci na Gaskiya Na Ci Gaba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kiristanci na Gaskiya Na Ci Gaba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tushen Haɗin Kai na Kirista
  • Abin da Ya Sa Coci ba Su da Haɗin Kai
  • Har Ila Kiristoci na Gaskiya Suna da Haɗin Kai
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Kasance da Tabbaci Cewa Ka Sami Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ina Yadda Zaka Sami Addini na Gaskiya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 3/1 pp. 5-7

Kiristanci na Gaskiya Na Ci Gaba

HIDIMAR Yesu Kristi ta shafi duniya sosai a ƙarni na farko. Saƙonsa ya ƙarfafa, ya wayar da mutane, ya kuma motsa su a hanya ta ban mamaki. Kalmominsa ya shafi mutane da yawa da suka saurare shi.—Matta 7:28, 29.

Yesu da gaba gaɗi ya ƙi sa hannu a wani tsarin addini na zalunci da na siyasa na zamaninsa, talakawa suna iya zuwa wajensa. (Matta 11:25-30) Ya yarda cewa miyagun ruhohi suna da rinjaya a duniya kuma ya nuna ikon da Allah ya ba shi a kansu. (Matta 4:2-11, 24; Yohanna 14:30) Yesu ya nuna alaƙa da ke tsakanin shan wahala da kuma zunubi, ya kuma nuna cikin ƙauna cewa Mulkin Allah ne zai kawo sauƙi na dindindin. (Markus 2:1-12; Luka 11:2, 17-23) Bayan haka, ya kawar da lulluɓi na duhu da ya rufe mutuntakar Ubansa da daɗewa, ya bayyana sunan Allah ga dukan waɗanda suke son su kasance da dangantaka da Shi.—Yohanna 17:6, 26.

Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa duk da hamayya ta addini da na siyasa mai tsanani, almajiran Yesu sun yaɗa saƙonsa da sauri. A cikin misalin shekaru 30 kawai, an kafa ikilisiyoyin Kirista masu ci gaba a Afirka, Asiya, da Turai. (Kolossiyawa 1:23) Gaskiya da Yesu ya koyar ya wayar da zukatan mutane masu tawali’u da masu zuciyar kirki a dukan Daular Roma.—Afisawa 1:17, 18

Ta yaya dukan waɗannan sababbin almajirai daga yanayi dabam dabam na tattalin arziki, al’adu, yare da kuma addini suka kasance da haɗin kai cikin “imani ɗaya” yadda manzo Bulus ya faɗa? (Afisawa 4:5) Menene zai sa su ci gaba da “magana ɗaya” domin kada su bijire? (1 Korinthiyawa 1:10) Domin rashin haɗin kai tsakanin waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne a yau, ya kamata mu bincika abin da Yesu kansa ya koyar.

Tushen Haɗin Kai na Kirista

Da ake tuhumarsa a gaban Bilatus Babunti, Yesu ya faɗi tushen haɗin kai na Kirista. Ya ce: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya. Kowanene da ke na gaskiya ya kan ji muryata.” (Yohanna 18:37) Saboda haka, amincewa da koyarwar Yesu tare da sauran hurariyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, yana da ikon haɗa kan almajiran Kristi na gaskiya.—1 Korinthiyawa 4:6; 2 Timothawus 3:16, 17.

Hakika, almajiran Yesu sukan yi tambayoyi ko kuma jayayya tsakaninsu wasu lokatai. Menene zai taimake su? Yesu ya yi bayani: “Sa’anda shi, Ruhu na gaskiya, ya taho, za ya bishe ku cikin dukan gaskiya: gama ba za ya faɗi daga kansa ba; amma dukan iyakar abin da ya ji, su za ya faɗi; za ya bayyana muku kuma abin da ke zuwa.” (Yohanna 16:12, 13) Da haka, ruhu mai tsarki na Allah zai taimaki almajiran Yesu na gaskiya su fahimci gaskiyar yadda Allah zai ci gaba da bayyana ta. Wannan ruhu kuma zai ba da ’ya’yan ruhu, kamar su ƙauna, farin ciki, da kuma salama, da za su kawo haɗin kai tsakaninsu.—Ayukan Manzanni 15:28; Galatiyawa 5:22, 23.

Yesu bai ƙyale a yi jayayya ba ko kuma a kafa rukuni tsakanin almajiransa; bai kuwa ba su ikon su sake fassara gaskiyar Allah ba don ta yi daidai da al’adu na addini na waɗanda za su sadu da su ba. Maimakon haka, a darensa na ƙarshe tare da su, ya yi addu’a: “Kuma ba domin waɗannan kaɗai ni ke yin addu’a ba, amma domin waɗancan kuma da ke bada gaskiya gareni ta wurin maganarsu: domin su duka su zama ɗaya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka, domin su kuma su zama cikinmu: domin duniya ta gaskata kai ne ka aiko ni.” (Yohanna 17:20, 21) Da haka, tabbataccen haɗin kai, cikin ruhu da gaskiya ne zai zama alamar da za ta bambanta almajiran Kristi daga lokacin da aka soma Kiristanci zuwa kwananmu. (Yohanna 4:23, 24) Duk da haka, coci a yau ba su da haɗin kai. Me ya kawo hakan?

Abin da Ya Sa Coci ba Su da Haɗin Kai

Abin da ya sa ake imani da ayyuka dabam dabam tsakanin waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne a yau shi ne cewa ba sa bin koyarwar Yesu. Wani marubuci ya ce: “Yadda yake dā, sababbin Kiristoci a yau suna amince da abin da yake biyan bukatunsu daga Littafi Mai Tsarki—kuma su ƙyale abubuwan da ba su jitu da nasu al’adu na addini” ba. Abin da Yesu da manzanninsa suka ce zai faru ke nan.

Alal misali, manzo Bulus da aka hure, ya rubuta wa abokinsa Timothawus mai kula: “Kwanaki za su zo inda ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu; za su kawarda kunnuwansu ga barin gaskiya, su karkata zuwa wajen tatsuniyoyi.” Za a yaudari dukan Kiristoci ne? A’a. Bulus ya ci gaba: “Amma kai, sai ka natsu cikin dukan abu, ka daure shan wuya, ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.” (2 Timothawus 4:3-5; Luka 21:8; Ayukan Manzanni 20:29, 30; 2 Bitrus 2:1-3) Timothawus da wasu Kiristoci masu aminci sun bi wannan hurarren gargaɗi.

Har Ila Kiristoci na Gaskiya Suna da Haɗin Kai

Kamar Timothawus, Kiristoci na gaskiya a yau suna natsuwa ta ƙin ra’ayin ’yan Adam, sun kuma amince da iko na Nassi kaɗai don koyarwar imaninsu. (Kolossiyawa 2:8; 1 Yohanna 4:1) A yin koyi da Kiristoci na ƙarni na farko, Shaidun Jehovah suna cika hidimarsu fiye da ƙasashe 230, suna kai wa mutane bisharar Mulkin a ko’ina, saƙon Yesu na asali. Ka yi la’akari da hanyoyi huɗu masu muhimmanci da suke yin koyi da Yesu da haɗin kai kuma suke yin Kiristanci na gaskiya a ko’ina da suke da zama.

Imaninsu daga Kalmar Allah ce. (Yohanna 17:17) Wani firist na wani yanki a Belgium ya rubuta game da su: “Abu ɗaya da za mu koya daga wurinsu [Shaidun Jehovah] shi ne niyyarsu na saurara ga Kalmar Allah da kuma gaba gaɗinsu su yi wa’azi game da kalmar.”

Suna Dogara ga Mulkin Allah ya sauƙaƙa matsaloli cikin dukan duniya. (Luka 8:1) A Barranquilla, Colombia, wani Mashaidi ya yi wa Antonio da yake tallafa wa wani rukunin siyasa magana. Mashaidin bai goyi bayan rukunin ba, bai kuma ɗaukaka wani ra’ayin siyasa ba. Maimakon haka, ya ce wa Antonio zai yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi da kuma ƙannensa mata kyauta. Ba da daɗewa ba Antonio ya gane cewa Mulkin Allah ne kaɗai begen da matalauta a Colombia da kuma dukan duniya suke da shi.

Suna ɗaukaka sunan Allah. (Matta 6:9) Sa’ad da Shaidun Jehovah suka sadu da Maria da farko, ’yar Katolika ce mai himma a Australia, ta yarda Shaidun su nuna mata sunan Allah cikin Littafi Mai Tsarki. Yaya ta ji? “Sa’ad da na ga sunan Allah da farko cikin Littafi Mai Tsarki, na yi kuka. Sanin cewa zan iya sanin sunan Allah kuma na yi amfani da shi ya motsa ni ƙwarai.” Maria ta ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma a lokaci na farko a rayuwarta, ta san irin mutumin da Jehovah yake kuma ta gina dangantaka ta dindindin da shi.

Ƙauna ta Haɗa Su. (Yohanna 13:34, 35) Wani labari a jaridar The Ladysmith-Chemainus Chronicle, Canada ta ce: “Kowane irin imani addininka yake bi, ko ma ba ka bin kowanne, ya kamata ka yaba wa Shaidun Jehovah 4,500 da suka yi aiki tuƙuru don su gina Majami’ar Taro na awon kafa 25,000 a Cassidy cikin mako ɗaya da rabi da ya shige . . . Yin haka da farin ciki ba tare da yin musu, jayayya, ko kuma su nemi ikon kansu ba, alamar Kiristanci na gaskiya ne.”

Ka yi la’akari da tabbacin. Yayin da ’yan tauhidi na Kiristendam, ’yan mishan, da masu zuwan coci suke fama da arangama a cocinsu, Kiristanci na gaskiya na ci gaba a dukan duniya. Hakika, Kiristoci na gaskiya suna yin aikinsu na wa’azi da kuma koyar da Kalmar Allah. (Matta 24:14; 28:19, 20) Idan kana cikin waɗanda suke “ajiyar zuci, suna kuwa kuka” domin abubuwan ƙazanta da suke faruwa yanzu kuma kana damuwa da rashin haɗin kai tsakanin addinin Kiristendam, muna gayyatarka ka bi Shaidun Jehovah a bauta ta haɗin kai na Kirista, na Allah makaɗaici na gaskiya, Jehovah.—Ezekiel 9:4; Ishaya 2:2-4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba