Coci Zai Tsira Kuwa?
“MUTANE a Britaniya har ila sun yi imani da Allah amma ba sa son su ba da kansu ga Kristi,” in ji Stephen Tirwomwe, limami a Uganda. Misalin shekara 20 da ta shige, ya tsira wa juyin shugabanci na ƙarfi da yaji da aka yi wa cocinsa a Uganda. A yau, yana wa’azi a kulob na maza a Leeds, Ingila, yana magana na minti goma kafin cacar karta ta kwashe hankalin masu sauraronsa.
Daga Britaniya, cocin Anglican Mission a Amirka da aka kafa kwanan bayan nan suna cikin irin wannan tarzoma ta ruhaniya. “Amirka ce yanzu take da jama’a mafi yawa a duniya da ba sa zuwan coci kuma marasa ruhaniya ne,” in ji mishan ɗin cikin Duniyar Gizonsu, (Web site). “Mu muka zama yankin da yake bukata a yi wa wa’azi.” Domin suna baƙin ciki cewa sun kasa yin canje-canje cikin cocinsu, ’yan mishan ɗin sun daina bin al’adunsu kuma suka soma tarayya da shugabannin Asiya da Afirka don su kawo hidimar addini wa Amirka.”
Amma, me ya sa ’yan mishan na Afirka, Asiya, da Latin American suke wa ‘mutane wa’azi’ a ƙasashen Turai da Amirka ta Arewa da suke da’awa su ƙasashen Kiristanci ne?
Su Wanene Ake Cetonsu?
Fiye da shekaru ɗari huɗu, ’yan mishan na Turai da suka ba da kansu sun ci gaba da yaɗuwa zuwa yankuna da suka mallaka, kamar Afirka, Asiya, Pacific, da Amirka ta Kudu. Manufarsu ita ce, su kai addininsu wa arna a waɗannan ƙasashe. A kwana a tashi, ’yan mallaka na Amirka, sun kafa ƙa’ida ta Kirista, suka sha kan ’yan mishan na Turai suka kafa nasu mishan a dukan duniya. Yanzu yanayin ya canja.
“Cibiyar [Kiristanci] ya canja in ji Andrew Walls, darekta da ya kafa
Centre for the Study of Christianity [Ƙungiyar Nazarin Kiristanci] a Ƙasashe da Ba na Turai ba. A shekara ta 1900, kashi 80 bisa ɗari na waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne daga Turai suke, ko kuma ’yan Amirka ta Arewa ne. Amma, a yau kashi 60 bisa ɗari na waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne suna zama a Afirka, Asiya, da Latin America. Labarai na kwanan bayan nan ya ce: “Cocin katolika a Turai suna ɗaukan firistoci daga Philippines da Indiya,” kuma “ɗaya cikin firistoci shida da suke hidima a cocin Katolika na Amirka an ɗauko su ne daga wata ƙasa.” ’Yan wa’azi na Afirka a Netherland, da yawancinsu ’yan Ankara ne, sun iske kansu “suna hidimar coci a wata nahiya.” Amma ’yan wa’azi daga Brazil suna manyan taro a ɓangarori dabam dabam na Britaniya. Wani marubuci ya ce: “Aikin mishan na Kirista ya koma baya.”
Ƙarin Tabbaci na Yin Arangama
Ana bukatar ’yan mishan musamman a nahiyoyin Turai da Amirka na Arewa da ba sa son addini. “A Scotland, Kiristoci ƙasa da kashi 10 bisa ɗari suna zuwan coci a kai a kai,” in ji wata jaridar labarai. Kalilan ne a Faransa da Jamus suke zuwan coci. Sa’ad da aka yi bincike, “misalin mutane kashi 40 bisa ɗari na ’yan Amirka da kuma ’yan Canada kashi 20 bisa ɗari suka ce suna zuwan coci a kai a kai,” in ji wani labari. Akasin haka, waɗanda suke zuwan coci a Philippines sun kusan kai kashi 70 bisa ɗari, haka yake kuma a sauran ƙasashe da suke tasowa.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne, masu zuwan coci a Afirka, Asiya, da Latin-America sun fi bin al’adu da waɗanda suke Turai da Amirka ta Arewa. Alal misali, sa’ad da aka yi wa Katolikawa da suke Amirka da kuma Turai tambaya, sun ci gaba da nuna rashin aminci ga ikon limamai da gardama da ’yanci da aka ba wa mata. A wata sassa kuma, Katolikawa da suke Nahiya ta Kudu, suna bin al’adu na cocinsu a kan waɗannan batutuwa. Da yake halin tallafa wa coci ya ci gaba da canjawa daga nahiya ta arewa zuwa nahiya ta kudu, ana daɗa samun dalilin arangama a nan gaba. Philip Jenkins, masani na tarihi da addini, ya ce: “Mai yiwuwa ne cewa a shekaru goma ko kuma ashirin nan gaba babu wani cikin cocin nahiya biyun nan da zai fahimci Kiristancin junansu ba.”
Domin waɗannan halaye, Walls ya ce batu na gaggawa shi ne “yadda Kiristoci a Afirka, Asiya, Latin American, da Amirka ta Arewa da kuma Turai za su iya zama tare a coci ɗaya, suna imani ɗaya.” Me kake tsammani? Coci za su iya tsira kuwa a duniya da take a rabe? Menene tushen haɗin kai na Kirista ta gaskiya? Talifi na gaba zai ba da amsa daga Nassi, tare da tabbaci da ya nuna rukunin Kiristoci da suke ci gaba a duniya.
[Hoto a shafi na 4]
Wannan coci na dā yanzu kantin cin abinci ne da ake kaɗe-kaɗe
[Inda aka Dauko]
AP Photo/Nancy Palmieri