Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 10/1 pp. 3-4
  • Tambayoyi Masu Yawa—Amma Kalilan Amsoshi Masu Gamsarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Masu Yawa—Amma Kalilan Amsoshi Masu Gamsarwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tangarɗa ce ga Imani?
  • Allah Yana Yi Mana Horo Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Biɗan Ilimi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Sashe na 1—Allah Yana Kula Da Mu Kuwa Da Gaske?
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 10/1 pp. 3-4

Tambayoyi Masu Yawa—Amma Kalilan Amsoshi Masu Gamsarwa

DA SAFE a hutun Ranar Dukan Waliyai da aka yi ranar 1 ga Nuwamba, 1755, an yi girgizar ƙasa da ta shafi Lisbon sa’ad da yawancin mazaunanta suke cikin coci. Gidaje dubbai suka halaka, kuma dubban mutane suka mutu.

Bai daɗe ba bayan wannan bala’i, marubucin yaren Faransa, Voltaire ya rubuta Poème sur le désastre de Lisbonne (waƙar bala’in Lisbon), da a ciki ya ƙi da’awar da ake yi cewa bala’in daga wurin Allah ne domin zunuban mutanen. Yana cewa ’yan Adam ba za su iya fahimta ko kuma bayyana irin wannan aukuwa ta bala’i ba, Voltaire ya rera:

Halitta ta yi shuru, muna ta tambaya amma babu amsa;

Muna bukatar Allah da yake magana da mutane.

Hakika, ba Voltaire ne na farko da ya yi tambayoyi game da Allah ba. A duk tarihin ’yan Adam, masifu da bala’i sun sa mutane suna tambayoyi. Shekaru dubbai da suka wuce, uban iyali Ayuba, a ɗan lokaci kawai ya yi hasarar dukan yaransa kuma muguwar cuta ta same shi, ya yi tambaya “Don me [Allah] ke bada haske ga wanda ya ke cikin azaba, rai kuma ga masu-fidda zuciya”? (Ayuba 3:20) A yau, mutane da yawa suna damuwa da yadda nagarin Allah mai ƙauna kamar ba ya damuwa da wahala da kuma rashin gaskiya.

Mutane da yawa suna ƙin yarda da ra’ayin cewa akwai Mahalicci da yake damuwa da mutane domin yunwa, yaƙi, ciwo, da kuma mutuwa. Wani shehun malami da bai yarda akwai Allah ba ya lura haka: Allah ba shi da wata hujja ya ƙyale yaro ya wahala, . . . sai dai ko babu Allah.” Manyan bala’i kamar halaka mai girma a lokacin Yaƙin Duniya na II ya sa mutane su kammala haka nan. Ka lura da wani kalami da marubuci Bayahudi ya yi cikin wata jarida: “A bayani mai sauƙi, abin da ya faru a Auschwitz ita ce cewa babu Allahn da zai sa hannu a harkokin ’yan Adam.” Daidai da wani ƙirge da aka yi a Faransa a shekara ta 1997, ƙasar ta addinin Katolika ne, mutane kashi 40 bisa ɗari suna shakkar Allah ya wanzu saboda ƙare-dangi da ake yi, irin wanda aka yi a Rwanda a shekarar 1994.

Tangarɗa ce ga Imani?

Me ya sa Allah bai sa hannu don ya hana miyagun abubuwa daga faruwa ba? Wani ɗan tarihi na Katolika ya yi da’awar cewa tambayar nan “tangarɗa ce sosai ga imani” a wurin mutane da yawa. Ya yi tambaya: “Shin, zai yiwu ne a gaskata da Allah wanda yake kallo kawai sa’ad da mutane da yawa marasa laifi suke mutuwa kuma ana ƙarar da dangi a duniya sa’in nan ba ya yin kome don ya hana hakan faruwa?”

Wani talifi cikin jaridar La Croix na Katolika ma ya ce: “Idan bala’i na tarihi ne, cin gaba na fasaha, tsarar bala’i, rukunin aika laifi, ko kuma mutuwar wani da muke ƙauna, a kowanne cikin waɗannan yanayi, mutanen da suka tsorata suna zuba ido wa Allah. Ina Allah yake? Suna neman amsa. Ba shi ne Wanda Ba Ya Damuwa, da Ba Ya Kula ba?”

Paparuma John-Paul na II ya tattauna wannan batun cikin wata wasiƙarsa ta manzanci na shekara ta 1984, Salvifici Doloris. Ya rubuta: “Ko da yake yanayin duniya yana ba wa mutane zarafin sanin Allah ya wanzu, hikimarsa, iko da girma, mugunta da wahala kamar sun rufe halayen Allah, a wasu lokatai sun rufe sarai, musamman ma idan bala’i suna faruwa kullayaumi bi da bi kuma ana laifi da yawa da ba a yin horon da ya dace.”

Wanzuwar Allah mai ƙauna kuma mafi ƙarfi yadda aka nuna cikin Littafi Mai Tsarki ya yi daidai ne da yadda mutane suke wahala da yawa haka? Yana sa hannu ne ya hana bala’i? Ashe, yana yi mana wani abu ne a yau? Kamar yadda Voltaire ya ce, akwai “Allah da yake magana da mutane” ne ya amsa waɗannan tambayoyi? Sai ka karanta talifi na gaba ka sami amsar.

[Hotuna a shafi na 3]

Halakar Lisbon a shekara ta 1755 ta sa Voltaire ya yi da’awar cewa irin aukuwan nan mutane ba sa iya fahimtawa

Inda aka Daukos]

Voltaire: From the book Great Men and Famous Women; Lisbon: J.P. Le Bas, Praça da Patriarcal depois do terramoto de 1755. Foto: Museu da Cidade/Lisboa

[Hoto a shafi na 4]

Mutane da yawa suna shakkar akwai Allah saboda ƙare-dangi da aka yi a Rwanda

[Inda aka Dauko]

AFP PHOTO

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba