Biɗan Ilimi
“JAHILCI bai fi ilimi ba,” in ji Enrico Fermi, manazarcin ƙarfin halittu wanda ya ci kyautar Nobel. Wasu ba za su yarda da haka ba, za su ce abin da ba ka sani ba ba zai ɓata maka rai ba. Amma ga yawanci, abin da Fermi ya ce gaskiya ne ba kawai a sashen bincike na kimiyya ba amma a sauran fasalolin rayuwa. Jahilci rashin sanin gaskiya ne, kuma hakan ya sa yawancin mutane suna ta yawo cikin duhun jahilci, na ɗabi’a da na ruhaniya da daɗewa.—Afisawa 4:18.
Shi ya sa mutane masu tunani suke neman ilimi. Suna son su san dalilin da ya sa muke duniya da kuma inda muka nufa. Bincikensu ya sa sun bi hanyoyi dabam dabam. Bari mu ɗan bincika wasu daga cikinsu.
Hanyar Addini
In ji al’adar Buddhawa, wahalar ’yan adam da mutuwa sun dame Siddhārtha Gautama, wanda ya kafa Buddhanci sosai. Ya tambayi malaman addinin Hindu su taimake shi neman “hanyar gaskiya.” Wasu sun ce ya bi yoga da kuma hana kai. Gautama ya zaɓi yin bimbini a matsayin hanyar samun ilimi na gaskiya.
Wasu sun yi amfani da kwayoyin da ke shafar hankali wajen neman ilimi. Alal misali, a yau, ’yan Native American Church (Cocin ’Yan Amirka) sun ce wasu kwayoyi masu sa gane-gane hanya ne “mai bayyana ɓoyayyun fahimi.”
Wani Bafaranshe mai ussan ilimin a ƙarni na sha takwas, Jean-Jacques Rousseau, ya gaskata cewa duk wani sahihin matambayi na iya samun wahayi na ruhaniya daga Allah. Ta yaya? Ta wajen bin “abin da Allah ya gaya wa zuciya.” Da haka, yadda ka ji game da abubuwa, wato abin da motsin zuciyarka da lamirinka suka gaya maka, zai zama “tabbataccen ja-gora a waɗannan ra’ayoyin mutane da aka dagula,” in ji Rousseau.—History of Western Philosophy.
Ta Hanyar Tunani
Yawancin mutanen zamanin Rousseau sun ƙi amincewa da irin tafarkin addinin nan. Alal misali, ɗan Faransa Voltaire, yana ganin cewa maimakon addini ya ilimantar da mutane, ya dulmuya Turai cikin jahilci, da camfi, da kuma rashin jituwa na dogon lokaci, lokacin da wasu ’yan tarihi suka kira Zamanin Jahilci.
Voltaire ya shiga ƙungiyar mutane masu tunani na Turai da ake kira Ilimi. Mabiyansa sun bi ra’ayin Helenawa na dā, wato tunanin mutane da kuma bincike na kimiyya sune ainihin ilimi na gaskiya. Wani ɗan ƙungiyar masu tunani, Bernard de Fontenelle ya ce tunanin mutane zai kai su ga “wani ƙarni wanda zai ci gaba da samun ilimi, wanda zai sa sauran ƙarnuka na dā za su zama jahilai idan aka gwada su.”—Encyclopædia Britannica.
Waɗannan kaɗan ne kawai cikin ra’ayoyin da suka sha bambam game da yadda za a sami ilimi. Akwai wata “tabbatacciyar ja-gora” da za mu juya wa domin neman gaskiya? Ka yi la’akari da abin da talifi na gaba zai ce game da tabbatacciyar hanyar samun ilimi.
[Hotuna a shafi na 3]
Gautama (Buddha), Rousseau, da kuma Voltaire sun bi hanyoyi dabam dabam wajen neman ilimi