Kana Da Halin “Jira”?
“Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma? kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai.”—2 BITRUS 3:11, 12.
1, 2. Yaya za mu kwatanta kasance da halin “jira” game da ranar Jehovah?
KA ZANA hoton zuci, wani iyali na jiran baƙi su zo su ci abincin dare. Lokacin da aka ba su ya yi kusa. Matar ta taƙure tana shirya abubuwa na ƙarshe don abincin. Mijinta da yaransu suna taimako su tabbata cewa kome ya yi daidai. Kowa na farin ciki. Hakika, dukan iyalin na jiran zuwan baƙin kuma suna marmarin abinci mai kyau da kuma zumunci.
2 Da yake mu Kiristoci ne, muna jiran wani abu da ya fi muhimmanci. Jiran menene? Dukanmu muna jiran ‘ranar Jehovah’! Har sai ta zo, muna bukatar mu zama kamar annabi Mikah, wanda ya ce: “Zan saurara ga Ubangiji; zan jira Allah na cetona.” (Mikah 7:7) Wannan yana nufin rashin aiki ne? A’a. Da akwai aiki da yawa da za a yi.
3. In ji 2 Bitrus 3:11, 12, wane hali Kiristoci za su kasance da shi?
3 Manzo Bitrus ya taimake mu mu kasance da halin da ya dace sa’ad da muke jira. Ya ce: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma? kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai.” (2 Bitrus 3:11, 12) Ka lura da wannan furcin, Bitrus ba tambaya yake yi ba game da irin mutane da ya kamata mu zama. A wasiƙunsa biyu da Allah ya hure, ya kwatanta irin mutane da ya kamata Kiristoci su zama. Ya kuma gargaɗe su su ci gaba da bin “tasarrufi mai-tsarki da ibada.” Ko da shekara 30 ya shige tun lokacin da Yesu Kristi ya ba da alamar “cikar zamani,” Kiristoci ba za su daina kasance a faɗake ba. (Matta 24:3) Za su yi “sauraron . . . [s]una kuwa marmarin zuwan” ranar Jehovah.
4. Menene “sauraron ranar Allah, [m]una kuwa marmarin zuwanta” ya ƙunsa?
4 Kalmar Helenanci da aka fassara “marmarin zuwanta” a zahiri na nufin “hanzartawa.” Hakika, a zahiri ba za mu iya ‘hanzarta’ ranar Jehovah ba. Domin ba mu “san rana ko sa’a ba” da Yesu Kristi zai zo ya zartar da hukunci a kan magabtan Ubansa. (Matta 24:36; 25:13) Wata majiya ta yi bayani cewa tushen aikatau na furcin nan “hanzartawa” a nan na nufin “ ‘a sa ya yi sauri’ kuma yana da nasaba ta kurkusa da ‘a kasance da himma, ƙwazo, a damu game da wani abu.’ ” Saboda haka, Bitrus yana ariritar ’yan’uwa masu bi su so ranar Jehovah sosai. Za su iya yin haka ta yin marmarin zuwanta koyaushe. (2 Bitrus 3:12) Da yake “babbar rana mai-ban razana ta Ubangiji” ta yi kusa sosai, ya kamata mu kasance da irin wannan halin.—Joel 2:31.
Jira Tare da “Tasarrufi Mai-Tsarki”
5. Ta yaya za mu nuna cewa muna so mu ga ‘ranar Jehovah’?
5 Idan muna so mu tsira wa ranar Jehovah, za mu sa wannan ya zama a bayyane ta namu “tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma.” Furcin nan “tasarrufi mai-tsarki” zai tuna mana gargaɗin Bitrus: “Kamar ’ya’yan biyayya, ba za ku daidaita kanku bisa sha’awoyinku na dā a zamanin jahilcinku ba: amma yadda shi wanda ya kira ku mai-tsarki ne, ku kuma ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi; domin an rubuta, Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.”—1 Bitrus 1:14-16.
6. Don mu kasance da tsarki, dole mu yi menene?
6 Don mu kasance da tsarki, dole mu riƙe tsabta ta jiki, ta hankali, ta ɗabi’a, da ta ruhaniya. Muna shiri ne domin ‘ranar Jehovah’ ta wajen kasance da tsarki mu ɗaɗɗaya masu riƙe da sunan Jehovah? Ba shi da sauƙi a kasance da tsarki a yau, domin mizanan ɗabi’a na duniya na ƙara lalacewa. (1 Korinthiyawa 7:31; 2 Timothawus 3:13) Muna iske cewa bambanci tsakanin namu mizanan ɗabi’a da na duniya suna ƙaruwa? Idan ba haka ba, muna da dalilin damuwa. Ba zai yiwu ba cewa ɗabi’armu, ko da sun fi na duniya, suna ragewa? Idan haka ne, muna bukatar mu ɗauki mataki mai kyau mu daidaita al’amura don mu faranta wa Allah rai.
7, 8. (a) Ta yaya za mu yi banza da muhimmancin sa hannu cikin “tasarrufi mai-tsarki”? (b) Wace gyara za a bukaci yi?
7 Da zuwan hotunan tsirarun mutane a Intane kuma domin yana a ɓoye, wasu da a dā ba su da hanyar samun littattafan lalata yanzu suna samun “zarafin jima’i marar iyaka,” in ji wani likita. Idan za mu nemi irin waɗannan wuraren da ba su da tsabta a Intane, babu shakka za mu ƙyale umurnin Littafi Mai Tsarki na kada mu “taɓa wani abu mai-ƙazanta.” (Ishaya 52:11) Za mu na ‘marmarin zuwan ranar Jehovah’ da gaske? Ko kuma a zuciyarmu muna tura ranar zuwa gaba, da tunanin cewa ko idan ma muna ɓata zuciyarmu da munanan littattafai, har ila muna da lokacin tsabtace kanmu? Idan muna da matsala a waɗannan wurare, da gaggawa mu roƙi Jehovah ya ‘kawarda idanunmu ga barin duba abin banza, kuma ya rayar da mu cikin tafarkunsa’!—Zabura 119:37.
8 Yawancin Shaidun Jehovah, matasa da tsofaffi suna manne wa mizanan Allah mai girma kuma suna guje wa sha’awar lalata na wannan duniya. Da yake sun san gaggawar lokacinmu da gargaɗin Bitrus cewa “ranar Ubangiji kamar ɓarawo za ta zo,” sun ci gaba da bin “tasarrufi mai-tsarki.” (2 Bitrus 3:10) Ayyukansu ya nuna cewa suna “sauraron ranar Allah, [s]una kuwa marmarin zuwanta.”a
Jira Tare da ‘Ayyuka na Ibada’
9. Me ya kamata ibada ta motsa mu mu yi?
9 ‘Ayyuka na ibada’ yana da muhimmanci idan za mu yi marmarin zuwan ranar Jehovah. “Ibada” ta ƙunshi ɗaukaka Allah da ke motsa mu mu yi abin da ke faranta masa. Manne wa Jehovah cikin aminci motsawa ce da ke ɗaukaka irin waɗannan ayyuka na ibada. Nufinsa ne “dukan [ire-iren] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:4) Allah “ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:9) Saboda haka, bai kamata ibadarmu ta motsa mu mu ƙara ƙoƙari mu taimake mutane su koya game da Jehovah kuma su yi koyi da shi ba?—Afisawa 5:1.
10. Me ya sa za mu tsare kanmu daga “ruɗin dukiya”?
10 Rayuwarmu za ta cika da ayyuka na ibada idan mun fara biɗan Mulkin Allah. (Matta 6:33) Wannan ya ƙunshi kasance da ra’ayin da ya dace game da abin duniya. Yesu ya yi kashedi: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luka 12:15) Ko da zai yi wuya mu yi tunani cewa za mu makanta ta son kuɗi, zai yi kyau mu lura cewa ‘ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya,’ su kan ‘shaƙe maganar’ Allah. (Matta 13:22) Ƙila ba zai yi sauƙi a samu na biyan bukata ba. A wasu ɓangarorin duniya, mutane da yawa suna tunani cewa don a yi rayuwa mai kyau, za su ƙaura zuwa ƙasa da ta fi arziki, wataƙila su bar iyalansu na ’yan shekaru. Har ma wasu cikin mutanen Allah sun bi irin tunanin nan. Ta tafiya wata ƙasa, suna iya yi wa iyalinsu tanadin moriyar zamani. Amma, me zai faru da yanayin ruhaniya na waɗanda suke ƙauna a gida? Ba tare da shugabanci da ya dace a gida ba, za su samu ruhaniyar da ake bukata don su tsira wa ranar Jehovah?
11. Ta yaya wani da ya ƙaura ya nuna cewa ayyuka na ibada sun fi arziki muhimmanci?
11 Wani da ya tafi wata ƙasa don neman aiki daga Philippines ya koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki daga Shaidun Jehovah a Japan. Da ya koya game da hakkin shugabanci na Nassi, ya fahimta cewa yana bukatar ya taimaki iyalinsa su zama masu bauta wa Jehovah. (1 Korinthiyawa 11:3) Matarsa can gida ta yi hamayya ƙwarai da sabon imaninsa, tana so ya ci gaba da aika da kuɗi maimakon ya dawo gida ya koya wa iyalin imaninsa da ke bisa Littafi Mai Tsarki. Amma gaggawar lokaci da damuwa game da waɗanda yake ƙauna, sun motsa shi ya koma gida. Haƙurinsa a bi da waɗanda suke cikin iyalinsa da ƙauna ya samu albarka. Da shigewar lokaci, iyalinsa suka zama da haɗin kai a bauta ta gaskiya, kuma matarsa ta shiga hidima ta cikakken lokaci.
12. Me ya sa ya kamata mu sa abubuwa na ruhaniya farko a rayuwa?
12 Za a iya kamanta yanayinmu da na mutane da suke cikin gida da ke cin wuta. Hikima ce a yi ƙoƙarin fitar da kayayyaki daga gidan da yake son ya fāɗi? Maimako, ba zai fi muhimmanci ba a ceci rayuka—namu da na waɗanda suke cikin iyalinmu da wasu da suke cikin gidan? To, wannan zamanin tana kan faɗiwa, kuma rayuka suna cikin haɗari. Fahimta wannan, babu shakka ya kamata mu saka abubuwa na ruhaniya farko kuma mu mai da hankali da himma a aikin wa’azin Mulki na ceton rai.—1 Timothawus 4:16.
Muna Bukatar Mu Zama “Marasa-Aibi”
13. Wane yanayi ya kamata mu so mu kasance ciki sa’ad da ranar Jehovah ta auko?
13 Da yake nanata muhimmancin kasance da halin jira, Bitrus ya ce: “Ƙaunatattu, tun da ku ke sauraron waɗannan al’amura, sai ku bada aniyya [Allah [y]a tararda ku cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gabansa.” (2 Bitrus 3:14) Ƙari ga gargaɗinsa cewa mu sa hannu cikin tasarrufi mai tsarki da ayyuka na ibada, Bitrus ya nanata muhimmancin Jehovah ya iske mu mutane da jinin Yesu mai tamani ya tsabtace. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Wannan yana bukatar mutum ya ba da gaskiya cikin hadayar Yesu kuma ya zama bawa da ya keɓe kansa ga Jehovah kuma ya yi baftisma.
14. Menene kasance “marasa-aibi” ya ƙunsa?
14 Bitrus ya ƙarfafa mu mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu kasance “marasa-aibi.” Muna sa tufafinmu na halaye da kuma mutuntakar Kirista marasa aibi, kuma duniya ba ta saka musu tabo ba? Sa’ad da muka ga tabo a tufafinmu, muna ƙoƙari mu cire shi nan da nan. Idan wata taguwa ce da muka fi so, muna mai da hankali game da wanke ta. Haka muke ji idan tabo ta taɓa tufafinmu na Kirista, a alamance, domin wasu kasawa a mutuntakarmu ko kuma a hali?
15. (a) Me ya sa aka ce Isra’ilawa su sa tuntaye a shafin rigarsu? (b) Me ya sa bayin Jehovah na zamanin yau suka kasance dabam?
15 An umurci Isra’ilawa su “sa tuntaye a shafin rigarsu” kuma “cikin kowane tuntu na shafin rigarsu za su ɗaura shuɗin zare.” Me ya sa? Domin su tuna da dokokin Jehovah, su kiyaye su, kuma su “zama masu-tsarki” ga Allahnsu. (Litafin Lissafi 15:38-40) Mu bayin Jehovah na zamani, mun kasance dabam da duniya domin muna kiyaye dokokin Allah da kuma ƙa’idodinsa. Alal misali, muna riƙe da ɗabi’a mai tsarki, muna daraja tsarkin jini, kuma muna guje wa kowacce irin bautar gumaka. (Ayukan Manzanni 15:28, 29) Mutane da yawa suna daraja mu don aniyarmu mu kasance marasa aibi.—Yaƙub 1:27.
Muna Bukatar Mu Kasance “Marasa-Laifi”
16. Menene kasance “marasa-laifi” ya ƙunsa”?
16 Bitrus ya kuma ce ya kamata a iske mu “marasa-laifi.” Yaya wannan zai yiwu? Ana iya wanke tabo amma ban da laifi. Laifi na nuna cewa wani abu a ciki bai yi daidai ba. Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa Kiristoci a Filibbi: “Sai ku aikata abu duka banda gunaguni da gardama; domin ku zama marasa-zargi, marasa-illa, ’ya’yan Allah marasa-aibi a cikin tsakiyar karkataciyar tsara mai-serare, da a ke ganinku daga cikinsu kamar haskoki a cikin duniya.” (Filibbiyawa 2:14, 15) Idan mun bi wannan gargaɗin, za mu guje wa gunaguni da gardama kuma mu bauta wa Allah da tsarkakken nufi. Ƙauna ga Jehovah da maƙwabta ne za ta motsa mu yayin da muke wa’azin “wannan bishara kuwa ta mulki.” (Matta 22:35-40; 24:14) Ƙari ga haka, za mu ci gaba da sanar da bishara ko da yawancin mutane ba za su fahimta abin da ya sa muke ba da lokacinmu don mu taimake wasu su koya game da Allah da Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ba.
17. Menene ya kamata ya zama burinmu sa’ad da muka sami gata a ikilisiyar Kirista?
17 Da yake muna son a iske mu “marasa-laifi,” zai yi kyau mu bincika nufinmu a dukan abubuwa da muke biɗa. Mun bar hanyar duniya na yin abubuwa na son kai, kamar su ƙoƙarin neman arziki ko kuma iko. Idan muna burin samun gata a cikin ikilisiyar Kirista, bari nufinmu koyaushe ya kasance da tsarki kuma ƙauna ga Jehovah da wasu koyaushe tana motsa mu. Abu mai kyau ne a ga maza na ruhaniya suna “biɗan aiki na [mai kula]” da farin ciki da sha’awa suna wa Jehovah da ’yan’uwansu masu bi hidima. (1 Timothawus 3:1; 2 Korinthiyawa 1:24) Hakika, waɗanda suka cancanta su yi hidima na dattawa suna “kiwon garken Allah . . . da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta, amma da karsashin zuciya; ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.”—1 Bitrus 5:1-4.
Muna Bukatar Mu Kasance “Cikin Salama”
18. Waɗanne halaye aka san Shaidun Jehovah da su?
18 A ƙarshe, Bitrus ya gaya mana mu kasance “cikin salama.” Don mu yi daidai da wannan farilla, muna bukatar mu kasance da salama da Jehovah da maƙwabcinmu. Bitrus ya nanata muhimmancin kasance da “ƙauna mai-huruwa zuwa ga juna” da kasance da salama tare da ’yan’uwanmu Kiristoci. (1 Bitrus 2:17; 3:10, 11; 4:8; 2 Bitrus 1:5-7) Don mu ci gaba da salamarmu, dole ne muna ƙaunar juna. (Yohanna 13:34, 35; Afisawa 4:1, 2) Ana ganin ƙaunarmu da salama musamman sa’ad da muka yi taron dukan ƙasashen duniya. A wani taro a Costa Rica a shekara ta 1999, wani mai sayar da kaya a filin jirgin sama ya ji haushi domin Shaidu na yankin da suke marabtar waɗanda suke zuwa taron suna tare masa wajen kasuwanci. Amma a rana ta biyu, ya lura da ƙauna da salama da aka nuna a marabtar waɗanda suka hallara, ko da Shaidu na yankin ba su san su ba. A rana ta ƙarshe, mai sayar da kayan shi ma ya yi wa waɗanda suka halarci taron maraba kuma ya ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
19. Me ya sa yake da muhimmanci mu biɗi salama da ’yan’uwa masu bi?
19 Biɗan salama ta gaske da ’yan’uwanmu na ruhaniya zai shafi yadda muke jiran ranar Jehovah da sabuwar duniya da ya yi alkawarinta. (Zabura 37:11; 2 Bitrus 3:13) A ce mun iske shi da wuya mu yi salama da wani ɗan’uwa mai bi. Za mu yi tunanin zama tare da shi cikin salama a Aljanna? Idan wani ɗan’uwa yana da wata ƙara game da mu, ya kamata nan da nan mu ‘je mu shirya da shi.’ (Matta 5:23, 24) Yin haka yana da muhimmanci idan za mu kasance da salama da Jehovah.—Zabura 35:27; 1 Yohanna 4:20.
20. A waɗanne hanyoyi ya kamata a nuna halin “jira”?
20 Muna “sauraron ranar Allah, [m]una kuwa marmarin zuwanta”? Muna nuna cewa muna so mu ga ƙarshen mugunta ta kasancewa da tsarki a wannan lalatacciyar duniya. Ƙari ga haka, ayyukanmu na ibada sa nuna cewa muna sauraron zuwan ranar Jehovah da kuma rayuwa cikin sarautar Mulki. Kuma muna nuna cewa muna zaton rayuwa cikin sabuwar duniya ta salama idan muna biɗan salama yanzu da ’yan’uwanmu masu bi. Ta haka, muna nuna cewa muna da halin “jira” kuma muna “sauraron ranar Allah, [m]una kuwa marmarin zuwanta.”
[Hasiya]
a Don misalai, ka duba Hasumiyar Tsaro na 1 ga Janairu, 2000, shafi na 31 da 1997 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafi na 51.
Ka Tuna?
• Menene yake nufi a yi ‘marmarin zuwan ranar Jehovah’?
• Ta yaya halin “jira” ke bayyana a halayenmu?
• Me ya sa ‘ayyuka na ibada’ ke da muhimmanci?
• Menene dole mu yi don Jehovah ya iske mu “cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi”?
[Hoto a shafi na 9]
Ana nuna halin “jira” cikin tasarrufi mai tsarki
[Hotuna a shafi na 10]
Aikin wa’azin Mulki yana ceton rai
[Hoto a shafi na 12]
Yayin da muke jiran ranar Jehovah, bari mu biɗi salama da wasu