Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 11/15 p. 20-p. 22 par. 11
  • Darussa Daga Wasiƙun Yaƙub da Bitrus

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Wasiƙun Yaƙub da Bitrus
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ALLAH YANA BA DA HIKIMA GA WAƊANDA SUKE “ROƘO DA BANGASKIYA”
  • (Yaƙ. 1:1–5:20)
  • ‘KU TSAYA CIKIN BANGASKIYA’
  • (1 Bit. 1:1–5:14)
  • ‘RANAR UBANGIJI ZA TA ZO’
  • (2 Bit. 1:1–3:18)
  • “Ku Yi La’akari Da Irin Mutane Da Ya Kamata Ku Zama!”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Saurara Ga Kalmomin Annabci Na Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Kana Da Halin “Jira”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 11/15 p. 20-p. 22 par. 11

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Wasiƙun Yaƙub da Bitrus

KUSAN shekaru 30 bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., manzo Yaƙub, ɗan’uwan Yesu, ya rubuta wasiƙa zuwa ‘ƙabilai goma sha biyu’ na Isra’ila ta ruhaniya. (Yaƙ. 1:1) Manufarsa ita ce: ya motsa su su ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su jimre sa’ad da suke fuskantar jarrabobi. Ya kuma ba da umurni don ya daidaita matsalolin da ke cikin ikilisiyoyi.

Kafin Nero da ke sarauta a Daular Roma ya soma tsananta wa Kiristoci a shekara ta 64 A.Z., manzo Bitrus ya rubuta wasiƙarsa ta farko zuwa Kiristoci, yana ƙarfafa su su tsaya da ƙarfi a cikin gaskiya. A wasiƙarsa ta biyu, wadda ya rubuta jim kaɗan da rubuta na farko, Bitrus ya ƙarfafa ’yan’uwansa masu bi su mai da hankali ga kalmar Allah kuma ya yi musu gargaɗi game da ranar Jehobah da ke tafe. Babu shakka, za mu amfana idan muka mai da hankali ga saƙonnin da ke cikin wasiƙun Yaƙub da Bitrus.—Ibran. 4:12.

ALLAH YANA BA DA HIKIMA GA WAƊANDA SUKE “ROƘO DA BANGASKIYA”

(Yaƙ. 1:1–5:20)

Yaƙub ya rubuta: “Mai-albarka ne mutum wanda ya daure da jaraba: gama sa’anda ya amintu, za shi karɓi rawanin rai.” Ga waɗanda suke “roƙo da bangaskiya,” Jehobah yana ba su hikimar da suke bukata don su jimre jarrabobi.—Yaƙ. 1:5-8, 12.

Waɗanda suka zama “masu-koyaswa” a cikin ikilisiya suna bukatar bangaskiya da hikima. Bayan ya kira harshe “ƙanƙanin gaɓa” da zai iya ‘ƙazantar da dukan jiki,’ Yaƙub ya yi gargaɗi game da abubuwan duniya da za su iya lalata dangantakar mutum da Allah. Ya kuma bayyana matakan da mutumin da ke rashin lafiya ta ruhaniya yake bukatar ya ɗauka don ya warke.—Yaƙ. 3:1, 5, 6; 5:14, 15.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

2:13, Littafi Mai Tsarki.—Ta wace hanya ce ‘jin ƙai yake rinjayar hukunci’? Idan ya zo ga ba da lissafin abin da muka yi ga Allah, yana yin la’akari ne da jin ƙai da muka nuna wa mutane kuma ya gafarta mana bisa hadayar fansa ta Ɗansa. (Rom. 14:12) Wannan ba dalili ba ne mai kyau da zai sa mu bar jin ƙai ya zama fitaccen hali a rayuwarmu?

4:5—Wane nassi ne Yaƙub ya yi ƙaulinsa a nan? Ba wai Yaƙub yana ƙaulin wata aya ba ce. Amma waɗannan hurarrun kalaman wataƙila suna bisa abubuwan da nassosi kamar su Farawa 6:5; 8:21; Misalai 21:10; da Galatiyawa 5:17 suka ce ne.

5:20—“Wanda ya juyo da mai-zunubi ga barin ratse hanyarsa” zai ceci ran wanene daga mutuwa? Kiristan da ya juyo da mai zunubi daga zunubansa ya ceci ran mutumin da ya tuba daga mutuwa ta ruhaniya wataƙila kuma daga halaka ta har abada. Mutumin da ya taimaka wa mai zunubin zai “[rufe zunuban mutumin] masu yawa kuma.”

Darussa Dominmu:

1:14, 15. Sha’awa marar kyau ce ke jawo zunubi. Saboda haka, bai kamata mu yi sha’awar abubuwa marar kyau ba ta wajen yin tunaninsu. Maimakon haka, muna bukatar mu “maida hankali” ga abubuwa masu ƙarfafawa kuma mu cika hankulanmu da zukatanmu da su.—Filib. 4:8.

2:8, 9. Nuna “tara” bai jitu da “shari’an nan ba’sarauciya” ta ƙauna ba. Saboda haka, Kiristoci na gaskiya ba sa nuna son kai.

2:14-26. An ‘cece mu ta wurin bangaskiya,’ ba “daga ayyuka” na Dokar Musa ba ko kuwa waɗanda Kiristoci suke yi. Bai kamata bangaskiyarmu ta kasance ta baki ba kawai. (Afis. 2:8, 9; Yoh. 3:16) Ya kamata ta motsa mu mu yi abubuwan da suka jitu da nufin Allah.

3:13-17. “Hikima mai-fitowa daga bisa” babu shakka ta ɗara hikimar ‘duniya, ta jiki, da ta Shaiɗan!’ Mu ci gaba da ‘biɗan hikima ta sama kamar yadda a ke biɗan ɓoyayyun dukiya.’—Mis. 2:1-5.

3:18. “Masu-yin salama” za su shuka iri na bisharar Mulki ne da “salama.” Yana da muhimmanci mu kasance masu salama ba masu girman kai ko rigima ba, ko ’yan ta da zaune tsaye.

‘KU TSAYA CIKIN BANGASKIYA’

(1 Bit. 1:1–5:14)

Bitrus ya tuna wa ’yan’uwansa masu bi game da ‘begensu mai-rai’ na zuwa sama. Bitrus ya ce su “zaɓaɓen iri ne, priesthood basarauci, al’umma mai-tsarki.” Bayan ya ba da shawara game da biyayya, ya aririci dukansu su ‘zama hankalinsu ɗaya, masu-juyayi, suna yin ƙauna kamar ’yan’uwa, masu-tabshin zuciya, masu-tawali’u.’—1 Bit. 1:3, 4; 2:9; 3:8.

Tun da yake “ƙarshen [zamanin Yahudawa] ya gabato,” Bitrus ya gargaɗi ’yan’uwa su ‘kame kansu, su natsu, domin su yi addu’a.’ Ya gaya musu: “Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. . . . Ku yi tsayayya da [Shaiɗan], kuna dagewa kan bangaskiyarku.”—1 Bit. 4:7; 5:8, 9.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

3:20-22—Ta yaya baftisma take cetonmu? Waɗanda suke son su sami ceto suna bukatar su yi baftisma. Amma fa, yin baftisma ba ya nufin cewa mun sami ceto. Ana samun ceto ainihi domin “tashin Yesu Kristi” daga matattu. Dole ne wanda zai yi baftismar ya gaskata cewa zai iya samun ceto ne kawai domin Yesu ya yi mutuwar hadaya, aka ta da shi daga matattu, kuma yana “hannun dama na Allah,” cike da iko bisa masu rai da matattu. Baftismar da aka yi cikin irin wannan imanin ita ce ta yi daidai da ‘masu-rai takwas, da suka tsira daga ruwa.’

4:6—Su wanene “matattu” da aka yi wa “wa’azin bishara”? Su ne waɗanda suka zama ‘matattu ta wurin laifofinsu da zunubansu,’ ko kuwa waɗanda suke mace a ruhaniya kafin su ji bishara. (Afis. 2:1) Amma, bayan sun ba da gaskiya ga bishara, sun zama ‘rayayyu’ a ruhaniya.

Darussa Dominmu:

1:7. Don bangaskiyarmu ta kasance da amfani sosai, dole ne ta kasance tabbatacciya ko kuwa wadda aka gwada. Irin wannan bangaskiyar mai ƙarfi ce take “ceton rai.” (Ibran. 10:39) Bai kamata mu guji gwajin bangaskiyarmu ba.

1:10-12. Mala’iku suna ɗokin gani kuma su fahimci koyarwa masu wuya ta ruhaniya da annabawan Allah na dā suka rubuta game da ikilisiyar Kirista da aka shafa da ruhu. Amma an fahimci waɗannan abubuwan ne sosai sa’ad da Jehobah ya soma yin sha’ani da ikilisiya. (Afis. 3:10) Bai kamata ba ne mu bi misalin mala’iku mu yi ƙoƙari mu bincika “zurfafan al’amuran Allah”?—1 Kor. 2:10.

2:21. Ta wajen yin koyi da Yesu Kristi wanda muke bin misalinsa, ya kamata mu kasance a shirye mu sha wahala ko da hakan zai kai ga mutuwa don mu ɗaukaka ikon mallaka na Jehobah.

5:6, 7. Sa’ad da muka miƙa alhininmu ga Jehobah, zai taimaka mana mu mai da bauta ta gaskiya abin farko a rayuwarmu maimakon mu riƙa damuwa game da gobe.—Mat. 6:33, 34.

‘RANAR UBANGIJI ZA TA ZO’

(2 Bit. 1:1–3:18)

Manzo Bitrus ya rubuta cewa: “Ba a taɓa kawo kowane annabci bisa ga nufin mutum ba: amma mutane suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” Mai da hankali ga kalmar da aka annabta zai iya kāre mu daga “masu-ƙaryan malanta” da kuma mutanen da za su iya ɓata tunaninmu.—2 Bit. 1:21; 2:1-3.

Bitrus ya yi gargaɗi cewa, “cikin kwanaki na ƙarshe masu-ba’a za su zo da ba’a.” Amma “ranar Ubangiji kamar ɓarawo za ta zo.” Bitrus ya kammala wasiƙarsa da shawara mai kyau ga waɗanda suke ‘sauraron ranar, kuma suke marmarin zuwanta ƙwarai.’—2 Bit. 3:3, 10-12.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:19—Wanene “tauraro na assubahi,” a wane lokaci ne ya fito, kuma ta yaya muka san cewa hakan ya riga ya faru? Yesu Kristi ne “tauraro na assubahi” sa’ad da ya zama Sarki na Mulkin Allah. (R. Yoh. 22:16) A shekara ta 1914, Yesu ya fito a gaban dukan halitta a matsayin Sarki Almasihu, yana sanar da fitowar sabuwar rana. Sake kamanni da Yesu ya yi ya nuna ɗaukakarsa da ikonsa na yin Mulki, kuma hakan ya bayyana tabbacin kalmar annabci na Allah. Mai da hankali ga wannan kalmar ya haskaka zukatanmu, kuma hakan ya sa mun fahimci cewa Tauraro na assubahi ya riga ya fito.

3:17—Menene Bitrus yake nufi da “kun rigaya kun sani”? Bitrus yana magana ne game da kasancewa da sanin abubuwan da za su faru a nan gaba, wanda aka ba shi da sauran marubutan Littafi Mai Tsarki ta hurarriyar hanya. Tun da yake wannan ba sani ba ne na har abada, hakan bai sa Kiristoci na farko su sami cikakken bayani ba game da abubuwan da za su faru a nan gaba. Abin da suka sani kawai shi ne abubuwan da za su faru.

Darussa Dominmu:

1:2, 5-7. Ƙari ga taimaka mana mu ƙara “sanin Allah da na Yesu,” ƙoƙartawa sosai wajen koyan halaye kamar su bangaskiya, jimiri, da kuma bauta wa Allah sosai za su hana mu zama ragwaye ko kuwa marasa amfani game da wannan sanin.—2 Bit. 1:8.

1:12-15. Don mu “kahu cikin gaskiya,” muna bukatar tunasarwa a kowane lokaci, kamar waɗanda muke samu a taron ikilisiya, nazarin da muke yi, da kuma karanta Littafi Mai Tsarki.

2:2. Muna bukatar mu mai da hankali kada halinmu ya sa a zagi Jehobah da kuma ƙungiyarsa.—Rom. 2:24.

2:4-9. Domin abubuwan da ya yi a dā, muna da tabbaci cewa “Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba, ya tsare marasa-adalci kuma ƙalƙashin hukunci har zuwa ranar shari’a.”

2:10-13. Ko da yake “maɗaukaka,” wato, dattawa Kiristoci suna da kasawa kuma suna iya yin kuskure a kowane lokaci, kada mu kuskura mu zage su.—Ibran. 13:7, 17.

3:2-4, 12. Mai da hankali sosai ga “zantattuka waɗanda aka faɗi a dā ta bakin annabawa masu-tsarki, da kuma umurnin Ubangiji da Mai-ceto” zai taimaka mana mu riƙa tuna cewa ranar Jehobah ta kusa.

3:11-14. A matsayin waɗanda suke ‘sauraron ranar Allah, kuma muna marmarin zuwanta ƙwarai,’ dole ne mu kasance masu (1) “tsarki” a halinmu, wato, kasancewa da tsabta a jiki, a tunaninmu, a dabi’armu da kuma a ruhaniya; (2) mu kasance da halayen da ke nuna “ibada,” kamar waɗanda suka shafi wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa; (3) halinmu ya kasance “marasa-aibi” a wannan duniyar; (4) mu kasance “marasa-laifi,” yin dukan abubuwa da nufi mai kyau; na (5) mu kasance “cikin salama” da Allah, ’yan’uwanmu Kiristoci, da kuma sauran mutane.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba