Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 87 p. 204-p. 205 par. 3
  • Idin Ketarewa na Karshe da Yesu Ya Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Idin Ketarewa na Karshe da Yesu Ya Yi
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • A Ɗaki A Gidan Sama
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • “Ku Yi Wannan Abin Tunawa da Ni”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Jibin Maraice na Ubangiji—Farilla da Ke Daraja Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Yesu Ya Ciyar da Dubban Mutane
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 87 p. 204-p. 205 par. 3
Yesu ya yi Jibin Maraice na Ubangiji tare da manzanninsa guda goma sha daya

DARASI NA 87

Idin Ƙetarewa na Ƙarshe da Yesu Ya Yi

A kowace shekara, Yahudawa suna yin Idin Ƙetarewa a ranar 14 ga Nisan. Hakan yana taimaka musu su tuna yadda Jehobah ya cece su daga zaman bauta a ƙasar Masar kuma ya kawo su Ƙasar Alkawari. A shekara ta 33, Yesu da manzanninsa sun yi Idin Ƙetarewa a wani ɗaki da ke gidan sama a Urushalima. Bayan sun gama cin abincin, sai Yesu ya ce musu: ‘Ɗaya daga cikinku zai ci amana ta.’ Abin ya ba manzannin mamaki sosai, sai suka tambaye shi: ‘Wane ne mutumin?’ Yesu ya ce musu: ‘Mutumin shi ne wanda zan miƙa masa wannan gurasan.’ Sai ya miƙa wa Yahuda Iskariyoti gurasan. Nan take, Yahuda ya fita daga ɗakin.

Sai Yesu ya yi addu’a, ya karya gurasar kuma ya miƙa wa manzanninsa da suka rage. Ya ce: ‘Ku ci wannan gurasar. Tana wakiltar jikina wanda zan bayar domin ku.’ Ya kuma yi addu’a a kan ruwan inabin, sai ya miƙa wa manzanninsa. Ya ce: ‘Ku sha wannan ruwan inabin. Yana wakiltar jinina wanda zan bayar don gafarar zunubai. Na yi muku alkawari cewa za ku yi sarauta tare da ni a sama. Ku riƙa yin haka kowace shekara don tunawa da ni.’ Har a yau, mabiyan Yesu suna taro a wannan yammar kowace shekara. Ana kiran taron Jibin Maraice na Ubangiji.

Bayan sun gama cin abincin, sai sauran manzannin suka yi gardama a kan wanda ya fi matsayi a cikinsu. Amma Yesu ya ce musu: ‘Wanda ya fi matsayi a cikinku shi ne wanda yake ɗaukan kansa mafi ƙanƙanta.

‘Ku abokaina ne. Shi ya sa nake gaya muku dukan abin da Ubana yake so ku sani. Nan ba da jimawa ba, zan koma sama wurin Ubana. Amma ku kuna nan. Idan kuna ƙaunar junanku, hakan zai sa a san cewa ku mabiyana ne. Dole ku ƙaunaci junanku yadda ni ma na ƙaunace ku.’

A ƙarshe, sai Yesu ya yi addu’a. Ya ce Jehobah ya kula da dukan almajiransa kuma ya taimaka musu su kasance da haɗin kai da salama. Ya kuma yi addu’a domin a tsarkake sunan Jehobah. Sa’an nan Yesu da manzanninsa suka yi waƙar yabo ga Jehobah. Bayan haka, sai suka fita waje. Lokacin da za a kama Yesu ya kusa.

“Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi ya ba ku mulkin.”​—Luka 12:32

Tambayoyi: Wane alkawari ne Yesu ya yi wa manzanninsa? Wane darasi mai muhimmanci ne Yesu ya koya wa manzanninsa sa’ad da suke idi na ƙarshe?

Matta 26:​20-30; Luka 22:​14-26; Yohanna 13:​1, 2, 26, 30, 34, 35; 15:​12-19; 17:​3-26

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba