Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 11/1 p. 30
  • Majami’un Mulki Suna Buɗe Domin Kowa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Majami’un Mulki Suna Buɗe Domin Kowa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Makamantan Littattafai
  • Wannan Wurin Ne Muke Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Menene Majami’ar Mulki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 11/1 p. 30

Rahoto Daga Masu Shelar Mulki

Majami’un Mulki Suna Buɗe Domin Kowa

SA’AD da yake koyar da almajiransa domin hidima ga jama’a, Yesu ya ƙarfafa su su “yi shelarsa a bisa soraye.” (Matta 10:27) Hakika, za su yi hidimarsu ta Kirista a fili, a gaban jama’a. Domin wannan kashedin, ayyukan Shaidun Jehovah ma ana yinsu a fili. Wannan sau da yawa yana sa Shaidun su ci nasara bisa adawa kuma a san da su.

Ko da yake taron ikilisiya na Shaidun Jehovah a buɗe yake ga jama’a, ƙiyayya da ake musu ya sa wasu mutane suke jinkirin shiga Majami’ar Mulki. Wannan haka yake a Finland. Wasu kuma ba sa son zuwa sababbin wurare. Sa’ad da aka gina sabuwar Majami’ar Mulki ko kuma aka sabonta wadda ake da ita dā sai a yi bikin buɗe ta. Ana ƙoƙari na musamman domin a gayyaci maƙwabta su ziyarci Majami’ar Mulki domin su fahimci ayyukan Shaidun Jehovah.

A wani wuri, Shaidun suka shirya kamfen na jarida a ranar da suke bikin buɗe sabuwar Majami’ar Mulkinsu. Shaidu biyu suka sadu da wani tsoho da ya ce yana jin daɗin karatun jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! ’Yan’uwa suka gaya masa game da bikin kuma suka ce za su kai shi Majami’ar Mulkin. Mutumin ya ce yana shirye ya bi su. Matarsa bayan ta saurari hirarsu, ta ce, “Kada ku tafi ku bar ni!”

Da shigarsa Majami’ar Mulkin, mutumin ya yi dube-dube ya ce: “Wannan ba baƙin fenti ba ne sam sam. A’a, wannan yana da kyau yana da haske. An gaya mini cewa Majami’ar Mulkin za ta yi duhu!” Mata da mijin suka zauna na ɗan lokaci sai suka karɓi wasu littattafai da aka baza.

Wata ikilisiya tana so ta sanar da bikin buɗe Majami’ar Mulkinta a ranar keɓe ta a wata jarida. Da aka sanar da shi game da wannan, babban editan ya ba da shawara a rubuta talifi game da wannan. ’Yan’uwan suka yarda, ba da daɗewa ba bayan haka, talifi rabin shafi ya bayyana a jaridar, ya bayyana bikin da kuma ayyukan ikilisiyar Shaidun Jehovah.

Bayan da aka buga talifin, wata tsohuwa Mashaidiya ta sadu da wata maƙwabciya da ta ce ma ta: “Da akwai wani talifi mai kyau game da Shaidun Jehovah a jarida yau!” ’Yar’uwar ta yi ma ta wa’azi kuma ta ba ta mujallar nan mai suna Jehovah Witnesses in the Twentieth Century.

Ƙari ga warware wasu ra’ayoyi game da Shaidun Jehovah, irin waɗannan tsarin game da biki da kuma tsarin ayyukan na bikin keɓe Majami’ar Mulki sun motsa masu shela ta wajen ƙarfafa su su gayyaci mutane su halarci taro. Hakika, wasu ƙasashe, haɗe da Finland, mutane suna koyon cewa Majami’ar Mulki na Shaidun Jehovah suna buɗe ga kowa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba