Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 11/1 p. 32
  • Dukanmu Muna Bukatar Yabo

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dukanmu Muna Bukatar Yabo
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 11/1 p. 32

Dukanmu Muna Bukatar Yabo

RANA ce ta farin ciki ga ’yar yarinyar. Ko da yake ta bukaci a yi ma ta faɗa a wasu lokatai, a wannan ranar, ta nuna ladabi ƙwarai. Cikin dare, bayan yarinyar ta kwanta mamarta ta ji ta tana kuka. Da aka tambaye ta me ya sa take kuka, ta ce: “Ban yi abin kirki ba ne yau?”

Wannan tambayar ta soki uwar kamar takobi. Tana da sauƙin yi wa ’yarta faɗa. Amma yanzu, bayan ta lura cewa ’yarta ta yi ƙoƙari ƙwarai ta yi ladabi, uwar ta ƙyale ta ba ta furta ko kalma ɗaya ba ta yabo.

Ba yara ƙanana ba ne kawai suke bukatar yabo da tabbaci. Dukanmu muna bukatar haka—kamar yadda muke bukatar a yi mana faɗa da kuma gyara.

Yaya kake ji sa’ad da aka yaba maka? Ba ta daɗaɗa maka rai kuma ta faranta maka zuciya? Wataƙila muna jin cewa wani ya lura da abin da muka yi, wani ya damu da abin da muka yi. Tana tabbatar mana cewa abin da muka yi ya yi kyau, kuma tana motsa mu mu yi ƙoƙari a nan gaba. Ba abin mamaki ba ne cewa yabo na gaske yana jawo mu kusa da mutumin da ya ba da lokaci ya faɗi abin da yake da ban ƙarfafa.—Misalai 15:23.

Yesu Kristi ya fahimta cewa yana da kyau a yaba wa mutane. A cikin almara ta talanti, ubangiji (da ke zaman Yesu kansa) ya yaba wa bayi biyu masu aminci, ya ce musu: “Madalla, kai bawan kirki mai-aminci!” Lallai yana daɗaɗawa! Ko da yake ba su cim ma abu iri ɗaya ba kuma ba su kasance ɗaya ba wajen ilimi, an yaba musu daidai wa daida.—Matta 25:19-23.

Saboda haka, ya kamata mu tuna da mamar ’yar yarinyar nan. Bai kamata mu jira har sai wasu suna hawaye ba kafin mu yaba musu. Maimakon haka, za mu iya neman zarafi mu yaba wa wasu. Hakika, muna da kyakkyawan dalili na yaba wa mutane a kowanne zarafi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba