Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/1 p. 10
  • Menene Majami’ar Mulki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Majami’ar Mulki?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Wannan Wurin Ne Muke Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Me Ya Sa Ake Gina Majami’un Mulki Kuma Yaya Ake Yin Ginin?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/1 p. 10

Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .

Menene Majami’ar Mulki?

▪ Majami’ar Mulki wajen bauta ne da Shaidun Jehobah suke amfani da shi don harkokin addininsu. Akwai dubban Majami’un Mulki da ake amfani da su a dukan faɗin duniya. A kowane mako, fiye da ikilisiyoyi 105,000 na Shaidun Jehobah ne suke yin taro a waɗannan majami’un.

Kowanne Majami’ar Mulki yana da babban ɗakin taro inda ake nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ake ba da jawabai. A yawancin babban ɗakin taron, akwai dakalin magana inda ake gudanar da taron. Akwai wurin zama na aƙalla mutane 100 zuwa 300 a majami’ar. Wasu Majami’ar Mulkin suna da ƙarin ɗakuna ɗaya ko biyu, ofishi, da kuma ɗan ƙaramin ma’adanar littattafai inda ake ajiye littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da na bincike da kowa a ikilisiyar zai iya yin amfani da su.

A Majami’ar Mulki, ba za ka ga kayayyakin addinin Kiristendam ba, kamar su siffofi da hotuna. Babu bagadi, gumaka, ko kuma giciye. Me ya sa? Shaidun Jehobah sun gaskata cewa yin amfani da irin waɗannan abubuwan sun saɓa wa umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na “ku guje ma bautar gumaka.” (1 Korintiyawa 10:14; Yohanna 4:24) An yi wa coci da haikalai da yawa kwalliya masu tsada. Akasin haka, an tsara Majami’un Mulki ne don a yi amfani da ko’ina a cikinta kuma ta kasance mai sauƙi. Ana mai da hankali ne ga koyarwar Littafi Mai Tsarki da ake yi a wurin ba ga fasalin ginin ba.

Me ya sa ake kiranta Majami’ar Mulki? Tarurrukan da ake yi a Majami’ar Mulki yana mai da hankali ainun ga koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma ainihin saƙonsa game da “mulkin Allah” ne, jigon hidimar Yesu. (Luka 4:43) Saboda haka, sunan nan Majami’ar Mulki wanda aka ƙirƙiro a cikin shekara ta 1930, ya bayyana manufar wannan ginin, wato, faɗaɗa bauta ta gaskiya da kuma cibiyar yin wa’azin ‘bishara ta mulki.’ (Matta 24:14) Saboda haka, ba a yin amfani da Majami’un Mulki don shaƙatawa ko sana’a. Ana samo kuɗaɗen gini, gyare-gyare da kuma na ayyukan dukan duniya ta hanyar gudummawa. Ba a wucewa da faranti don jama’a su saka kuɗi a cikinta. Maimakon hakan, akwai akwatin da aka ajiye a ɓangare ɗaya don wanda yake da niyar ba da kyauta.

Ana amfani da Majami’un Mulki domin manufa ɗaya a dukan duniya, amma fasalinsu da girmansu sun bambanta. Fasalin yana bambanta bisa ga irin kayayyakin gini da ke yankin, yanayin wurin, da kuma nauyin aljihun Shaidun Jehobah da suke wurin. Ana yin wasu ginin da bulo, katako, da duwatsu. Wasu kuma ba su da bango, wasu suna da bangon itatuwan gora da rufin baibaya.

Ana gayyatar baƙi a koyaushe su halarci taro a kowane Majami’ar Mulki. (Ibraniyawa 10:25) Hakika, ana yin taro don jama’a a kowane mako, wanda ke mai da hankali ga jigon da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki da ke shafar waɗanda suke halartar taro kullum da kuma baƙi. Zai dace ka ziyarci Majami’ar Mulkin da ke yankinka.

[Hoton da ke shafi na 10]

Malawi, Afirka

[Hotuna da ke shafi na 10]

Ingila, Britaniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba