Ka Koyi Biyayya Yayin Da Ƙarshe Ya Matso Kusa
“Gareshi [Shiloh] kuma biyayyar al’ummai za ta nufa.”—FARAWA 49:10.
1. (a) A dā, menene biyayya ga Jehovah sau da yawa yake nufi? (b) Wane annabci ne game da biyayya Yakubu ya yi?
BIYAYYA ga Jehovah sau da yawa na nufin biyayya ga wakilansa. Waɗannan sun haɗa da mala’iku, ubanni, alƙalai, firistoci, annabawa, da sarakuna. Har an kira kursiyin sarakunan Isra’ila kursiyin Jehovah. (1 Labarbaru 29:23) Amma abin baƙin ciki, sarakunan Isra’ila da yawa sun yi wa Allah rashin biyayya, sun jawo wa kansu da talakawansu masifa. Amma Jehovah bai bar mutanensa masu aminci babu bege ba; ya ƙarfafa su da alkawari zai naɗa Sarki da ba shi da lalata, wanda adalai za su yi farin cikin yin masa biyayya. (Ishaya 9:6, 7) Da yake so ya mutu Yakubu uban iyali ya yi annabci game da wannan sarki na nan gaba, yana cewa: “Kandirin ba za ya rabu da Yahuda ba, Sandar mai-mulki kuma daga tsakanin sawayensa, har Shiloh ya zo; zuwa gareshi kuma biyayyar al’ummai za ta nufa.”—Farawa 49:10.
2. Menene ma’anar “Shiloh,” kuma menene sarautarsa ta ƙunsa?
2 “Shiloh” kalma ce ta Ibrananci da ke nufin “Mai shi.” Hakika, Shiloh zai gāji cikakken iko na sarauta, da kandirin ya alamta, da ikon mulki, da sandan mulki ke wakilta. Ban da haka, sarautarsa ba ga ’ya’yan Yakubu kawai za ta tsaya ba amma ta haɗa da dukan “al’ummai.” Wannan ya yi daidai da alkawarin Jehovah ga Ibrahim: “Tsatsonka kuma za shi gāji ƙofar magabtansa; cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka.” (Farawa 22:17, 18) Jehovah ya tabbatar da wannan ‘zuriya’ a shekara ta 29 A.Z., sa’ad da ya shafe Yesu na Nazarat da ruhu mai tsarki.—Luka 3:21-23, 34; Galatiyawa 3:16.
Mulkin Yesu na Farko
3. Wace sarauta ce Yesu ya samu sa’ad da ya hau sama?
3 Sa’ad da Yesu ya hau sama, bai soma sarauta nan da nan ba bisa mutanen duniya. (Zabura 110:1) Amma, ya samu “mulkin” da talakawa da suke masa biyayya. Manzo Bulus ya nuna wannan mulkin sa’ad da ya rubuta: “[Allah] wanda ya tsame mu [shafaffu Kiristoci] daga cikin ikon duhu, ya maishe mu zuwa cikin mulkin Ɗa na ƙaunarsa.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Kolossiyawa 1:13) Wannan ceton ya soma a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka zubo wa mabiyan Yesu masu aminci ruhu mai tsarki.—Ayukan Manzanni 2:1-4; 1 Bitrus 2:9.
4. A waɗanne hanyoyi almajiran Yesu na farko suka nuna biyayyarsu, kuma yaya Yesu ya nuna cewa su rukuni ne?
4 Da yake su “manzanni ne madadin Kristi,” almajirai shafaffu cikin biyayya suka soma tare wasu da za su zama “abokan ’yangaranci” a wannan mulki na ruhaniya. (2 Korinthiyawa 5:20; Afisawa 2:19; Ayukan Manzanni 1:8) Ƙari ga haka, waɗannan za su “zama cikakku cikin hankali ɗaya da shawara ɗaya” don su more naɗa Sarkinsu Yesu Kristi. (1 Korinthiyawa 1:10) A rukuni, su ne “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ko kuma ajin wakili mai aminci.—Matta 24:45; Luka 12:42.
Albarka don Yi wa “Wakilin” Allah Biyayya
5. Daga lokacin dā, yaya Jehovah yake koya wa mutanensa?
5 Jehovah koyaushe yana tanadin malamai wa mutanensa. Alal misali, bayan Yahudawa suka dawo daga Babila, Ezra da wasu mutane da suka cancanta ba kawai sun karanta Dokar Allah wa mutanen ba, sun kuma ba da “fassarar” dokar, ‘suna ba da ma’anarsa har da suka fahimta’ Kalmar Allah.—Nehemiah 8:8.
6, 7. Ta yaya ajin bawa ya ba da abinci na ruhaniya a kan lokaci ta Hukumar Mulki, me ya sa biyayya ga ajin bawa ta dace?
6 A ƙarni na farko, sa’ad da batun kaciya ya taso a shekara ta 49 A.Z., hukumar mulki ta wannan ajin bawa na farko suka yi addu’a don ja-gora sa’ad da suke bincika batun, suka zo ga kammala da ke bisa Nassi. Lokacin da suka sanar da shawararsu ta wajen wasiƙa, ikilisiyoyin suka yi biyayya da ja-gora da aka bayar kuma suka more albarkar Allah mai yawa. (Ayukan Manzanni 15:6-15, 22-29; 16:4, 5) Hakanan ma a zamani, bawa mai aminci ta Hukumar Mulki sun yi bayani a kan batutuwa masu muhimmanci kamar su tsakatsaki na Kirista, tsarkakar jini, da shan ƙwayoyi da taba. (Ishaya 2:4; Ayukan Manzanni 21:25; 2 Korinthiyawa 7:1) Jehovah ya albarkaci mutanensa don biyayyarsu ga Kalmarsa da bawan nan mai aminci.
7 Ta yin biyayya da ajin bawa, mutanen Allah sun nuna suna biyayya ga Ubangijinsu, Yesu Kristi. Irin wannan biyayya ta fi muhimmanci a zamani domin ikon Yesu da ya ƙaru, yadda aka annabta cikin annabci da Yakubu ya yi lokacin da yake son ya mutu.
Shiloh Ya Zama Sarkin da Ya Dace na Duniya
8. Yaushe kuma ta yaya ikon Kristi ya ƙaru?
8 Annabcin Yakubu ya annabta cewa Shiloh zai ba da umurnin “biyayyar al’ummai.” Hakika, sarautar Kristi zai miƙe fiye da ta Isra’ila ta ruhaniya. Menene za ta ƙunsa? Ru’ya ta Yohanna 11:15 ta amsa: “Mulkin duniya ya zama na Ubangijinmu, da na Kristinsa: za ya yi mulki kuma har zuwa zamanun zamanai.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Yesu ya samu wannan iko a ƙarshen “wokatai guda bakwai” na annabci—“zamanan Al’ummai”—a shekara ta 1914.a (Daniel 4:16, 17; Luka 21:24) A wannan shekara, “bayyanuwar” Kristi marar ganuwa na Sarki Almasihu ya soma, yadda lokacinsa ya yi ya “ci sarauta a tsakiyar maƙiyan[sa].”—Matta 24:39; Zabura 110:2.
9. Menene Yesu ya yi sa’ad da ya samu Mulkinsa, kuma yaya wannan ya shafi ’yan Adam, musamman almajiransa?
9 Abin da Yesu ya yi da farko bayan ya samu ikon sarauta shi ne ya jefo wanda aka fi sani da rashin biyayya—Shaiɗan—tare da aljanunsa “duniya.” Tun lokacin, waɗannan miyagun ruhohi sun haddasa masifu ga ’yan Adam, ban da gabatar da mahalli da ke sa biyayya ga Jehovah ke wuya sosai. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-12; 2 Timothawus 3:1-5) Hakika, ainihin waɗanda Shaiɗan yake fako a wannan yaƙi na ruhaniya sun haɗa da shafaffu na Jehovah, “waɗanda su ke kiyaye da dokokin Allah, suna riƙe da shaidar Yesu,” tare da abokan tarayyarsu “waɗansu tumaki.”—Ru’ya ta Yohanna 12:17; Yohanna 10:16.
10. Cikar waɗanne annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki suka tabbatar da rashin nasarar yaƙin Shaiɗan da Kiristoci na gaskiya?
10 Shaiɗan ba zai yi nasara ba, domin wannan “ranar Ubangiji” ce, kuma ba abin da zai hana Yesu “yin nasara.” (Ru’ya ta Yohanna 1:10; 6:2) Alal misali, zai tabbata cewa an hatimce sauran 144,000 na Isra’ila ta ruhaniya. Zai kuma kāre “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa, daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:1-4, 9, 14-16) Amma ba kamar shafaffu abokan tarayyarsu ba, waɗannan za su zama talakawan Yesu masu biyayya a duniya. (Daniel 7:13, 14) Bayyanuwarsu a duniya yau ya riga ya ba da tabbaci cewa Shiloh ne Sarki bisa “Mulkin duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 11:15.
Yanzu Lokaci ne na “Biyayya da Bishara”
11, 12. (a) Su waye za su tsira wa ƙarshen wannan zamani? (b) Wane hali ne waɗanda suke ɗaukan “ruhun duniya” suke koya?
11 Dukan waɗanda suke son rai madawammi dole su koyi biyayya, don Littafi Mai Tsarki ya ce dalla-dalla “waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu,” ba za su tsira a ranar ramako na Allah ba. (2 Tassalunikawa 1:8) Amma wannan mugun yanayi da halin tawaye ga dokoki da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ke sa biyayya ga bishara take da wuya.
12 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan halin tawaye ga Allah cewa “ruhun duniya” ne. (1 Korinthiyawa 2:12) Da yake bayyana yadda ya shafi mutane, manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci na ƙarni na farko a Afisus, cewa: “Ku ke tafiya a dā bisa ga zamanin wannan duniya, ƙarƙashin sarkin ikon sararin sama, ruhun da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara; a cikinsu kuwa mu duka muna zamanmu a dā a cikin sha’awoyin jikinmu, muna bin gurin jiki da na tunani; bisa ga tabi’a kuma ’ya’yan fushi ne, kamar sauran mutane.”—Afisawa 2:2, 3.
13. Ta yaya Kiristoci za su yi nasara a ƙi da ruhun duniya, da wane amfani mai kyau?
13 Abin farin ciki, Kiristoci na Afisus ba su ci gaba da zama bayi na ruhun rashin biyayya ba. Maimako, sun zama ’ya’yan Allah masu biyayya ta miƙa kai ga ruhunsa kuma suna samun amfani mai kyau a yalwace. (Galatiyawa 5:22, 23) Hakanan ma yau, ruhun Allah—iko mafi ƙarfi a duniya—na taimakon mutane miliyoyi su yi biyayya ga Jehovah, da amfani cewa za su samu “tabbatawar bege har ƙarshe.”—Ibraniyawa 6:11; Zechariah 4:6.
14. Ta yaya Yesu ya sa Kiristoci da suke zama a kwanaki na ƙarshe su kasance a shirye ga takamammun abubuwa da za su gwada biyayyarsu?
14 Ka tuna cewa, muna da goyon bayan Shiloh, wanda tare da Ubansa ba za su bar magabta—aljanu ko ’yan Adam—su gwada biyayyarmu fiye da yadda za mu jimre ba. (1 Korinthiyawa 10:13) Hakika, don ya taimake mu a yaƙi na ruhaniya, Yesu ya kwatanta takamammun matsaloli da za mu fuskanta a wannan kwanaki na ƙarshe. Ya yi haka ta wajen wasiƙu bakwai, wanda ya ba da a wahayi ga manzo Yohanna. (Ru’ya ta Yohanna 1:10, 11) Babu shakka, suna ɗauke da gargaɗi na musamman ga Kiristoci a lokacin, amma ainihinsu ga “ranar Ubangiji” ce, tun shekara ta 1914. Saboda haka, ya dace mu mai da hankali ga waɗannan saƙonni!b
Ka Guji Rashin So, Lalata, da Son Abin Duniya
15. Me ya sa za mu guji matsalar da ta shafi ikilisiya a Afisus, kuma ta yaya za mu yi haka? (2 Bitrus 1:5-8)
15 Wasiƙar Yesu ta farko zuwa ga ikilisiyar da ke Afisus ce. Bayan ya yaba wa ikilisiyar don jimirinta, Yesu ya ce: “Amma ina da wannan game da kai, da ka bar ƙaunarka ta fari.” (Ru’ya ta Yohanna 2:1-4) Yau, wasu Kiristoci da a dā masu himma ne sun bar ƙaunar da suke da ita ga Allah. Irin wannan rashi zai raunana dangantakar mutum da Allah kuma dole a gyara babu ɓata lokaci. Ta yaya za a sake ƙarfafa irin wannan ƙauna? Ta nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, halartan taro, addu’a, da yin bimbini. (1 Yohanna 5:3) Hakika, wannan na bukatar “ƙara bada ƙoƙari,” amma kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu. (2 Bitrus 1:5-8) Idan ka bincika kanka sosai ka ga cewa ƙaunarka ta yi sanyi, ka gyara yanayin babu ɓata lokaci, a yin biyayya da gargaɗin Yesu: “Ka tuna fa daga inda ka fāɗi, ka tuba kuma, ka yi ayyuka na fari.”—Ru’ya ta Yohanna 2:5.
16. Wace mummunar rinjaya ga ruhaniya ta kasance a ikilisiyoyin Birgamus da Thyatira, me ya sa maganar da Yesu ya yi musu ta dace a yau?
16 An yaba wa Kiristoci a Birgamos da Thyatira don amincinsu, jimiri, da himma. (Ru’ya ta Yohanna 2:12, 13, 18, 19) Duk da haka, wasu da suke nuna mugun hali na Balaam da Jezebel sun rinjaye su, waɗanda ta wajen lalata da bautar Ba’al suka lalata Isra’ila ta dā. (Litafin Lissafi 31:16; 1 Sarakuna 16:30, 31; Ru’ya ta Yohanna 2:14, 16, 20-23) Lokacinmu kuma fa—“ranar Ubangiji”? Da akwai irin wannan mugun tasiri? Hakika, domin lalata ce ainihin dalili na yankan zumunci tsakanin mutanen Allah. Saboda haka, yana da muhimmanci mu guji cuɗanya da dukan mutane—a ciki da waje da ikilisiya—da suke da rinjaya ta lalata! (1 Korinthiyawa 5:9-11; 15:33) Waɗanda suke son su zama talakawa masu biyayya na Shiloh za su kuma guji nishaɗi da hotunan tsirarun mutane da aka buga da kuma Intane.—Amos 5:15; Matta 5:28, 29.
17. Ta yaya ra’ayi da halin waɗanda suke cikin Sardisu da Lawudikiya yake idan aka gwada da ra’ayin Yesu ga yanayinsu na ruhaniya?
17 Ban da mutane kalilan, ba a yaba wa ikilisiya da ke Sardisu ba sam. Tana da “suna,” ko ta bayyana kamar tana da rai, amma tana ƙin abubuwa na ruhaniya sosai da Yesu ya ce ‘matacciya’ ce. Biyayya da bishara suna yi ne kawai. Lallai yanayin mummuna ne! (Ru’ya ta Yohanna 3:1-3) Ikilisiya da ke Lawudikiya ita ma tana cikin irin wannan yanayin. Tana fahariya da arziki, cewa, “Na sami dukiya,” amma ga Kristi “abin tausayi, matalauci, makaho, tsirara” ne.—Ru’ya ta Yohanna 3:14-17.
18. Ta yaya mutum zai guje zama marar ƙwazo a gaban Allah?
18 A yau, wasu Kiristoci da dā masu aminci ne sun fāɗa cikin irin wannan yanayi na rashin biyayya. Wataƙila sun bar ruhun duniya ya rage yadda suke da azancin gaggawa a rayuwarsu, da haka sun kasance da rashin ƙwazo a ruhaniya game da nazarin Littafi Mai Tsarki, addu’a, taron Kirista, da kuma hidima. (2 Bitrus 3:3, 4, 11, 12) Yana da muhimmanci irin waɗannan su yi wa Kristi biyayya ta yin ajiyar arziki na ruhaniya don nan gaba—hakika, su “sayi zinariya daga wurin [Kristi] zinariya gyartaciya ta wurin wuta”! (Ru’ya ta Yohanna 3:18) Irin wannan tabbataciyar dukiya ta ƙunshi ‘wadata cikin kyawawan ayyuka, da niyyar bayarwa.’ Ta jarinta a waɗannan dukiya mai tamani, muna ‘ajiye wa kanmu tushe mai-kyau domin wokaci mai-zuwa, da za mu ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.’—1 Timothawus 6:17-19.
An Yaba Musu don Biyayyarsu
19. Wane yabawa da gargaɗi Yesu ya yi wa Kiristoci a Samiruna da Filadalfiya?
19 Ikilisiyoyi a Samiruna da Filadalfiya sun kasance na farko a misalan biyayya, gama wasiƙun Yesu zuwa gare su ba su da horo. Game da waɗanda suke Samiruna ya ce: “Na san ƙuncinka da talaucinka amma mawadaci ne kai.” (Ru’ya ta Yohanna 2:9) Lallai sun bambanta da waɗanda suke Lawudikiya da suke fahariya a wadata ta duniya da a gaske talakawa ne su! Hakika, Iblis ba ya farin cikin ya ga wanda yake da aminci da biyayya ga Kristi. Saboda haka, Yesu ya yi kashedi: “Kada ka ji tsoron wahala da za ka sha: ga shi, Shaiɗan yana shiri ya jefa waɗansu daga cikinku a kurkuku, domin a gwada ku; kwana goma kuwa za ku sha ƙunci. Ka yi aminci har mutuwa, ni ma in ba ka rawanin rai.” (Ru’ya ta Yohanna 2:10) Hakanan ma, Yesu ya yaba wa waɗanda suke Filadalfiya, cewa: “Ka kiyaye maganata [ko, ka yi mini biyayya] ba ka yi musun sunana kuma. Ina zuwa da sauri: ka riƙe abin da ka ke da shi da kyau, domin kada kowa shi amshi rawaninka.”—Ru’ya ta Yohanna 3:8, 11.
20. Ta yaya mutane miliyoyi a yau suka yi biyayya da maganar Yesu, duk da wane yanayi?
20 A “ranar Ubangiji,” somawa a shekara ta 1914, amintattu raguwar da abokan tarayyarsu waɗansu tumaki, da yanzu miliyoyi ne, sun kiyaye maganar Yesu ta sa hannu a hidima da himma kuma ta riƙe amincinsu. Kamar ’yan’uwansu na ƙarni na farko, wasu sun sha wahala don biyayyarsu ga Kristi, har an jefa su cikin kurkuku da sansani. Wasu sun yi biyayyar maganar Yesu ta riƙe ‘idonsu sosai,’ ko da dukiya da haɗama sun gewaye su. (Matta 6:22, 23) Hakika, a kowane mahalli da yanayi, Kiristoci na gaskiya, ta wurin biyayyarsu sun ci gaba da faranta zuciyar Jehovah.—Misalai 27:11.
21. (a) Wane hakki ne na ruhaniya ajin bawa zai ci gaba da cikawa? (b) Ta yaya za mu nuna cewa da gaske muna son mu yi wa Shiloh biyayya?
21 Yayin da muka yi kusa da ƙunci mai girma, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya ƙudiri aniya ba zai fasa biyayya ga Ubangiji, Kristi ba. Wannan ya haɗa da shirya abinci na ruhaniya a kan lokaci wa iyalin Allah. Saboda haka, mu ci gaba da godiya ga tsarin ƙungiya mai ban al’ajabi na Jehovah da abin da take bayarwa. A wannan hanyar, muna biyayya da Shiloh, wanda zai saka wa dukan talakawansa masu biyayya da rai madawwami.—Matta 24:45-47; 25:40; Yohanna 5:22-24.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani a kan “wokatai guda bakwai,” ka duba babi 10 na littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, da Shaidun Jehovah suka buga.
b Don bayani na dalla-dalla na dukan wasiƙu bakwai, sai ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand!, (Turanci) da Shaidun Jehovah suka buga, somawa a shafi na 33.
Ka Tuna?
• Wane aiki Yesu zai yi yadda Yakubu ya annabta a annabcinsa sa’ad da ya kusa mutuwa?
• Ta yaya muka san cewa Yesu shi ne Shiloh, kuma wane hali za mu guje wa?
• Wane gargaɗi da ya dace da zamaninmu yake ƙunshe cikin wasiƙu bakwai da aka aika wa ikilisiyoyi na Ru’ya ta Yohanna?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu yi koyi da waɗanda suke cikin ikilisiyoyi a Samiruna da Filadalfiya na dā?
[Hotuna a shafi na 26]
Jehovah ya albarkaci mutanensa don sun yi wa ‘wakilai’ masu aminci biyayya
[Hoto a shafi na 27]
Rinjayar Shaiɗan ta sa yi wa Allah biyayya ke da wuya
[Hotuna a shafi na 29]
Dangantaka mai ƙarfi da Jehovah na taimakonmu mu yi masa biyayya