Ya Kamata Ka Kasance Mai Rashin Damuwa?
YAWANCIN mutane wataƙila za su ga cewa yabo ne a ce wa mutum ba ya damuwa, mai lumana, ba shi da saurin fushi, yana da sauƙin hali. Amma akwai wani fanni na kasance da rashin damuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ɓaraicin marasa-wayo za ya kashe kansu.” (Misalai 1:32) Menene wannan yake nufi?
Wasu fassaran Littafi Mai Tsarki sun fassara kalmar asali ta Ibrananci da furci kamar su “rashin damuwa” (American Standard Version), “gamsuwa da kai” (The New American Bible), da “rashin kulawa.” (The New English Bible) A wannan azanci, rashin damuwa an haɗa da ragonci da rashin kulawa da haka ya zama shashanci ko wauta.
A ƙarni na farko, Kiristoci a ikilisiyar Lawudikiya ba su sani ba ko ba su damu ba game da kasawarsu na ruhaniya. Cikin rashin damuwa sun yi fahariya cewa ba su “bukaci kome ba.” Yesu Kristi ya yi musu gyara, ya ce su farfaɗo da himmarsu na Kirista.—Ru’ya ta Yohanna 3:14-19.
Mutane na zamanin Nuhu su ma suna da halin rashin damuwa. Sun shagala cikin abin duniya na rayuwa “suna ci, suna sha, suna aure, suna auraswa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, . . . ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.” Yesu ya daɗa cewa: “Hakanan kuma bayyanuwar Ɗan mutum za ta zama.”—Matta 24:37-39.
Cikan annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa muna cikin lokacin “bayyanuwar Ɗan mutum,” Yesu Kristi. Kada mu zama waɗanda ba sa damuwa, ba sa kula, masu koshin kai—rashin damuwa yadda bai kamata ba.—Luka 21:29-36.