Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 3/1 pp. 14-18
  • Masu Koyar Da Kalmar Allah Shiryayyu Ne Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Masu Koyar Da Kalmar Allah Shiryayyu Ne Sosai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kalmar Jehovah Tana Sa Mu Ƙware
  • Ruhun Jehovah Yana Sa Mu Ƙware
  • Ƙungiyar Jehovah Tana Sa Mu Ƙware
  • Na Ƙware na Yi Wa’azi Kuwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Su Wanene Masu Hidima Na Allah A Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Jehobah Yana Yi wa Kungiyarsa Ja-goranci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 3/1 pp. 14-18

Masu Koyar Da Kalmar Allah Shiryayyu Ne Sosai

“Allah . . . ya kuma isarda mu muna masu-hidiman.”—2 KORINTHIYAWA 3:5, 6.

1, 2. Waɗanne ƙoƙarce-ƙoƙarce aka yi a yin wa’azi, amma me ya sa sau da yawa suke kasawa?

YAYA za ka ji idan an ba ka aiki da ba ka ƙware a yi ba? Ka yi tunani: An shimfiɗa maka kayan aiki da ka ke bukata a gabanka. Amma ba ka san yadda za ka yi aikin ba. Mafi muni kuma, ana bukatar wannan aikin nan da nan. Mutane sun dangana a gare ka. Lalle wannan abin baƙin ciki ne!

2 Irin wannan bala’i ba kawai saƙar zuci ba ne. Yi la’akari da wani misali. Wasu lokatai cocin Kiristendam sukan yi ƙoƙari su tsara hidima ta ƙofa ƙofa kuma su yi ta. Sau da yawa, irin ƙoƙarce-ƙoƙarcen nan yakan lalace, yana lalacewa cikin ’yan makonni ko watanni. Me ya sa? Kiristendam ba ta taimaki mabiyanta su ƙware ba domin aikin. Limaman ma ba ƙwararru ba ne a wannan aikin wa’azi, duk da shekaru na karatu a makarantu da kuma makarantun tauhidi. Me ya sa za mu faɗi haka?

3. A 2 Korinthiyawa 3:5, 6, wane furci aka yi amfani da shi sau uku, kuma me yake nufi?

3 Kalmar Allah ta bayyana abin da ke isar da mai wa’azi na gaske na bisharar Kirista. An hure manzo Bulus ya rubuta: “Ba cewa mu bisa kanmu mun isa mu maida komi kamar daga kanmu ne; amma isarmu daga Allah ce; wanda ya kuma isarda mu muna masu-hidiman.” (2 Korinthiyawa 3:5, 6) Ka lura da furci da aka yi amfani da shi sau uku a nan—‘isa.’ Menene yake nufi? Vine’s Expository Dictionary of Biblical Words ya ce: “Idan ana maganar abubuwa [wannan kalmar Helenanci na asali na nufin ‘isa’ . . . ; idan ana maganar mutane, tana nufin ‘ƙwarewa,’ ‘cancanta.’ ” Saboda haka, wanda ya ‘isa’ ya ƙware kuma ya cancanta a ba shi aiki. Hakika, masu hidimar bishara na gaske sun ƙware su yi wannan aikin. Sun gwaninta, dace, ko kuma cancanta su yi wa’azi.

4. (a) Ta yaya misalin Bulus ya nuna cewa ƙwarewa don hidimar Kirista ba domin masu ilimi ’yan kalilan ba ne? (b) A waɗanne hanyoyi uku ne Jehovah yake sa mu ƙware a hidima?

4 Amma daga ina ne gwanintar nan take zuwa? Daga iyawar mutum ne? Daga yawar basira? Daga ilimantarwa na musamman a manyan makarantu? Babu shakka manzo Bulus yana da waɗannan abubuwa duka. (Ayukan Manzanni 22:3; Filibbiyawa 3:4, 5) Duk da haka, cikin tawali’u ya fahimci cewa ƙwarewarsa na mai hidima ta zo, ba daga babban makarantar koyo ba, amma daga Jehovah Allah ne. Irin wannan ƙwarewar ga ’yan rukunin kalilan da aka zaɓa ne? Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiyar Korinthiyawa game da ‘ƙwarewarmu.’ Wannan ya nuna cewa Jehovah yana tabbata cewa duka amintattun bayinsa sun gwanance, su yi aikin da ya ba su su yi. Ta yaya Jehovah yake sa Kiristoci na gaskiya su ƙware a yau? Bari mu tattauna hanyoyi uku da yake amfani da su: (1) Kalmarsa, (2) ruhunsa mai tsarki, da (3) ƙungiyarsa ta duniya.

Kalmar Jehovah Tana Sa Mu Ƙware

5, 6. Wane tasiri Nassosi Masu Tsarki ke da shi a kan Kiristoci na gaskiya?

5 Na farko, ta yaya Kalmar Allah ke sa mu ƙware a hidima? Bulus ya rubuta: “Kowane nassi hurare daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Timothawus 3:16, 17) Da haka Nassosi Masu Tsarki suna sa mu ‘gwanance, shiryayyu sarai’ mu yi “managarcin aiki” na koyar da mutane game da Kalmar Allah. Duka mabiyan cocin Kiristendam kuma fa? Suna da Littafi Mai Tsarki. Ta yaya littafi guda zai taimaki wasu mutane su zama masu hidima da suka gwanance kuma ya bar wasu? Amsar ta dangana bisa halinmu ne game da Littafi Mai Tsarki.

6 Abin baƙin ciki, da yawa da suke zuwa coci ba su amince da saƙon Littafi Mai Tsarki “yadda ta ke hakika, maganar Allah” ba. (1 Tassalunikawa 2:13) Kiristendam tarihinsu abin kunya ne game da wannan. Bayan sun ɓatar da shekaru da yawa a yin nazari a makarantun tauhidi, limaman gwanaye ne wajen koyar da Kalmar Allah? Ko kaɗan. Wasu ɗalibai suna soma karatu su gaskata da Littafi Mai Tsarki amma su sauke karatu kuma su zama ’yan shakka! Bayan haka, maimakon yin wa’azin maganar Allah—wanda da yawa cikinsu ba su gaskata da ita ba kuma—sun mai da hidimarsu a wasu hanyoyi, suna ba da goyon baya a muhawwara ta siyasa, suna wa’azi game da matsalolin jama’a, ko kuma nanata falsafar wannan duniya a huɗubarsu. (2 Timothawus 4:3) Akasin haka, Kiristoci na gaske suna bin misalin Yesu Kristi.

7, 8. Yaya halin Yesu game da Kalmar Allah ya bambanta daga na shugabannan addini na zamaninsa?

7 Yesu bai ƙyale shugabannan addinai na zamaninsa su rinjayi tunaninsa ba. Ko yana koya wa ƙaramin rukuni ne, kamar manzanninsa, ko babban garke, Yesu ya yi amfani da littattafai masu tsarki. (Matta 13:10-17; 15:1-11) Wannan ya bambanta shi daga shugabannan addinai na zamaninsa. Sun hana talakawa bincika zurfafan al’amuran Allah. Hakika, al’ada ce ga malamin zamanin ya gaskata cewa wasu ayoyi na Nassi ma’anarsu suna da zurfi da ba za a tattauna su da kowa ba sai da ɗalibi mafi kusa da shi—har ila, za a yi hakan da ƙaramar murya kuma kai rufe. Waɗannan shugabannan addinai sun camfa furta sunan Allah kamar yadda suka camfa tattauna wasu wurare cikin Littafi Mai Tsarki!

8 Kristi ba haka yake ba. Ya gaskata cewa, ba zaɓaɓɓu kalilan ba ne kawai, amma mutane gabaki ɗaya suna bukatar su bincika “kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” Yesu ba ya son ya ba da mabuɗin sani wa rukunin manazarta na Nassi ba. Ya gaya wa almajiransa: “Abin da ni ke faɗa muku cikin duhu, ku furta a sarari: abin da ku ke ji cikin kunne kuma, ku yi shelarsa a bisa soraye.” (Matta 4:4; 10:27) Yesu ya so sosai ya gaya wa mutane da yawa sanin Allah yadda ya yiwu.

9. Wane amfani Kiristoci na gaskiya suke yi da Littafi Mai Tsarki?

9 Kalmar Allah ce ta kamata ta zama aba ta musamman na koyarwarmu. Alal misali, lokacin da muke ba da jawabi a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehovah, karanta ayoyi da aka zaɓa daga Littafi Mai Tsarki bai isa ba. Muna bukatar mu ɗauki lokaci mu yi bayani, mu yi kwatanci, kuma mu yi amfani da Nassosin yadda suka shafe mu. Makasudinmu shi ne mu bayyana rubucaccen saƙon Littafi Mai Tsarki kuma mu dasa su cikin zukatan masu sauraronmu. (Nehemiah 8:8, 12) Ya kamata a yi amfani da Littafi Mai Tsarki yayin da ake ba da gargaɗi ko kuma ba da horo na gyara. Ko da yake mutanen Jehovah suna yare dabam dabam kuma sun fito daga wurare dabam dabam, dukansu suna daraja Littafi mafi girma—Littafi Mai Tsarki.

10. Wane sakamako huraren saƙon Littafi Mai Tsarki ya kasance da shi cikinmu?

10 Idan an yi amfani da shi a wannan hanyar, saƙon Littafi Mai Tsarki yana da iko. (Ibraniyawa 4:12) Yana motsa mutane su yi gyara a rayuwarsu, su daina ayyuka da ba na nassi ba irinsu fasikanci, zina, bautar gumaka, maye, da sata. Ya taimaki mutane da yawa su tuɓe halinsu na dā su saka sabo. (Afisawa 4:20-24) Hakika, in mun daraja shi fiye da kowane ra’ayi ko kuma al’ada ta mutane kuma muka yi amfani da shi sosai, Littafi Mai Tsarki zai iya sa mu gwanance, shiryayyu sosai masu koyar da Kalmar Allah.

Ruhun Jehovah Yana Sa Mu Ƙware

11. Me ya sa aka kira ruhu mai tsarki na Jehovah yadda ya dace ‘mataimaki’?

11 Na biyu, bari mu tattauna matsayin ruhu mai tsarki na Jehovah, ko kuma ikon aiki, a sa mu kasance shiryayyu sosai. Kada mu manta cewa ruhun Jehovah shi ne iko mafi ƙarfi da ke akwai. Jehovah ya ba Ɗansa ƙaunacacce iko ya nuna wannan ƙarfi na ban mamaki domin dukan Kiristoci na gaskiya. Daidai kuwa, Yesu ya ce ruhu mai tsarki ‘mai-taimako’ ne. (Yohanna 16:7) Ya aririci mabiyansa su roƙi Jehovah domin wannan ruhu, ya tabbatar musu cewa Jehovah zai yi musu tanadinsa hannu sake.—Luka 11:10-13; Yaƙub 1:17.

12, 13. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi addu’a domin ruhu mai tsarki ya taimake mu cikin hidimarmu? (b) Ta yaya Farisawa suka nuna cewa ruhu mai tsarki ba ya aiki cikinsu?

12 Muna bukatar mu yi addu’a don ruhu mai tsarki kullum, musamman ya taimake mu a hidimarmu. Yaya wannan ikon aiki yake taɓa mu? Yana aiki cikin azancinmu da zuciyarmu, yana taimakonmu mu canja, mu yi girma a ruhaniya, mu sake halinmu na dā da sabo. (Kolossiyawa 3:9, 10) Zai iya taimakonmu mu koyi halaye masu tamani irin na Kristi. Da yawa cikinmu za mu iya maimaita Galatiyawa 5:22, 23 a zuciya. Waɗannan ayoyi sun jera ’ya’yan ruhun Allah. Na farko ƙauna ce. Wannan hali yana da muhimmanci a hidimarmu. Me ya sa?

13 Ƙauna tana motsuwa ƙwarai. Ƙaunarmu ga Jehovah da maƙwabtanmu na motsa Kiristoci na gaskiya su yi shelar bishara. (Markus 12:28-31) In ba tare da irin wannan ƙaunar ba, ba za mu ƙware mu zama masu koyar da Kalmar Allah ba. Ka lura da bambanci tsakanin Yesu da Farisawa. Matta 9:36 ta ce game da Yesu: “Amma sa’anda ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Yaya Farisawan suke ji game da talakawan? “Amma taron nan, da ba su san Attaurat ba, la’anannu ne.” (Yohanna 7:49) Waɗannan Farisawan ba sa ƙaunar mutanen amma ƙyamarsu suke yi. A bayyane yake, ruhun Jehovah ba ya aiki cikinsu.

14. Ta yaya ya kamata misalin Yesu na nuna ƙauna cikin hidimarsa ya motsa mu?

14 Yesu ya ji tausayin mutane. Yana sane da wahalarsu. Ya san an azabtar da su, sun wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Yohanna 2:25 ya gaya mana cewa Yesu “yana sane da abin da ke cikin mutum.” Domin shi Gwani Mai Aiki ne na Jehovah a lokacin halitta, Yesu ya san haliccin ’yan Adam. (Misalai 8:30, 31) Wannan sanin ya sa ƙaunarsa ta yi zurfi. Bari irin ƙaunar nan koyaushe ta zama abin da ke motsa mu cikin aikinmu na wa’azi! Idan muna ji ya kamata mu yi gyara game da wannan, mu yi addu’a don ruhun Jehovah mai tsarki kuma mu yi aiki cikin jituwa da addu’o’inmu. Jehovah zai amsa mana. Zai aiko da wannan iko da ba za a iya ƙi ba ya taimaka mana mu zama kamar Kristi, wanda mafifici ne a ƙwarewarsa a yin wa’azin bishara.

15. Yaya kalmomin Ishaya 61:1-3 suka aika a kan Yesu amma suka fallasa marubuta da Farisawa?

15 Daga ina ƙwarewar Yesu ya zo? “Ruhun Ubangiji yana bisa gareni,” in ji shi. (Luka 4:17-21) Hakika, Jehovah ne da kansa ya naɗa Yesu ta wurin ruhunsa mai tsarki. Yesu ba ya bukatar ƙarin ƙwarewa. An naɗa shugabannan addini na zamaninsa da ruhu mai tsarki ne? A’a. Ba a kuwa shirya su su cika wannan Ishaya 61:1-3 ba, wadda Yesu ya karanta kuma ya yi amfani da shi ga kansa. Muna roƙonka ka karanta ayoyin ka ga da kanka cewa ’yan riya marubuta da Farisawa ba su cika wannan ba. Ba su da bishara da za su sanar wa matalauta. Kuma yaya za su yi wa ɗaurarru shela ta ’yanci, da mayar da ido ga makafi? A ruhaniya, su ma makafi ne kuma ɗaurarru ga ala’du na mutane! Ba kamar waɗannan mutanen ba, mun ƙware mu koyar da mutane?

16. Wane gaba gaɗi mutanen Jehovah za su iya kasancewa da shi game da ƙwarewarsu na masu hidima?

16 Gaskiya, ba mu yi karatu a manyan makarantu na Kiristendam ba. Ba mu da takardar izini na masu koyarwa daga makarantar tauhidi. Ba mu ƙware ba ke nan ne? A’a! Naɗinmu na Shaidunsa ya zo ne daga wurin Jehovah. (Ishaya 43:10-12) Idan mun yi addu’a domin ruhunsa kuma muka yi aiki cikin jituwa da addu’armu, muna da ƙwarewa mafi girma. Hakika, mu ajizai ne kuma mun kasa sosai wajen misalin Babban Malami, Yesu. Duk da haka, ba ma godiya ne cewa Jehovah yana amfani da ruhunsa ya sa mu ƙware kuma mu shiryu mu zama masu koyar da Kalmarsa?

Ƙungiyar Jehovah Tana Sa Mu Ƙware

17-19. Ta yaya taro guda biyar kowane mako da ƙungiyar Jehovah ta tanadar ya taimake mu mu ƙware mu zama masu hidima?

17 Yanzu, bari mu tattauna hanya ta uku da Jehovah yake sa mu shiryu sosai mu zama masu koyar da Kalmarsa—ikilisiyarsa ko kuma ƙungiyarsa ta duniya da take koyar da mu mu zama masu hidima. Ta yaya? Ka yi tunanin tsarin koyarwa da muke morewa! A kowane mako, muna halartar taron Kirista biyar. (Ibraniyawa 10:24, 25) Muna taruwa a ƙananan rukuni a Rukunin Nazarin Littafi Mai Tsarki mu more nazarin Littafi Mai Tsarki mai zurfi ta wurin littafin da ƙungiyar Jehovah ta yi tanadinsa. Ta wajen saurarawa da yin furci, muna koyo daga juna kuma muna ƙarfafa juna. Muna kuma samun koyarwa ɗaɗɗaya da kula daga mai kula da nazarin rukunin. A Taron gabatar da Jawabi da kuma Nazarin Hasumiyar Tsaro, muna ƙara cin abinci na ruhaniya mai kyau da yawa.

18 An shirya Makarantar Hidima ta Allah ta koya mana yadda za mu koyar. Ta shirya jawabin ɗalibi, muna koyar da yadda za a yi amfani da Kalmar Allah a koyar da darussa dabam dabam. (1 Bitrus 3:15) An taɓa ba ka aiki a kan wani darassi da kamar ka san shi, amma ka iske kana koyon sabon abu game da shi? Yana faruwa kullum. Koya wa wasu wani darasi yana wasa saninmu ƙwarai. Ko ma lokacin da ba mu da aiki, har ila muna koya mu zama masu koyarwa da kyau. A kowane ɗalibi, muna lura da hali mai kyau, muna tunanin yadda za mu yi koyi da waɗannan halaye.

19 An shirya Taron Hidima ya shirya mu masu koyar da Kalmar Allah. Kowanne mako, muna more jawabai masu kyau, tattaunawa, da gwaji da aka shirya don hidimarmu. Wane irin gabatarwa za mu yi amfani da shi? Yaya za mu bi da ƙalubale na musamman a hidimarmu ta fage? Wace hanyar yin wa’azi ne da muke da ita za mu bukaci mu yi amfani da ita? Menene zai sa mu zama masu koyarwa da kyau yayin da muke koma ziyara da gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki? (1 Korinthiyawa 9:19-22) Ana bayyana kuma tattauna irin waɗannan tambayoyi da wasu a Taron Hidima. Sashen taro da yawa daga cikin talifofin Our Kingdom Ministry ne ake ɗauko su, wani kayan aiki da aka yi tanadinsa ta shirya mu don aikinmu mai muhimmanci.

20. Ta yaya za mu iya amfana sosai daga taro da kuma manyan taro?

20 Ta yin shiri don taro da kuma halartarsa da yin amfani da abin da muka koya wajen aikinmu na masu koyarwa, muna koyo da kyau. Amma akwai ƙari. Muna da manyan taro—babban taro da taron gunduma—an shirya su su shirya mu masu koyar da Kalmar Allah. Muna alla-alla mu saurara sosai kuma mu yi amfani da irin waɗannan gargaɗi!—Luka 8:18.

21. Wane tabbaci ya nuna cewa koyar da mu ya yi amfani, kuma ga wa za a yi yabon?

21 Koyarwa da Jehovah ya yi tanadinsa yana taimakawa ne? Gaskiya ta yi magana da kanta. Kowacce shekara ana taimaka wa ɗarurruwan dubban mutane su koyi muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki kuma su rayu cikin jituwa da abin da Allah ke bukata a gare su. Adadinmu yana ƙaruwa, amma ba wani cikinmu da zai yaba wa kansa don wannan. Dole ne mu ɗauki al’amura yadda Yesu ya yi. Ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” Kamar manzanni na dā, mu mutane ne marasa ilimi kuma talakawa. (Yohanna 6:44; Ayukan Manzanni 4:13) Nasararmu ta dangana bisa Jehovah ne, wanda yake jawo mutane masu zuciyar kirki ga gaskiya. Manzo Bulus ya faɗi haka daidai: “Ni na dasa, Apollos ya yi ban ruwa; amma Allah ne ya bada amfani.”—1 Korinthiyawa 3:6.

22. Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ainu game da sa hannu sosai cikin hidimar Kirista ba?

22 Hakika, Jehovah Allah na sa hannu sosai cikin aikinmu na masu koyar da Kalmarsa. Ba koyaushe ba ne za mu ji mun ƙware kamar masu koyarwa. Amma ka tuna Jehovah ne ke jawo mutane ga kansa da kuma Ɗansa. Jehovah ne ke sa mu ƙware mu yi hidima ga sababbin ta wurin Kalmarsa, ruhunsa mai tsarki, da ƙungiyarsa ta duniya. Bari mu karɓi koyarwar Jehovah ta yin amfani da abubuwa masu kyau da yake ba mu yanzu mu zama shiryayyu sosai masu koyar da Kalmar Allah!

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya Littafi Mai Tsarki ke shirya mu don aikin wa’azi?

• Wane matsayi ruhu mai tsarki ke da shi a ƙware mu mu zama masu hidima?

• A waɗanne hanyoyi ƙungiyar Jehovah ke taimakonka ka ƙware zama mai wa’azin bishara?

• Me ya sa za mu yi gaba gaɗi yayin da muke shagala cikin hidima?

[Hoto a shafi na 15]

Shi mai koyar da Kalmar Allah, Yesu ya nuna ƙauna ga mutane

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba