Na Ƙware na Yi Wa’azi Kuwa?
1. Me ya sa bai kamata mu yi tunanin ba mu ƙware yin wa’azi ba?
1 Idan ka taɓa yi wa kanka irin wannan tambayar, kada ka yi sanyin gwiwa! Ba ilimin boko ko kuma iyawarmu ba ce ke sa mu ƙware don zama masu hidima ba. An kira wasu almajiran farko “mutane marasa-karatu ne, talakawa.” Duk da haka, su ƙwararrun masu wa’azin bishara ne domin sun ƙudurta su bi misalin da Yesu ya kafa.—A. M. 4:13; 1 Bit. 2:21.
2. Menene wasu fasalolin koyarwar Yesu?
2 Yadda Yesu Ya Koyar: Koyarwarsa tana da sauƙi, tana da amfani, kuma tana da sauƙin fahimta. Tambayoyinsa, kwatancinsa, da kuma gabatarwarsa masu sauƙi sun ja hankalin masu sauraro. (Mat. 6:26) Ya nuna cewa ya damu da mutane sosai. (Mat. 14:14) Bugu da ƙari, Yesu ya yi magana da gaba gaɗi da kuma iko, domin ya san cewa Jehobah ya umurce shi kuma ya ƙarfafa shi ya cika aikinsa.—Luk 4:18.
3. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu cim ma hidimarmu?
3 Jehobah Yana Taimaka Mana: Ta hanyar Kalmarsa da ƙungiyarsa, Malaminmu Mafi Girma yana koyar da mu don mu samu nasara a yin wa’azin bishara. (Isha. 54:13) Domin Jehobah ya sa a rubuta yadda Yesu ya koyar, hakan ya sa mu bincika hanyoyinsa kuma mu yi koyi da su. Jehobah yana ba mu ruhunsa mai tsarki kuma yana koyar da mu ta hanyar tarurruka na ikilisiya. (Yoh. 14:26) Ƙari ga hakan, yana yin tanadin masu shela da suka ƙware sosai waɗanda za su iya taimaka mana mu ƙara ƙwarewa.
4. Me ya sa ya kamata mu ji cewa mun ƙware mu yi wa wasu wa’azin bishara?
4 Muna da dukan dalilin jin cewa mun ƙware don yin wa’azi, tun da “iyawarmu daga Allah take.” (2 Kor. 3:5, Littafi Mai Tsarki) Yayin da muka dogara ga Jehobah kuma muka yi amfani da dukan tanadodin da ya yi mana cikin ƙauna, za mu “zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.”—2 Tim. 3:17.