Iyaye Ku Biya Bukatun Yaranku!
YARA suna bukatar ja-gora da horo cikin ƙauna, musamman daga iyayensu. Game da wannan, wata malama a Brazil, Tania Zagury ta ce: “Bukatar kowane yaro ne ya samu jin daɗi. Yana da muhimmanci a kafa wa yaro iyaka. Iyaye ne ya kamata su yi wannan. Idan ba su yi ba, ba za a iya ja-gorar yaran ba.”
Amma, a ƙasashe da yawa inda ake ɗaukaka ’yancin kai zai kasance da wuya a bi shawara na baya. To, ina ne iyaye za su juya don taimako? Iyaye masu jin tsoron Allah sun fahimci cewa yaransu “gādo ne daga wurin Ubangiji.” (Zabura 127:3) Da haka, suna dogara ga Kalmar Allah, don ja-gora a renonsu. Alal misali, Misalai 13:24 ta ce: “Wanda ya sauƙaƙa bulalatasa yana ƙin ɗansa ke nan: amma wanda ya ƙaunace shi ya kan hore shi da aniya.”
Bai kamata a fahimci amfani da Littafi Mai Tsarki ya yi da kalmar “bulala,” ya nufa horo na zahiri kaɗai ba; yana nufin hanyar gyara, ko yaya aka yi ta. Hakika, sau da yawa horo da baki ake bukata kaɗai don a gyara tafarkin taurin kai na yaro. Misalai 29:17 ta ce: “Ka hori ɗanka, shi kuwa za ya hutadda ranka: I, za ya sa murna a ranka.”
Yara suna bukatar horo cikin ƙauna don su kawar da halaye da ba a so. Irin wannan gyara ta tsayin daka da alheri yana nuna cewa mahaifi yana kula da yaron. (Misalai 22:6) Saboda haka, iyaye kada ku yi sanyin gwiwa! Ta bin gargaɗi mai kyau, na Littafi Mai Tsarki, za ku faranta wa Jehovah Allah rai kuma ku samu darajar yaranku.