Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 3/1 p. 32
  • “Yanzu, Wannan Zai Yi Maka Zafi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Yanzu, Wannan Zai Yi Maka Zafi”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 3/1 p. 32

“Yanzu, Wannan Zai Yi Maka Zafi”

KA TAƁA jin irin wannan maganar? Wataƙila likita ko nas ya faɗe su kafin ya yi maka allura.

Mai yiwuwa, ba ka ƙi karɓan allurar ba don kada ka ji zafi da aka faɗa. Maimako ka jure wa zafin don ka samu lafiya a nan gaba. A yanayi mai tsanani, karɓa ko ƙin allura da ba ka so zai zama batun rai da mutuwa.

Ko da yake ba koyaushe ba ne za mu bukaci zuwa wurin likita, dukanmu mutane ajizai na bukatar horo, ko gyara, har da wanda wani lokaci yake da zafi. (Irmiya 10:23) Nanata cewa yara na bukatar wannan, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro: amma sandar horo za ta kore masa ita nesa.”—Misalai. 22:15.

Sanda a wannan wurin, alama ce na ikon iyaye. Gaskiya ne cewa yara kalilan ne suke son gyara. Idan ya haɗa da horo, suna iya su yi fushi. Amma iyaye masu ƙauna masu hikima ba sa damuwa da yadda yaron zai yi fushi amma suna damuwa da lafiyar yaron a nan gaba. Iyaye Kirista sun sani cewa Kalmar Allah gaskiya ce yayin da ta ce: “Kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba, amma abin ban ciwo ne a loton yi: amma daga baya ya kan bada amfani mai-salama—watau na adalci ke nan—ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa.”—Ibraniyawa 12:11; Misalai 13:24.

Hakika, ba yara kaɗai ba ne suke bukatar horo. Manya ma suna bukatarsa. Littafi Mai Tsarki magana yake wa manya sa’ad da ya ce: “Ka kama koyarwa da kyau: kada ka sake ta: ka kiyaye ta: gama ranka ce.” (Misalai 4:13) Hakika, mutane masu hikima—yara da manya—za su karɓi horo da ke bisa Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, domin yin haka, daga baya zai tsare rayuwarsu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba