Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ta yaya mace Kirista za ta daidaita aminci ga Allah da yin biyayya ga mijinta marar bi idan yana yin biki na addini?
Yin haka zai bukaci hikima da basira wajenta. Amma tana yin abu mai kyau a yin ƙoƙari ta daidaita hakkokinta biyu. Yesu ya ba da gargaɗi game da yanayi da ya yi daidai da wannan: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.” (Matta 22:21) Hakika, yana maganar hakki ne ga gwamnati, wadda aka gaya wa Kiristoci daga baya su yi biyayya da ita. (Romawa 13:1) Duk da haka, za a yi amfani da gargaɗinsa ga mata ta daidaita hakkinta ga Allah da biyayyarta ta Nassi ga mijinta, ko da shi marar bi ne.
Babu wanda ya san Littafi Mai Tsarki da zai musanta cewa ya nanata hakkin farko na Kirista yana ga Allah Maɗaukaki ne ba, a yi aminci gare shi a dukan lokaci. (Ayukan Manzanni 5:29) Har ila, a yanayi da yawa mai bauta ta gaskiya zai kula da bukatu na marar bi da ke da wani iko ba tare da ya karya dokokin Allah ba, masu girma.
Mun samu misali mai wayarwa daga Ibraniyawa uku, da Daniel sura 3 ta ba da labarinsu. Shugaban ƙasar da suke Nebuchadnezzar, ya ba da doka cewa su da sauran mutanen su zo filin Dura. Da suka fahimci cewa za a yi bautar ƙarya ne a wajen, wataƙila da Ibraniyawa ukun za su fi so su guji zuwa wurin. Wataƙila Daniel ya ba da hujjar ba zai iya kasancewa a nan ba, amma mutane ukun nasu bai yiwu ba.a Saboda haka, suka yi biyayya har zuwa wajen, amma ba za su—kuma ba su—sa hannu ba a wani munanan ayyuka.—Daniel 3:1-18.
Hakanan ma, a lokatai na biki miji marar bi zai bukaci matarsa Kirista ta yi abu da ba za ta so yi ba. Ga wasu misalai: Ya gaya mata ta dafa abinci a ranar da shi da wasu za su yi bikin wani addini. Ko ya ce iyalinsa (har da matarsa) su ziyarce danginsa a ranar su ci abinci ko kuma kawai don ziyara. Ko kuma kafin ranar bikin, zai iya cewa sa’ad da matarsa take cefane, ta saya masa wasu abubuwa—abinci na musamman don bikin, kayan kyauta, ko kuma takardar ƙunsa kyautar da katuna da zai haɗa da kyautar.
A nan ma, mata Kirista za ta ƙudura niyya kada ta sa hannu cikin ayyukan bauta ta ƙarya, waɗannan abubuwa da ya yi aika fa? Shi ne shugaban iyalin, kuma Kalmar Allah ta ce: “Ku mata, ku yi zaman biyayya da maza naku, abin da ya kamata ke nan cikin Ubangiji.” (Kolossiyawa 3:18) A irin wannan yanayi, za ta nuna biyayya ta mata yayin nan kuma tana kasancewa da aminci ga Allah? Dole ta yanke shawara a yadda za ta daidaita biyayya ga mijinta da taka biyayyarta ga Jehovah.
A wasu lokatai, mijinta zai gaya mata ta dafa wani abinci, ƙila domin ya fi son sa ko domin ya saba da cin irin abincin a wani lokaci. Za ta so ta nuna masa ƙauna kuma ta amince da shugabancinsa. Za ta yi haka ko idan ma ya biɗi hakan a lokacin wani hutu? Wasu mata Kirista za su iya yin hakan da lamiri mai tsabta, suna ɗauka shi aiki ne na dafa abinci da suke yi kowace rana. Babu shakka, babu Kirista mai aminci da za ta haɗa wani biki na musamman ga wannan, ko idan mijinta ya yi hakan. Hakanan ma, zai so ta kasance da shi yayin da ya ziyarce danginsa a lokatai dabam dabam kowane wata ko kuma shekara. Za ta iya yin hakan ko ma a ranar hutu ne? Ko kuma za ta saya masa abubuwan da yake son ta sayo masa, ba tare da ƙoƙarin ta san abin da yake so ya yi da kayan da za ta saya masa ba yayin da take cefane?
Hakika, ya kamata mata Kirista ta yi tunanin wasu—yadda zai shafe su. (Filibbiyawa 2:4) Za ta guji nuna wa mutane cewa tana sa hannu cikin hutun, yadda Ibraniyawa ukun ba su so wasu su gan su suna tafiya ba zuwa filin Dura. Saboda haka, cikin hikima za ta yi ƙoƙari ta yi magana da maigidanta ta bincika, ko don darajar motsin ranta, zai iya yin wasu abubuwa game da hutun shi kansa domin ba da dama wa matar da take ƙaunarsa kuma take daraja shi. Zai iya fahimtar hikima na kada ya kawo yanayin kunya tsakaninsu idan ta ƙi ta sa hannu cikin ayyukan addinin ƙarya. Hakika, tattaunawa a hankali tun da wuri zai sa a warware wannan cikin salama.—Misalai 22:3.
A ƙarshe, Kirista mai aminci dole ta gwada gaskiyar kuma ta yanke shawarar abin da za ta yi. Dole ne biyayyanta ga Allah ta zama ta farko, yadda ya kasance ga Ibraniyawa ukun. (1 Korinthiyawa 10:31) Amma a tuna wannan, Kirista za ta tsai da abubuwan da za a iya yi ba tare da karya ƙa’ida ba wajen wanda yake da iko cikin iyali ko kuma a yankin.
[Hasiya]
a Duba “Tambayoyi Daga Masu Karatu” a cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Agusta, 2001 na Turanci.