Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 12/1 pp. 3-4
  • Ƙa’idar Ja-gora—Koyarwa ce ta Dukan Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙa’idar Ja-gora—Koyarwa ce ta Dukan Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Ɓata Ƙa’idar Ja-Gorar
  • Yaya Yesu Ya Ce Mu Rika Bi da Mutane?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙa’idar Ja-gora—Tana da Muhimmanci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Bi da Mutane a Hidimarka Yadda Za Ka So Su Bi da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ɗan Maraƙin Zinariya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 12/1 pp. 3-4

Ƙa’idar Ja-gora—Koyarwa ce ta Dukan Duniya

“Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi muku, ku yi musu hakanan.”—Matta 7:12.

YESU Kristi ya furta waɗannan kalmomi kusan shekara dubu biyu da ta shige a Huɗubarsa mafi shahara a kan Dutse. A cikin ƙarnuka bayan haka, an yi magana ƙwarai kuma an yi rubutu sosai bisa wannan kalami mai sauƙi. Alal misali, an ɗaukaka shi cewa “shi ne ainihin manufar Nassosi,” “taƙaice ayyukan Kirista ga maƙwabcinsa,” kuma “tushen ƙa’idar taɓi’a.” Kamar yadda ta zama sananniya, sau da yawa ana kiranta Ƙa’idar Ja-Gora.

Amma, batun Ƙa’idar Ja-Gora, ba ta ƙare wajen duniyar Kiristoci kawai ba. Yahudanci, Budhidanci, da kuma falsafar Helenawa dukansu sun yi magana bisa wannan wasiyya ta taɓi’a a hanyoyi dabam dabam. Sananniya ce ƙwarai, musamman ga mutane Can Gabas, a cikin furcin Confucius, wanda ake ɗaukaka shi a gabashin duniya cewa Mashahuri ne mai hikima kuma malami. A cikin Analect, na uku cikin Littattafai Huɗu na Confucius, mun samu an furta wannan ra’ayi sau uku. Sau biyu, amsoshi ne ga tambayoyin ɗalibai, Confucius ya ce: “Abin da ba ka so a yi maka, kada ka yi wa wasu.” A wani lokaci, sa’ad da ɗalibinsa, Zigong ya yi fariya, “Abin da ba na so wasu su yi mini, ni ma ba na so na yi musu,” malamin ya mai da martani da wannan amsar mai tunasarwa, “Hakika, amma har yanzu ka kasa yin haka.”

Daga karatun waɗannan kalmomi, mutum zai gani cewa furcin Confucius akasin abin da Yesu ya ce ne daga baya. Bambanci da ya bayyana sarai a Ƙa’idar Ja-Gora da Yesu ya furta shi ne cewa yana bukatar ayyukan kirki wajen yin nagarta ga wasu. A ce mutane suna aikata abubuwa cikin jituwa da furcin kirki na Yesu, suna damuwa da wasu, yin ƙoƙari a taimakon wasu, da kuma bin wannan tsarin kullum. Kana tsammani zai gyara duniyarmu ta yau? Hakika.

Ko an faɗi wannan ƙa’idar a hanya mai kyau, ko marar kyau, ko kuma a wasu hanyoyi dabam, abin da ya fi muhimmanci shi ne mutane a lokatai, a wurare da kuma al’adu dabam dabam sun ba da gaskiya ga ra’ayin Ƙa’idar Ja-Gora. Wannan ya nuna cewa abin da Yesu ya faɗa a cikin Huɗuba a kan Dutse koyarwa ce ta dukan duniya da ta taɓa rayukan mutane a ko’ina a dukan zamani.

Ka tambayi kanka: ‘Zan so a bi da ni cikin daraja, da rashin son zuciya, da kuma rashin ha’inci? Zan so in zauna a cikin duniya da babu wariyar fata, yin laifi, da kuma yaƙi? Zan so in kasance cikin iyalin da kowa yana nuna damuwa da wasu da kuma lafiyarsu?’ To, wa zai ce a’a ga irin wannan? Gaskiyar ita ce, mutane kalilan ne suke more irin wannan yanayin. Ga mutane da yawa, ba za su ma yi begen irin waɗannan abubuwa ba.

An Ɓata Ƙa’idar Ja-Gorar

A cikin dukan tarihi, da akwai lokatai da aka ci mutuncin ’yan Adam kuma aka take musu hakki. Waɗannan sun haɗa da sayar da bayi daga Afirka, sansanin mutuwa na Nazi, tilasta wa yara aiki, da kuma kisan kyashi a wurare dabam dabam. Jerin abubuwa masu ban tsoro ya fi haka yawa.

A yau, duniyarmu ta kimiyya da fasaha ta fiye son kai. Mutane kalilan ne suke tunanin wasu idan ya shafi sukuninsu ko kuma hakkinsu. (2 Timothawus 3:1-5) Me ya sa mutane da yawa suka zama masu son kai, azzalumai, marasa tausayi? Ba domin Ƙa’idar Ja-Gora ce, ko da yake an san ta, amma an ture ta gefe ɗaya cewa ba ta da muhimmanci, ɗabi’ar dā ce ba? Abin baƙin ciki, wannan shi ne ke faruwa har a tsakanin waɗanda suke da’awar suna bauta wa Allah. Kuma daga yadda abubuwa suke faruwa, mutane sai su ƙara zama masu son kai.

Saboda haka, tambayoyi masu muhimmanci da za mu bincika su ne: Menene rayuwa bisa Ƙa’idar Ja-Gora ta ƙunsa? Shin akwai wanda har yanzu yana rayuwa bisanta ne? Kuma za a taɓa samun lokaci da dukan mutane za su rayu cikin jituwa da Ƙa’idar Ja-Gora? Domin amsoshi na gaskiya ga waɗannan tambayoyi, don Allah ka karanta talifi na gaba.

[Hoto a shafi na 3]

Confucius da wasu sun koyar da wasu ɓangarori na Ƙa’idar Ja-Gora

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba