Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 5/1 pp. 14-19
  • Ka Mai Da Hankali Ga Ayyuka Masu Ban Al’ajabi Na Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Mai Da Hankali Ga Ayyuka Masu Ban Al’ajabi Na Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ayyuka Masu Ƙarfi Masu Ban Al’ajabi
  • Yaya Ka Kammala?
  • Ayyuka Masu Ban Al’ajabi a nan Gaba
  • Dubi Mai Aikata Abin Ban Al’ajabi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Jehobah Ya Warkar da Shi
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 5/1 pp. 14-19

Ka Mai Da Hankali Ga Ayyuka Masu Ban Al’ajabi Na Allah

“Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka.”—ZABURA 40:5.

1, 2. Muna da waɗanne tabbaci ne na ayyuka masu ban al’ajabi na Allah, kuma me wannan ya kamata ya motsa mu mu yi?

IDAN ka karanta Littafi Mai Tsarki, za ka ga cewa Allah ya yi abubuwa masu ban al’ajabi ga mutanensa na dā, Isra’ilawa. (Joshua 3:5; Zabura 106:7, 21, 22) Ko da Jehovah ba ya saka hannu haka yanzu a al’amuran ’yan Adam, a kewaye da mu muna ganin tabbaci da yawa da suka tabbatar da ayyukansa na ban al’ajabi. Saboda haka, muna da dalilin haɗa da mai Zabura wajen cewa: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! Da hikima ka yi su duka: duniya cike ta ke da wadatarka.”—Zabura 104:24; 148:1-5.

2 Da yawa a yau suna ƙyale ko suna ƙi da bayyanannan tabbacin ayyukan Mahalicci. (Romawa 1:20) Amma mu, yana da kyau kuma daidai ne mu yi tunani a kansu kuma mu kai ga kammala daidai da matsayinmu a gaban Mahaliccinmu da kuma aikinmu a gabansa. Ayuba surori 38 zuwa 41 za su yi taimako ƙwarai bisa ga wannan, domin a nan Jehovah ya tunasar da Ayuba wani ɓangaren Ayyukansa masu ban al’ajabi. Ka yi la’akari da wasu al’amura masu muhimmanci da Allah ya tayar.

Ayyuka Masu Ƙarfi Masu Ban Al’ajabi

3. Kamar yadda aka rubuta a Ayuba 38:22, 23, 25-29, Allah ya yi tambaya game da waɗanne abubuwa?

3 A wani lokaci Allah ya tambayi Ayuba: “Ka taɓa shiga rumbunan [dusar ƙanƙara], ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara, waɗanda na ajiye domin kwanakin ƙunci, domin kwanakin faɗa da yaƙi?” A ɓangarorin duniyarmu da yawa, dusar ƙanƙara da ƙanƙara abubuwa ne da ake rayuwa tare da su. Allah ya ci gaba: “Wanene ya tsaga gwalolo domin ruwan rigyawa? Wanene ya tsaga hanya domin walƙiyar tsawa? Domin a sa a yi ruwan sama a ƙasar da babu mutum: a hamada kuwa inda babu mutum; domin a ƙosarda busashiyar ƙasa mai-fako, a kuma sa ɗanyar ciyawa ta tsiro? Ruwan sama yana da uba? Wanene ya haifi ɗiɗigan raɓa? Daga cikin cikin wacece ƙanƙara ta fito? Farin [ƙanƙara] ta sama kuwa, wanene mahaifinta?”—Ayuba 38:22, 23, 25-29.

4-6. A wace hanya ce ilimin mutum game da dusar ƙanƙara ba cikakke ba ne?

4 Wasu da suke cikin zamani na yawan hanzari, za su ga dusar ƙanƙara wata tangarɗa ce gare su. Duk da haka, wasu da yawa kuma suna ɗaukar dusar ƙanƙara abin morewa ce, abin da zai sa a sami wurare masu kyan gani don ayyuka na musamman. Tuna da tambayar Allah, kana da sani sosai kuwa game da dusar ƙanƙara, har ma da kamaninta? Hakika, mun san yadda tarin dusar ƙanƙara take, wataƙila daga hoton tarinta ko kuma domin mun ga tarinta a zahiri. Amma ƙwayar dusar ƙanƙarar kuma fa? Ka san yadda take wataƙila domin ka bincika tushensu?

5 Wasu mutane sun ɗauki shekaru suna nazarin kuma suna ɗaukan hotunan ƙwayar dusar ƙanƙarar. Ƙwayar dusar ƙanƙara ɗaya tana ɗauke da ƙanƙananan duwatsu kyawawa masu salo dabam dabam. Littafin nan Atmosphere ya ce: “Iri dabam dabam da ba ya ƙarewa na dusar ƙanƙara ƙage ne, ko da yake masana kimiyya sun nace cewa babu dokar da ta hana a sami tagwayensu, ba a taɓa samun ƙwayoyin dusar ƙanƙara da suke kama da juna ba. Wani bincike na musamman da . . . Wilson A. Bentley, ya yi fiye da shekara 40 yana bincika kuma yana ɗaukan hotunan ƙwayoyin dusar ƙanƙara da madubin kawo nesa kusa kuma bai taɓa ganin waɗanda suka yi kama da juna ba.” Idan ma aka samu tagwaye, da ƙyar, wannan zai ɓata mamaki ne na yawan bambancin ƙwayar dusar ƙanƙara?

6 Ka tuna da tambayar da Allah ya yi: “Ka taɓa shiga rumbunan [ƙanƙara]?” Mutane da yawa suna tsammanin cewa gizagizai ne rumbunan ajiyar dusar ƙanƙara. Za ka yi tunanin zuwa rumbunan don ka kiɗaya dusar ƙanƙarar a irin su da ba ya ƙarewa kuma ka yi nazarin yadda suka kasance? Wani kundin sani na kimiyya ya ce: “Asali da kuma tushen cibiyar ƙanƙara, da ke kawo daskarewar ɗiɗɗigar gizagizai lokacin da sanyin ya kai awo-40, ba a fahimci wannan ba tukuna.”—Zabura 147:16, 17; Ishaya 55:9, 10.

7. Yaya yawan ilimin mutane yake game da ruwan sama?

7 Ko kuma ruwan sama fa? Allah ya tambayi Ayuba: “Ruwan sama yana da uba? Wanene ya haifi ɗiɗigan raɓa?” Wannan kundin sani na kimiyyar ya ce: “Saboda wuyar fahimtar yadda tafiye-tafiyen sarari yake da kuma bambancin da yake tsakanin turari da burbuɗin iska, kamar ba zai yiwu ba a ba da bayani daki-daki a kansa, labarin yadda gizagizai suke ɗiɗɗigowa.” Cikin kalmomi masu sauƙi, masana kimiyya sun ba da doguwar hasashe, amma da gaske ba za su iya ba da cikakken bayani ba game da ruwan sama. Amma, ka san cewa yana da muhimmanci a yi ruwan sama, ya jika duniya, ya rayar da itatuwa, yana sa rayuwa ta yiwu ta zama da daɗi.

8. Me ya sa kalmomin Bulus da ke rubuce a Ayukan Manzanni 14:17 daidai suke?

8 Ba za ka yarda da yadda manzo Bulus ya kammala ba? Ya aririce wasu su bincika waɗannan ayyuka na ban al’ajabi su ba da shaida game da Wanda yake yin su. Bulus ya ce game da Jehovah Allah: “Ba ya bar kansa babu shaida ba, da shi ke yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farinciki.”—Ayukan Manzanni 14:17; Zabura 147:8.

9. Ta yaya ayyuka masu ban al’ajabi na Allah suke nuna ikonsa mai girma?

9 Babu shakka cewa wanda yake yin waɗannan ayyuka masu ban al’ajabi yana da hikima mara iyaka da kuma iko mai yawa. Game da ikonsa, ka yi tunanin wannan: An ce walƙiyar aradu yana aukuwa kowacce rana sau 45,000, fiye da sau miliyan 16 a shekara. Wannan yana nufin cewa 2,000 suna aukuwa a yanzu haka. Tarin girman gizagizai da ke ƙunshe cikin walƙiyar aradu ɗaya, daidai yake da bom na nukiliya guda goma ko fiye da haka da aka jefa a lokacin Yaƙin Duniya na II. Kana iya ganin ƙarfin nan cikin walƙiyar aradu. Ban da ban al’ajabinta, walƙiyar aradu yana taimakawa a ba da iskar nitrogen da ke kai wa ƙasa kuma ya zama taki ga tsiro. Saboda haka, walƙiyar aradu bayyanar ƙarfi ce, amma kuma tana kawo fa’idodi ƙwarai.—Zabura 104:14, 15.

Yaya Ka Kammala?

10. Ta yaya za ka amsa tambayoyi da suke a Ayuba 38:33-38?

10 Ka sa kanka a matsayin Ayuba, cewa Allah Mai Iko Duka yana maka tambaya. Babu shakka za ka yarda cewa mutane da yawa ba sa mai da hankali yadda ya kamata ga ayyukan Allah masu ban al’ajabi. Jehovah ya yi mana tambayoyi da muka karanta a Ayuba 38:33-38. “Ka san ka’idodin sammai? Ka iya kafa mulkinsu a duniya? Ka iya ka tada muryarka ta kai gizagizai, domin ruwa a yalwace shi zubo shi rufe ka? Ka iya ka aika walƙiya, ta tafi, ta ce maka, ga mu nan? Wanene ya sanya hikima a cikin kayan ciki? Wanene kuwa ya bada fahimi ga zuciyar mutum? Wanene ya iya lissafta gajimarai ta wurin hikimarsa? Wanene kuwa ya iya juya tulunan sama, sa’anda turɓaya ta yi gudu ta taru wuri ɗaya ta daskare, hogga kuma suna liƙe ma juna?”

11, 12. Waɗanne abubuwa ne suka ba da tabbacin cewa Allah mai Aikata ayyuka masu ban al’ajabi ne?

11 Darussa kaɗan ne kawai da Elihu ya yi muhawararsu da Ayuba muka yi magana a kan su, sai kuma muka lura da wasu abubuwan da Jehovah ya tambayi Ayuba ya ba da amsa kamar “namiji.” (Ayuba 38:3) Mun ce “wasu” domin a Ayuba surori 38 da 39, Jehovah ya mai da hankali har ila a kan wasu muhimman fasalolin halitta. Alal misali, ya ambata sarƙoƙin sammai. Waye ya san dokokinsu ko ƙa’idodinsu? (Ayuba 38:31-33) Jehovah ya yi magana da Ayuba game da wasu dabbobi—zaki da hankaka, awakan dutse da jakin dawa, ɓauna da jimina sai kuma doki da gaggafa. A taƙaice dai, Allah ya tambayi Ayuba ko shi ya ba su halayensu da yadda suke ci gaba da rayuwa da lafiya. Za ka ji daɗin yin nazarin wannan surar musamman idan kana son dawakai ko kuma wasu dabbobi.—Zabura 50:10, 11.

12 Kana iya bincika surori 40 da 41 ma, inda Jehovah ya sake tambayar Ayuba ya ba da amsa ga tambayoyi game da wasu halittu biyu musamman. Mun fahimci waɗannan su ne dorina, mai girma kuma ƙaƙƙarfa, da kadar Bahar Maliya. Kowannensu abin al’ajabi ne na halitta da ya cancanci mu mai da hankali a kansu. Bari yanzu mu ga yadda za mu kammala.

13. Yaya tambayoyin Allah ya taɓa Ayuba, kuma yaya waɗannan batun ya kamata ya taɓa mu?

13 Ayuba sura 42 ta nuna mana yadda tambayoyin da Allah ya yi ya taɓa Ayuba. Da farko, Ayuba ya fi mai da hankali ga kansa ainun da kuma wasu. Amma, da ya yi na’am da gyara ta wajen tambayoyin Allah, Ayuba ya canja tunaninsa. Ya ce: “Na sani ka iya komi [Jehovah], ba kuwa wani nufinka da za shi hanuwa. Wanene wannan da ke duhunta shawara da rashin sani? Na fa furta abin da ban gane ba, al’amuran da sun fi ƙarfina, waɗanda ban san su ba.” (Ayuba 42:2, 3) Hakika, bayan ya mai da hankali a kan ayyukan Allah, Ayuba ya ce waɗannan abubuwa sun fi ƙarfinsa. Bayan mun bincika waɗannan halittu na ban al’ajabi, ya kamata su sahinta cikinmu hikima da iko mai girma na Allah. Ga menene? Domin kawai mu burge da iko da iyawarsa mai girma ne? Ko kuma ya kamata ya taɓa mu fiye da hakan?

14. Yaya Dauda ya amsa ga ayyuka masu ban al’ajabi na Allah?

14 A Zabura ta 86, mun sami furci da yake da alaƙa da wannan da Dauda ya yi, wanda a cikin zabura na farko ya ce: “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa. Yini yana magana da yini, kuma dare yana gwada ma dare sani.” (Zabura 19:1, 2) Dauda ya ci gaba. A Zabura 86:10, 11 mun karanta: “Mai-girma ne kai, mai-aikata al’ajabai: kai kaɗai ne Allah. Ya Ubangiji, ka koya mini tafarkinka; ni kuwa in yi tafiya cikin gaskiyarka: ka daidaita zuciyata ta ji tsoron sunanka.” Tsoron da Dauda yake da shi ga Mahalicci domin dukan ayyukansa na ban al’ajabi, ya haɗa da tsoro na ban girma. Ka fahimci abin da ya sa. Dauda ba ya son ya baƙanta wa Wanda ya iya yin waɗannan ayyuka masu ban al’ajabi rai. Mu ma ba za mu yi haka ba.

15. Me ya sa tsoro irin na ibada na Dauda ga Allah yake da kyau?

15 Dauda ya fahimci cewa tun da yake Allah yana da iko mai yawa, zai iya yin ikon a kan dukan wanda ba shi da tagomashinsa. Wannan bala’i ne a gare su. Allah ya tambayi Ayuba: “Ka taɓa shiga rumbunan [dusar ƙanƙara], ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara, waɗanda na ajiye domin kwanakin ƙunci, domin kwanakin faɗa da yaƙi?” Dusar ƙanƙara, ƙanƙara, guguwa, iska, da kuma walƙiya, duk suna cikin ma’ajin makamansa. Lalle waɗannan abubuwa ne masu ƙarfi sosai na ban tsoro!—Ayuba 38:22, 23.

16, 17. Menene ya kwatanta iko na ban tsoro da Allah yake da shi, kuma yaya ya yi amfani da waɗannan iko a dā?

16 Wataƙila ka tuna da wani bala’i da ya faɗā wa wasu a yankin da irin waɗannan suka haddasa—ko wani bala’in guguwa ko hadari, ko kuma kamanin ambaliya. Alal misali, a kusan ƙarshen shekara ta 1999, kudu maso yammacin Turai ta fuskanci guguwa da yawa. Ya ba har masana yanayin sarari mamaki. Iska mai ƙarfi tana hurawa mil 125 cikin sa’a guda, ta yayyage jinka, ta wargaje tamfol da kuma wayar lantarki, kuma ta kifar da manyan motoci. Ka yi ƙoƙari ka ƙaga wannan: Hadarin ya tuge ko kuma ya karya bishiyoyi miliyan 270,10,000 a gonar Versailles kawai, a waje da Paris. Miliyoyin gidaje suka kasance babu wutar lantarki. Mutanen da suka mutu sun kusa 100. Dukan wannan a cikin ɗan ƙaramin lokaci. Lalle ƙarfi ne na ƙwarai!

17 Mutum zai iya kiran hadari muguwar aukuwa, mara ja-gora, mara kamewa. To, me zai faru in Wanda ke mai dukan iko da ke yin ayyuka na ban al’ajabi, ya yi amfani da ikon nan da aniyya, ya ja-gorance shi a hanyar da yake so fa? Ya yi abu mai kama da haka a can baya a lokacin Ibrahim, wanda ya koyi cewa Alƙalin dukan duniya ya auna muguntar birane biyu, Saduma ga Gwamarata. Lalatarsu ta yi yawa da kukan laifinsu ya haura zuwa wurin Allah, wanda ya taimaki dukan masu adalci su tsira daga biranen nan da aka hukunta. Tarihi ya ce: “Sa’annan Ubangiji ya zubarda Kibiritu da wuta daga wurin Ubangiji a sama bisa Sodom da Gomorrah,” a kan waɗannan birane. Wannan ma ɗaya ne cikin ayyukan masu ban al’ajabi na Allah, yana ceton masu adalci kuma yana halaka mugaye.—Farawa 19:24.

18. Ga wane abubuwa masu ban al’ajabi ne Ishaya sura 25 ya yi nuni?

18 A wani lokaci Jehovah ya yanke shawara a kan birnin Babila ta dā, wanda wataƙila birnin da aka yi maganarsa a Ishaya sura 25. Allah ya annabta cewa wani birni zai zama kufai: “Ka maida birni tudun ƙasa; birni mai-ganuwa kuma ka maishe shi kufai: fadar baƙi ta zama ba birni ba ce: ba za a gina ta ba daɗai.” (Ishaya 25:2) ’Yan ziyara na zamani da suka ziyarci Babila ta dā za su tabbatar da cewa hakan ya kasance. Halakar Babila tsausayi ne kawai? A’a. Maimako, za mu yarda da bayanin Ishaya: “Ya Ubangiji, kai ne Allahna: zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka; gama ka yi al’ajibai; shawarwarai na tun dā ke nan, cikin aminci da gaskiya.”—Ishaya 25:1.

Ayyuka Masu Ban Al’ajabi a nan Gaba

19, 20. Wane cikar Ishaya 25:6-8 ne za mu yi tsammaninta?

19 Allah ya cika wannan annabci na baya a dā, kuma zai aikata abin al’ajabi a nan gaba. A cikin wannan mahalli, inda Ishaya ya ambaci “al’ajabai” na Allah, mun sami tabbacaccen annabci da bai cika ba tukuna, kamar yadda hukuncin Babila ya cika. Wane ‘al’amari na al’ajabi’ ne aka yi alkawarinsa? Ishaya 25:6 ta ce: “A cikin wannan dutse Ubangiji mai-runduna za ya yi ma dukan al’ummai biki na abinci mai-mai, biki na ruwan anab ajiyayye da tsakinsa, na abinci mai-mai cike da laka, na ruwan anab gyartace sarai, ajiyayye da tsakinsa.”

20 Wannan annabcin babu shakka zai cika a cikin sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta, a nan gabanmu kaɗan. A lokacin, mutane za su sami sauƙaƙawa daga matsaloli da yanzu ke nawaita wasu da yawa. Hakika, annabci da ke cikin Ishaya 25:7, 8 ya ba da tabbacin cewa Allah zai yi amfani da ikonsa na halitta ya yi ayyukansa mafi ban al’ajabi: “Ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki: za ya kuma kawarda zargin mutanensa daga dukan duniya: gama Ubangiji ya faɗi.” Manzo Bulus daga baya ya kawo wannan ayar ya yi amfani da shi ga ta da matattu zuwa rai da Allah zai yi, tashin matattu. Lalle wannan zai zama aiki ne na ban al’ajabi!—Korinthiyawa 15:51-54.

21. Waɗanne ayyuka ne na ban al’ajabi Allah zai yi ga matattu?

21 Wani dalili da ya sa hawayen baƙin ciki zai ɓace daga idanun mutane shi ne cewa za a kawar da dukan cututtuka. Lokacin da Yesu yake duniya, ya warkar da mutane da yawa—ya mai da ganin gari wa makafi, ji ga kurame, ƙarfi ga naƙasassu. Yohanna 5:5-9 ya ba da labarin cewa ya warkar da wani mutum da gurgu ne na shekara 38. Waɗanda suka gani suna ganin abin al’ajabi ne, aiki na ban mamaki. Kuma haka yake! Amma Yesu ya gaya musu cewa abu mafi ban al’ajabi shi ne ta da matattu da zai yi: “Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma: waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai; waɗanda sun yi mugunta, zuwa tashi na shari’a.”—Yohanna 5:28, 29.

22. Me ya sa matalauta da tsiyayyu za su zuba ido tare da bege?

22 Wannan tabbas ne domin wanda ya yi alkawarin Jehovah ne. Ka tabbata cewa lokacin da ya ɗauki kuma ya yi amfani da ikonsa mai girma, sakamakon abin al’ajabi ne. Zabura 72 ta nuna abin da zai yi ta wurin Ɗansa, Sarki. A lokacin masu adalci za su yawalta. Salama za ta zama a ko’ina. Allah zai ceci matalauta da kuma tsiyayyu. Ya yi alkawari: “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu; zangarku za su riƙa lilo kamar Lebanon [na dā]: mazaunan birni za su yi albarka kamar tsiri na ƙasa.”—Zabura 72:16.

23. Ayyuka masu ban al’ajabi na Allah ya kamata su motsa mu mu yi menene?

23 A bayyane yake, muna da dalilin mai da hankali ga ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah—abin da ya yi dā, abin da yake yi a yau, da kuma abin da zai yi a nan gaba ba da daɗewa ba. “Albarka ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, Wanda yana aika al’ajabai shi kaɗai: kuma albarka ga sunansa mai-daraja har abada; bari dukan duniya ta cika da darajarsa. Amin, Amin kuma.” (Zabura 72:18, 19) Wannan ya kamata ya zama al’amarin taɗinmu cike da marmari tare da dangi da kuma wasu. Hakika, bari mu “bayyana darajatasa a wurin al’ummai, al’ajabansa kuma wurin dukan dangogi.”—Zabura 78:3, 4; 96:3, 4.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya tambayar da aka yi wa Ayuba ta nanata iyakar ilimin ’yan Adam?

• Waɗanne misalan ayyuka masu ban al’ajabi na Allah ne da aka nanata a Ayuba surori 37-41 suka burge ka?

• Yaya ya kamata mu amsa bayan mun bincika wasu ayyuka masu ban al’ajabi na Allah?

[Hotuna a shafi na 16]

Me ka kammala game da salo dabam dabam na dusar ƙanƙara da kuma ƙarfi mai ban tsoro na walƙiyar aradu?

[Inda aka Dauko]

snowcrystals.net

[Hotuna a shafi na 19]

Ya kamata ayyuka masu ban al’ajabi na Allah su zama cikin taɗinka kullum

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba