Dubi Mai Aikata Abin Ban Al’ajabi!
“Tsaya kurum, ka tuna da ayyukan Allah masu-ban al’ajabi.”—AYUBA 37:14.
1, 2. A shekara ta 1922, wane abu aka gano na ban al’ajabi, kuma yaya aka ji?
MASANIN kimiyyar haƙar ƙasa da Lord na Ingila suka haɗa kai wajen neman dukiyar na shekaru. A ƙarshe, a ranar 26 ga Nuwamba, 1922, a kabarin Fir’auna na Masarawa a fitaccen ƙwarin Sarakuna, masanin kimiyyar haƙar ƙasar Howard Carter da Lord Carnarvon suka sami ladarsu—kabarin Fir’auna Tutankhamen. Suka kai ga rufaffiyar ƙofa, suka huda. Carter ya saka kyandir ya leƙa.
2 Daga baya Carter ya ba da labari: “Da Lord Carnarvon ya kasa jure wa taraddadi, ya yi tambaya, ‘Kana ganin wani abu kuwa?’ na yi ƙoƙari sosai kafin na furta kalmomin nan, ‘E, abubuwan ban al’ajabi.’ ” Tsakanin dubban dukiya da ke cikin kabarin da akwatin gawa na zinariya. Wataƙila ka iya ganin waɗansu cikin waɗannan ‘abubuwan ban al’ajabi’ a hotuna ko kuma a ma’adanar kayayyakin tarihi. Duk da haka, duk da ban mamakin waɗannan kayayyaki, wataƙila ba su shafi rayuwarka ba. Saboda haka, bari mu juya ga abubuwan ban al’ajabi da babu shakka sun shafe ka kuma suna da muhimmanci a gare ka.
3. A ina muka sami bayani game da abubuwa masu ban al’ajabi da za su kasance da muhimmanci a gare mu?
3 Alal misali, ka yi tunanin mutum wanda ya rayu ƙarnuka da yawa da suka shige, mutumin da ya fi dukan wani zakaran fim, jarumin wasanni, ko kuma ɗan sarakuna. An kira shi wanda ya fi kowa a ƙasar gabas arziki. Za ka gane sunansa—Ayuba. An rubuta littafi guda na Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya game da shi. Duk da haka, wani a zamanin Ayuba, saurayi mai suna Elihu, ya ga ya wajaba ya yi masa gyara. A taƙaice, Elihu ya ce Ayuba yana mai da hankali sosai ga kansa da kuma waɗanda suka kewaye shi. A Ayuba sura 37, mun sami takamaimai kuma shawara ta hikima da za ta amfani kowannenmu.—Ayuba 1:1-3; 32:1–33:12.
4. Me ya kai ga gargaɗi da Elihu ya bayar da aka rubuta a Ayuba 37:14?
4 Wasu uku da ya kamata su zama abokanan Ayuba suka ba da dogon jawabi game da wajejen da suke tsammanin Ayuba ya yi zunubi a tunaninsa ko kuma a abin da ya aikata. (Ayuba 15:1-6, 16; 22:5-10) Elihu ya yi haƙuri har sai da jawabin ya ƙare. Sai ya yi magana da fahimi da kuma hikima. Ya yi furci masu muhimmanci, amma ka lura da wannan furci mai muhimmanci: “Ka ji wannan, ya Ayuba, tsaya kurum, ka tuna da ayyukan Allah masu-ban al’ajabi.”—Ayuba 37:14.
Wanda Ya Yi Ayyukan
5. Menene “ayyukan Allah masu–ban al’ajabi” da Elihu yake nufi suka ƙunsa?
5 Ka lura da cewa Elihu bai shawarci Ayuba ya mai da hankali ga kansa ba, ko Elihu kansa, ko kuma wasu mutane. Elihu cikin hikima ya umurci Ayuba—da kuma mu—mu mai da hankali ga ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah Allah. Me ka ke tsammani furcin nan “ayyukan Allah masu-ban al’ajabi” ya ƙunsa? Bugu da ƙari, domin damuwa da za ka yi game da lafiyar jiki, kuɗi, abin da ke zuwa a nan gaba, iyalinka, abokan aikinka, da kuma maƙwabtanka, me ya sa za ka mai da hankali ga ayyukan Allah? Babu shakka, ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah sun haɗa da hikimarsa da kuma ikonsa bisa dukan halittu na zahiri da suka kewaye mu. (Nehemiah 9:6; Zabura 24:1; 104:24; 136:5, 6) Domin a mai da hankali ga wannan, ka lura da wannan muhimmiyar magana a littafin Joshua.
6, 7. (a) Jehovah ya yi waɗanne ayyuka ne masu ban al’ajabi a zamanin Musa da Joshua? (b) Da ka ga ɗaya daga cikin waɗannan ayyuka na zamanin Musa da Joshua da yaya za ka yi?
6 Jehovah ya kawo annoba bisa ƙasar Masar ta dā kuma ya raba Jar Teku domin Musa ya ja-goranci Isra’ila ta dā zuwa ’yanci. (Fitowa 7:1–14:31; Zabura 106:7, 21, 22) Da akwai abin da ya yi kama da wannan da aka ba da labarinsa ne cikin Joshua sura 3. Joshua da ya gāji Musa, shi ya ja-goranci mutanen Allah su ƙetare wani kogi kuma zuwa Ƙasar Alkawari. Joshua ya ce: “Ku tsarkake kanku: gama gobe Ubangiji za shi aika al’ajabai a wurinku.” (Joshua 3:5) Waɗanne abubuwa masu ban al’ajabi ne?
7 Labarin ya nuna cewa Jehovah ya saka hanya a tsakiyar ruwan Kogin Urdun, saboda dubbai da yawa maza, mata, da yara su wuce a kan sandararriyar ƙasa. (Joshua 3:7-17) Da muna wurin muna kallon kogin ta rabu kuma mutanen suka haye lafiya, irin wannan abin da aka cim ma na ban al’ajabi, da ya burge mu! Ya nuna ikon Allah bisa halitta. Har yanzu ma—a kwanakin ranmu—da akwai abubuwa da suka daidaita wajen ban al’ajabi. Domin mu ga wasu daga cikin waɗannan da kuma dalilin da ya sa za mu mai da hankalinmu a kansu, bincika Ayuba 37:5-7.
8, 9. Ga waɗanne abubuwa masu ban mamaki Ayuba 37:5-7 ta nuna, amma me ya sa za mu yi tunani a kan waɗannan?
8 Elihu ya yi shela: “Allah yana tsawa da muryatasa abin ban mamaki; manyan al’amura ya ke yi, waɗanda sun fi ƙarfinmu.” Menene Elihu yake nufi game da Allah yana yin abubuwa a hanya ‘na ban mamaki’? To, ya ambaci dusar ƙanƙara da kuma ruwan sama. Waɗannan za su iya hana manomi aiki a gona, su ba shi zarafi da kuma dalilin bincika ayyukan Allah. Ba za mu kasance manoma ba, amma ruwan sama da kuma dusar ƙanƙara wataƙila su shafe mu. Ya dangana ga inda ka ke da zama, dusar ƙanƙara da kuma ruwan sama suna shafan ayyukanmu ma. Muna ɗaukan lokaci mu yi bimbini a kan wa yake yin waɗannan abin ban mamaki kuma me wannan yake nufi? Ka taɓa yin haka?
9 Don muhimmancinsa, kamar yadda muka karanta a Ayuba sura 38, Jehovah Allah da kansa ya yi irin wannan tunanin, ya yi wa Ayuba tambayoyi masu ma’ana. Ko da yake Mahaliccinmu ya yi wa Ayuba ne waɗannan tambayoyi, babu shakka sun shafe halinmu, wanzuwarmu, da kuma abin da za mu fuskanta a nan gaba. Bari mu ga abin da Allah ya yi tambaya a kai, kuma bari mu yi tunani game da abin da wannan yake nufi, i, bari mu yi abin da Ayuba 37:14 ya umurce mu.
10. Yaya ya kamata Ayuba sura 38 ta shafe mu, kuma waɗanne tambayoyi ne ta tayar?
10 Sura ta 38 ta fara: “Ubangiji ya amsa ma Ayuba daga cikin hadari, ya ce, Wanene wannan da ke duhunta shawara da maganganu marasa-ilimi? Ka yi ɗamara yanzu kamar namiji; gama zan tambaye ka, sai ka shaida mini.” (Ayuba 38:1-3) Wannan ya shirya salon. Ya taimaki Ayuba ya gyara tunaninsa zuwa ga gaskiyar cewa yana gaban Mahaliccin dukan sararin samaniya kuma zai yi masa hisabi. Wannan abu ne mai kyau a gare mu mu yi da kuma mutanen zamaninmu. Sai Allah ya yi magana a kan irin abubuwan da Elihu ya ambata. “Ina ka ke sa’anda na sanya tussan duniya? Shaida dai, idan kana da fahimi. Wanene ya aiyana iyakarta, ko ka sani? Wanene ya miƙa igiyar aunawa a kanta? A kan me aka gina gurabun tussanta? Wanene ya sanya dutsen ƙusurwarta?”—Ayuba 38:4-6.
11. Waɗanne abubuwa ya kamata Ayuba 38:4-6 ta sa mu gane?
11 A ina Ayuba yake—a ina muke—lokacin da duniya ta kasance? Mu ne mutane da muka zana duniya, kuma daga wannan zanen, muka ayyana kusurwoyin kamar da rula? A’a! Mutane ba su kasance ba ma lokacin. Kamar dai duniyarmu gini ne, Allah ya yi tambaya: “Wanene ya sanya dutsen kusurwarta?” Mun san cewa nisar duniya daga rana daidai ne domin mu rayu kuma mu ci gaba. Kuma girmanta ma ta dace daidai. Da duniya ta fi haka girma, da iskar hydrogen ta fice daga sararinmu kuma duniyarmu ba za ta marabci rai ba. Babu shakka, akwai wanda ya “sanya dutsen kusurwarta” kuma a wurin da ya dace. Ayuba ya cancanci yabo ne? Mu fa? Ko kuma dai Jehovah Allah?—Misalai 3:19; Irmiya 10:12.
Wane Mutum ke da Amsoshin?
12. Tambayar da aka yi a Ayuba 38:6 ta kai mu ga tunanin menene?
12 Allah kuma ya yi tambaya: “A kan me aka gina gurabun tussanta?” Ba kyakkyawar tambaya ba ce? Wataƙila ka san kalmomi da Ayuba bai san su ba—ƙarfin maganaɗison ƙasa. Yawancinmu mun fahimci cewa ƙarfin maganaɗiso daga girmar rana take riƙe duniyarmu, a ce an kafa tushenta. Duk da haka, waye ke da cikakken sani game da ƙarfin maganaɗison ƙasa?
13, 14. (a) Menene dole ne a yarda game da ƙarfin maganaɗison ƙasa? (b) Yaya ya kamata mu amsa ga abin da Ayuba 38:6 ta bayyana?
13 Wani littafi da aka buga ba da daɗewa ba mai jigo The Universe Explained ya yarda cewa ‘maganaɗison ƙasa abu ne da aka sani, duk da haka shi ne abin da ba a fahimta ba ƙwarai a cikin ikon halitta.’ Ya daɗa cewa: “Kamar dai ƙarfin maganaɗiso ya kan yi tafiya cikin sarari nan da nan, ba tare da wani bayyanennan abin yin haka ba. Amma a shekarun baya bayan nan, masana kimiyyar ababan ƙasa suka fara tunanin cewa ƙarfin maganaɗison ƙasa yana tafiya cikin taguwar birbiɗin da ake kira gravitons . . . Amma babu wanda ya tabbata da wanzuwarsu.” Ka yi tunani game da abin da wannan yake nufi.
14 Kimiyya ta ci gaba na shekara 3,000 tun daga lokacin da Jehovah ya yi wa Ayuba waɗancan tambayoyi. Duk da haka, ba mu ba, ba kuma masana ababan ƙasa za su iya yin bayani cikakke a kan ƙarfin maganaɗison da ya riƙe duniyarmu a kan zobenta, daidai inda ya kamata da zai ƙyale mu mu more rayuwa a nan. (Ayuba 26:7; Ishaya 45:18) Amma wannan ba shawara ake bayarwa ba mu nemi zurfaffan ilimin abin da ya wuce fahimta na ƙarfin maganaɗison ƙasa. Maimakon haka, mai da hankali ga wannan batu guda na ayyuka masu ban al’ajabi na Allah ya kamata ya rinjayi ra’ayinmu game da shi. Hikimarsa da sani suna tsoratar da kai, kuma ka ga abin da ya sa ya kamata mu yi koyi game da nufinsa?
15-17. (a) Bisa menene Ayuba 38:8-11 ya mai da hankali, kuma ya kai ga waɗanne tambayoyi? (b) Menene dole ne a yarda da shi game da ilimin teku da yadda suke a duniya?
15 Mahalicci ya ci gaba da tambayarsa: “Wanene kuwa ya kukkulle teku da ƙyamare, sa’anda ya fasu, sai ka ce fitowa ya yi daga cikin ciki. Sa’anda na rufe shi da hadari kamar riga, duhu kuwa baƙi ƙirin ya zama masa tsumman haihuwa, na sa masa iyakata kuma, na sa sama makublai da ƙyamare, na ce, inda za ka zo ke nan, ba za ka wuce ba; a nan fa raƙuman ruwanka masu-alfarma za su tsaya?”Ayuba 38:8-11.
16 Yi wa teku iyaka ya ƙunshi ƙasashe, tekuna, da kuma malalar teku. Yaya tsawon lokacin da mutane suka lura kuma suka yi nazarin a kan waɗannan? A dubban shekaru—an yi wannan sosai a ƙarni na ƙarshe da ya shige. Za ka yi tunanin cewa dukan abin da za a sani game da su, war haka an riga an gama. Duk da haka, a wannan shekara ta 2001, idan ka bincika wannan batu a babban laburare ko kuma ka yi amfani da hanya mai girma na bincike na Intane don ka samu tabbaci na baya bayan nan, menene za ka gani?
17 A cikin wata majiya da aka yarda da ita, za ka samu wannan maganar: “Yadda aka ayana wajejen ƙasa da daben teku a duniya da yadda aka ayana fasalolin manyan ƙasa tun da daɗewa matsala ce ta ban marmari don binciken kimiyya da zace-zace.” Bayan ya faɗi wannan, kundin sani da aka ɗauko maganar nan a ciki ya ba da bayanai guda huɗu da ake tsammani daidai ne amma kuma ya ce waɗannan suna tsakanin “ƙage da yawa.” Kamar yadda ku ka sani, ƙage na nufin “abin da ba shi da cikakken tabbaci wanda yake bayar da bayani bisa zato.”
18. Ga wane kammalawa Ayuba 38:8-11 ya kai ka?
18 Wannan bai nanata cewa tambayoyi da muka karanta a Ayuba 38:8-11 sun zo a kan kari ba? Babu shakka ba za a yaba mana ba domin shirya waɗannan fasalolin duniyarmu. Ba mu kafa wata ba saboda ƙarfin maganaɗinso ya ja ruwa ya malala zuwa inda muke da zama ko kuma ga mu kanmu. Ka san wanda ya yi, Mai Aikata ayyuka masu ban al’ajabi.—Zabura 33:7; 89:9; Misalai 8:29; Ayukan Manzanni 4:24; Ru’ya ta Yohanna 14:7.
Ka Yaba wa Jehovah
19. Furcin waƙa na Ayuba 38:12-14 sun jawo hankalinmu ga waɗanne tabbaci na zahiri?
19 Mutane ba za su karɓi yabo ba domin yadda duniya take zagayawa, da aka ambata a Ayuba 38:12-14. Wannan zagayar ce take kawo wayewar gari, sau da yawa gwanin sha’awa. Yayin da rana ta fito, sifoffin duniyarmu sai su bayyana sarai. Idan muka ɗan mai da hankali ga motsin duniya, dole ne mu yi mamaki da duniya ba ta zagaya da sauri, wadda za ta kasance da haɗari, yadda muka sani. Kuma ba ta tafiya a hankali da dare da rana, su sa su yi tsawo ainun, da zai jawo zafi da sanyi da za su hana rayuwa. Babu shakka, ya kamata mu yi farin ciki cewa Allah ne ba rukunin wasu mutane ba ne suka ayana saurin zagaya ta duniya.—Zabura 148:1-5.
20. Yaya za ka amsa tambayar da aka yi a Ayuba 38:16, 18?
20 Yanzu, ka yi tunanin cewa Allah ya yi maka waɗannan ƙarin tambayoyi: “Kai ka taɓa shiga mafitan teku? Ka taɓa yawo cikin lolokan zurfafa?” Masana kimiyyar teku ma ba za su iya ba da cikakkiyar amsa ba! “Ka gane faɗin duniya? Furta, idan dai ka san wannan duka.” (Ayuba 38:16, 18) Ka ziyarci kuma ka binciki dukan yankunan duniya, ko ma yawancinta? Mai da hankali ga kyawawan wajeje da kuma abubuwan ban mamaki na duniya zai ɗauki tsararraki nawa? Wannan lalle zai kasance lokatai ne na ban al’ajabi!
21. (a) Tambayar da take Ayuba 38:19 ta tayar da waɗanne ra’ayi ne na kimiyya? (b) Gaskiya game da haske ya kamata ta motsa mu mu yi menene?
21 Ka duba wannan tambayar da ta cika da hikima a Ayuba 38:19: “Ina hanya zuwa mazaunin haske? A ina kuma duhu yake?” Wataƙila ka sani da daɗewa cewa masana kimiyya sun gaskata cewa haske yana tafiya kamar rakumin iska kamar gargada da muke gani a bisa tafki. Sai a shekara ta 1905, Albert Einstein ya bayyana cewa haske kama yake da wani dami, ko kuma burbuɗin kuzari. Wannan ya warware batun ne? Wani sabon kundin sani ya yi tambaya: “Haske rakumin iska ne ko burbuɗi?” Ya amsa: “Yadda yake dai, [haske] ba zai zama ko ɗaya a cikinsu ba, domin abubuwa biyun [rakumin iska da burbuɗi] sun sha bam bam. Amsar da ta fi kyau ita ce, haske ba ko ɗaya ba ne cikinsu sam.” Duk da haka, hasken yana ɗuma mu (kai tsaye ko kuma ta wata hanya) ko da ma babu mutumin da zai iya ba da cikakken bayanin ayyukan Allah game da wannan. Muna morar abinci da kuma iskar oxygen da ake samu yayin da itatuwa sun sami haske. Za mu iya karatu, mu ga fuskar waɗanda muke ƙauna, mu ga faɗuwar rana, da kuma abubuwa da yawa. Yayin da muke wannan, bai kamata mu mai da hankali ba ga ayyuka masu ban al’ajabi na Allah?—Zabura 104:1, 2; 145:5; Ishaya 45:7; Irmiya 31:35.
22. Ta yaya Dauda na dā ya amsa ga ayyuka masu ban al’ajabi na Allah?
22 Bimbininmu a kan ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah domin kawai ya burge mu ne, kamar dai kawai mu cika da tsoro har ba za mu iya magana ba? A’a. Mai Zabura na dā ya yarda da rashin yiwuwar fahimtar da kuma yin kalami a kan dukan ayyukan Allah. Dauda ya rubuta: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, . . . ba su lissaftuwa a gabanka; ko da ni ke so in bayyana su in bada labarinsu, sun fi gaban lissafi.” (Zabura 40:5) Babu shakka, ba ya nufin cewa, zai yi shiru game da waɗannan manyan ayyukan. Dauda ya tabbatar da haka ta niyyarsa da ya furta a Zabura 9:1: “Zan yi godiya ga Ubangiji da dukan zuciyata; zan bayyana dukan al’ajabanka.”
23. Yaya ka ke ji game da ayyuka masu ban al’ajabi na Allah, kuma ta yaya za ka taimaki wasu?
23 Bai kamata mu ma ya motsa mu ba? Bai kamata mamaki bisa manyan ayyukan Allah su motsa mu mu yi magana game da shi ba, game da abin da ya yi, da kuma abin da har ila zai yi? Amsar a bayyane take—ya kamata mu “bayyana darajatasa a wurin al’ummai, al’ajabansa kuma wurin dukan dangogi.” (Zabura 96:3-5) Hakika, za mu iya nuna godiyarmu cikin tawali’u ga ayyuka masu ban al’ajabi na Allah ta wajen gaya wa wasu abin da muka koya game da shi. Ko ma sun yi girma a cikin al’adar da ba su yarda da Allah ba, furcin mu mai kyau, mai ilimantarwa zai iya motsa su ga gano cewa da akwai Allah. Fiye da haka, zai iya motsa su su so su koya game da shi kuma su bauta wa wanda ya “halicci dukan abu,” Mai Aikata ayyuka masu ban al’ajabi, Jehovah.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.
Yaya Za Ka Amsa?
• Gargaɗi da aka rubuta a Ayuba 37:14 ya sa ka ka yi tunani a kan waɗanne ayyukan Allah?
• Waɗanne abubuwa ne aka nanata a cikin Ayuba sura 37 da 38 da kimiyya ba za ta iya ba da cikakken bayani ba?
• Yaya ka ke ji game da ayyuka masu ban al’ajabi na Allah, kuma yana motsa ka ka yi menene?
[Hoto a shafi na 13]
Wa ya yi wa teku iyaka, ya ajiye ta a wajen ta?
[Hoto a shafi na 13]
Waye ya ziyarci dukan kyawawan wajeje na duniya, waɗanda Allah ya halitta?