Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 2/1 pp. 13-17
  • Ka Mai Da Gaskiya Taka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Mai Da Gaskiya Taka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dabarun Shaiɗan
  • Idan Shakka ta Daɗe Kuma Fa?
  • Ku Yi Hankali da Dabarun Shaiɗan!
  • Adana Abin da Muke da Shi
  • Sunanmu ba Laƙabi ba ne Kawai
  • Ta Yaya Za Ka Kau da Shakka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Waɗanda Suke Tare da Mu, Sun Fi Waɗanda Suke Tare da Su
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Elisha Ya Ga Karusai na Wuta​—⁠Kai Kuma Fa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Nazari Da Kanmu Da Yake Sa Mu Ƙware Wajen Koyarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 2/1 pp. 13-17

Ka Mai Da Gaskiya Taka?

“Ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” —Romawa 12:2.

1, 2. Me ya sa ba shi da sauƙi a zama Kirista na gaskiya a yau?

ZAMA Kirista na gaskiya a waɗannan kwanaki na ƙarshe—waɗannan “zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai”—ba shi da sauƙi. (2 Timoti 3:1) Gaskiyar ita ce, domin a bi misalin Kristi, dole ne mutum ya yi nasara bisa duniya. (1 Yahaya 5:4) Ka tuna da abin da Yesu ya ce game da hanyar Kirista: “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa halaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa. Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.” Ya sake cewa: “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki [gungumen azabtar da shi] kowace rana, ya bi ni.”—Matiyu 7:13, 14; Luka 9:23.

2 Bayan ya samu ƙunƙuntacciyar hanyar rai, ƙalubale na gaba ga Kirista shi ne ya tsaya a kanta. Me ya sa hakan ta zama ƙalubale? Domin keɓe kanmu da kuma baftisma sun sa mun zama abin farautar Shaiɗan ta makidodi ko kuma dabarunsu. (Afisawa 6:11) Yana lura da inda muka raunana kuma yana amfani da su a ƙoƙarinsa na halaka ruhaniyarmu. Ballantana ma, ya yi ƙoƙarin ya halaka Yesu, me zai sa ya ƙyale mu?—Matiyu 4:1-11.

Dabarun Shaiɗan

3. Ta yaya Shaiɗan ya dasa tantama a zuciyar Hauwa’u?

3 Wata dabara da Shaiɗan yake amfani da ita, ita ce saka tantama a zukatanmu. Yana neman inda muka raunana ne a makamanmu na ruhaniya. A farko farko ma, ya yi amfani da wannan dabarar ga Hauwa’u, ya yi tambaya: “Ko Allah ya ce, Ba za ku ci daga wani itace da ke a gonar ba?” (Farawa 3:1) Wato, Shaiɗan yana cewa ne, ‘Shin zai yiwu kuwa a ce Allah ya raɗa muku wannan hani? Zai hana ku abu haka mai kyau? To, ai Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta!’ Shaiɗan ya dasa ƙwayar tantama, sai ya jira ta tsiro.—Farawa 3:5.

4. Waɗanne tantama za su iya su shafi wasu a yau?

4 Ta yaya Shaiɗan yake amfani da wannan dabarar a yau? Idan muka yi watsi da karatunmu na Littafi Mai Tsarki, nazarinmu, yin addu’armu, da kuma hidimarmu da taro na Kirista, za mu zama ba mu da kāriya daga shakka da wasu za su furta. Alal misali: “Ta yaya za mu san cewa wannan ita ce gaskiya da Yesu ya koyar?” “Waɗannan da gaske kwanaki na ƙarshe ne? Ballantana ma, mun riga muna cikin ƙarni na 21.” “Armageddon ya yi kusa, ko kuma yana da nisa har yanzu?” Idan irin waɗannan shakka suka taso, me za mu yi mu cire su?

5, 6. Menene tilas ne mu yi idan shakka ta taso?

5 Yakubu ya ba da gargaɗi mai amfani da ya rubuta: “In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi. Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska ke korawa tana tuttunkuɗawa. Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa, gu ɗaya a kudan al’amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.”—Yakubu 1:5-8.

6 To, menene tilas ne mu yi? Ya kamata mu ‘ci gaba da roƙon Allah’ cikin addu’a ya ba mu bangaskiya da fahimi kuma ya albarkaci ƙoƙarinmu a nazari na kanmu game da kowace tambaya ko kuma shakka. Za mu iya kuma mu nemi taimako daga wajen waɗanda suke da ƙarfi a bangaskiya, kuma kada mu taɓa yin shakkar cewa Jehovah zai ba mu taimako da muke bukata. Yakubu har ila ya ce: “Ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku. Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku.” Hakika, shakkarmu za ta ƙare idan muka miƙa kanmu ga Allah ta wajen nazari da addu’a.—Yakubu 4:7, 8.

7, 8. Waɗanne sharuɗa ne da akwai na tabbatar da hanyar bauta da Yesu ya koyar kuma su waye suke bin waɗannan sharuɗa?

7 Alal misali, mu ɗauki wannan tambayar: Ta yaya muka sani cewa muna yin bauta da Yesu ya koyar? Don a amsa wannan, waɗanne sharuɗa za a bincika? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Kiristoci na gaskiya dole ne su kasance suna da ƙauna ta gaskiya tsakaninsu. (Yahaya 13:34, 35) Dole ne su tsarkake sunan Allah, Jehovah. (Ishaya 12:4, 5; Matiyu 6:9) Kuma dole ne su sanar da wannan sunan.—Fitowa 3:15; Yahaya 17:26.

8 Wata aba da take nuna bauta ta gaskiya ita ce daraja Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Littafi ne na musamman wanda ya bayyana mutumtakar Allah da kuma nufe-nufensa. (Yahaya 17:17; 2 Timoti 3:16, 17) Ƙari ga haka, Kiristoci na gaskiya suna sanar da Mulkin Allah shi ne kaɗai begen mutum domin rai madawwami a aljanna a duniya. (Markus 13:10; Wahayin Yahaya 21:1-4) Sun ware kansu daga siyasar lalaci na wannan duniya da kuma hanyar rayuwarta ta ƙazanta. (Yahaya 15:19; Yakubu 1:27; 4:4) Su wa suke bin waɗannan sharuɗa a yau? Gaskiya ta nuna cewa amsar ɗaya ce kawai—Shaidun Jehovah.

Idan Shakka ta Daɗe Kuma Fa?

9, 10. Menene za mu yi domin mu magance shakka da ta daɗe?

9 To, yaya idan muka fuskanci cewa muna cikin rijiyar shakka? Menene ya kamata mu yi? Mai hikima Sarki Sulemanu ya ba da amsa: “Ɗana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na faɗa maka ka yi. Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi. I, ka roƙi ilimi da tsinkaya. Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya. Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah.”—Karin Magana 2:1-5.

10 Wannan ba abin mamaki ba ne? Idan kana da niyyar ka saurari hikimar Allah za ka yi “nasara a kan koyon sanin Allah.” Hakika, za mu iya samun sanin Mamallakin dukan halitta idan muna da niyyar ɗauka kuma mu riƙe maganarsa. Wannan yana nufin komawa ga Jehovah ta wajen addu’a da kuma nazari na kanmu. Ɓoyayyiyar dukiya na Kalmarsa za ta iya cire shakka kuma ya taimake mu mu ga gaskiya.

11. Ta yaya shakka ta shafi baran Elisha?

11 Misali da ya fita sarai na yadda addu’a ta taimaki bawan Allah da ya razana kuma yake shakka, yana cikin 2 Sarakuna 6:11-18. Baran Elisha ba shi da fahimta ta ruhaniya. Bai iya fahimtar cewa akwai runduna na samaniya da suke wajen don su tallafa wa annabin Allah ba, wanda sojojin Suriya suke neman yi wa hari. Domin tsoro kuwa baran ya yi kuka: “Wayyo, maigidana! Me za mu yi?” Me Elisha ya yi? “Kada ka ji tsoro gama waɗanda ke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.” Amma ta yaya baran nan zai tabbata da haka? Bai iya ganin rundunar samaniyar ba.

12. (a) Ta yaya aka magance shakka ta baran? (b) Ta yaya za mu magance kowace irin shakka da muke da ita?

12 “Elisha ya yi addu’a ya ce, ‘Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa ya gani.’ Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin, sai ga dutsen cike da dawakai da karusan wuta kewaye da Elisha.” A wannan lokacin Jehovah ya sa baran ya ga rundunar samaniya da suke kāre Elisha. Kada mu yi tsammanin irin wannan taimakon a yau. Ka tuna cewa baran annabin ba shi da cikakken Littafi Mai Tsarki wanda zai karanta domin ya ƙarfafa masa bangaskiya. Mu muna da Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi amfani da shi da kyau, bangaskiyarmu za ta ƙarfafa ma. Alal misali, za mu iya yin tunani a kan labarai da yawa da suka kwatanta Jehovah a kotunsa na samaniya. Waɗannan babu shakka cewa Jehovah yana da ƙungiya ta samaniya wadda take taimakon bayinsa a aikin ilimantarwa a dukan duniya a yau.—Ishaya 6:1-4; Ezekiyel 1:4-28; Daniyel 7:9, 10; Wahayin Yahaya 4:1-11; 14:6, 7.

Ku Yi Hankali da Dabarun Shaiɗan!

13. Ta wace hanya ce Shaiɗan yake so ya raunana riƙe gaskiyarmu?

13 Waɗanne hanyoyi ne kuma Shaiɗan yake amfani da su ya raunana ruhaniyarmu da kuma riƙon gaskiya da muka yi? Ɗaya cikinsu ita ce lalata, a dukan fannoninta. A duniya da ta haukace da jima’i, abin da ake kira sha’ani ko kwanan gida ya zama abu na kullum ga wannan tsara mai son nishaɗi wadda ta dage sai ta sami nishaɗi ko ta yaya. Siliman, telibijin, da kuma bidiyo suna ɗaukaka irin wannan salon rayuwa. Hotunan mutane tsirara sun cika hanyar sadarwa, musamman ma Intane. Jaraba tana jiran wanda yake so ya sha kallo.—1 Tasalonikawa 4:3-5; Yakubu 1:13-15.

14. Me ya sa wasu Kiristoci suka faɗi ga dabarun Shaiɗan?

14 Wasu Kiristoci sun ƙyale son su sani ya shafi rayuwarsu kuma ya ɓata musu tunani ta wajen kallon hotunan mutane tsirara ko kuma waɗanda suke jima’i. Sun ƙyale kansu su faɗa cikin tarkon dabara na Shaiɗan. Yin haka sau da yawa ya kai ga haɗari na ruhaniya. Irin waɗannan ba su yi ‘halin jarirai ba wajen mugunta.’ Ba su yi ‘dattako ba wajen hankali.’ (1 Korantiyawa 14:20) Kowacce shekara dubbai suna ganin sakamakon rashin bin sharuɗa da kuma mizanan Kalmar Allah. Suka yi banza da ɗauka da kuma adana “dukan makamai na Allah.”—Afisawa 6:10-13; Kolosiyawa 3:5-10; 1 Timoti 1:18, 19.

Adana Abin da Muke da Shi

15. Me ya sa yake yi wa wasu wuya su yi godiya ga gadōnsu na ruhaniya?

15 “Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yanta ku,” in ji Yesu. (Yahaya 8:32) Yawancin Shaidu ya kasance dole su bar halayensu na dā da kuma hulɗa da addinansu na dā. Saboda haka, suke jin daɗin ’yanci da gaskiya ta kawo. A wani ɓangare kuma, wasu matasa waɗanda iyaye da suka yi renonsu suna cikin gaskiya yana yi musu wuya su yi godiya ga gadōnsu na ruhaniya. Ba su taɓa zama sashen addinin ƙarya ba ko kuma na duniyar nan da take ba da nanaci a kan biɗan nishaɗi, da shan ƙwayoyi, da kuma lalatarta. Sakamakon haka, sun kasa gane bambanci mai girma da yake tsakanin aljannarmu ta ruhaniya da kuma duniyar lalaci ta Shaiɗan. Wasu suna faɗa wa jarabar ɗanɗana guba ta duniyar, su ga abin da suke hasararsa!—1 Yahaya 2:15-17; Wahayin Yahaya 18:1-5.

16. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu? (b) Me aka koya mana kuma aka ƙarfafa mu mu yi?

16 Da gaske muna so mu ƙona yatsarmu domin mu san ciwo da kuma wahalar? Za mu iya koya daga wahala da wasu suka fuskanta? Muna bukatar mu koma “ƙazantar” duniyar nan ne domin mu gani ko muna hasarar wani abu? (2 Bitrus 2:20-22) Bitrus ya tunasar da Kiristoci na ƙarni na farko waɗanda suka taɓa zama sashen duniyar Shaiɗan: “Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al’ummai ke son yi, ya isa hakanan, wato zaman fajirci, da mugayen sha’awace-sha’awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama.” Hakika, ba ma bukatar mu ɗanɗana ‘ƙazamar rayuwa’ don mu ga yadda take. (1 Bitrus 4:3, 4) Akasin haka, ana koya mana mizanan Jehovah na ɗabi’a a Majami’un Mulki waɗanda cibiyar ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki ne. Kuma, an ƙarfafa mu mu yi amfani da ƙarfin tunaninmu mu tabbatar wa kanmu cewa muna da gaskiya kuma saboda haka mu mai da gaskiyar ta zama tamu.—Joshuwa 1:8; Romawa 12:1, 2; 2 Timoti 3:14-17.

Sunanmu ba Laƙabi ba ne Kawai

17. Ta yaya za mu zama Shaidun Jehovah na ƙwarai?

17 Idan muka mai da gaskiya tamu, za mu yi ƙoƙari mu gaya wa wasu a kowane lokaci da ya dace. Wannan ba ya nufin cewa za mu yi ƙoƙari mu tilasa wa waɗanda ba su da marmari ba. (Matiyu 7:6) Maimako, ba za mu yi shiru ba wajen nuna kanmu Shaidun Jehovah. Idan mutum ya nuna marmari ko kaɗan ne ta wajen yin tambaya ta gaskiya ko kuma ta wajen karɓan littafi na Littafi Mai Tsarki, za mu kasance a shirye mu gaya masa begenmu. Babu shakka, wannan zai bukaci cewa koyaushe za mu kasance da littattafai ko a ina muke—a gida, a wurin aiki, a makaranta, a shago, a wajen wasanni.—1 Bitrus 3:15.

18. Ta yaya nuna kanmu Kiristoci ne sarai zai amfane mu a rayuwa?

18 Idan muka bayyana kanmu Kiristoci, muna ƙarfafa kāriyarmu ce ga farmaki na dabara na Shaiɗan. Idan ana bikin ranar haihuwa ko kuma Kirsimati ko kuma caca a ofis, abokan aiki sau da yawa suna cewa, “Ku ƙyale ta. Mashaidiyar Jehovah ce.” Domin wannan dalilin har ila yau, mutane ba za su so yin wasu maganganun banza ba a gabanmu. Saboda haka, sanar da matsayinmu na Kirista yana da amfani ƙwarai a rayuwarmu, kamar yadda Bitrus ya nuna: “To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da ke nagari? Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da ke daidai, ku masu albarka ne.”—1 Bitrus 3:13, 14.

19. Ta yaya muka sani cewa mun yi nisa cikin kwanaki na ƙarshe?

19 Wani amfanin mai da gaskiya tamu, shi ne za mu tabbata cewa waɗannan da gaske kwanaki ne na ƙarshe na wannan tsarin abubuwa. Za mu sani cewa yawancin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suna kaiwa ƙarshensu a zamaninmu.a Gargaɗin Bulus cewa “a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai,” miyagun abubuwa na ƙarni da ya shige ya tabbatar da wannan. (2 Timoti 3:1-5; Markus 13:3-37) Wani talifin jarida a baya bayan nan game da ƙarni na 20 an yi masa laƙabi “Za a Tuna da Shi Tsara ne na Mugunta.” Talifin ya ce: “Shekara ta 1999 ta kasance mafi kisa a kashi na biyu na ƙarni da aka fi kisa.”

20. Yanzu lokaci ne na yin wane aiki?

20 Yanzu ba lokaci ba ne na tantama. Albarkar Jehovah ta tabbata a kan aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki mafi girma da aka taɓa yi a dukan duniya domin shaida ga dukan al’ummai. (Matiyu 24:14) Ka mai da gaskiya taka kuma ka gaya wa wasu. Madawwamiyar rayuwarmu nan gaba ta dangana bisa abin da muka yi yanzu. Karaya ba za ta sa a samu albarkar Jehovah ba. (Luka 9:62) Maimako, lokaci ne na “tsaya a kafe, kullum kuna himantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san faman da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza yake ba.”—1 Korantiyawa 15:58.

[Hasiya]

a Duba Hasumiyar Tsaro, 1 ga Fabrairu 2000, shafuffuka 6-7. Izifi na 13-18 sun ba da hanyoyi shida da suka nuna tabbacin cewa tun daga shekara ta 1914 muke rayuwa cikin kwanaki na ƙarshe.

Ka Tuna?

• Ta yaya za mu kawar da shakka?

• Menene za mu koya daga misalin baran Elisha?

• Game da wane jaraba ne a ɗabi’a dole mu mai da hankali ko da yaushe?

• Me ya sa ya kamata mu nuna sarai mu Shaidun Jehovah ne?

[Hotuna a shafi na 14]

Nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai zai iya taimake mu mu kawar da shakka

[Hoto a shafi na 15]

An kawar da shakkar baran Elisha ta wajen wahayi

[Hoto a shafi na 16]

Ana koya mana mizanan ɗabi’a masu girma na Jehovah a cikin Majami’ar Mulki kamar wannan da ke Benin

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba