Nazari Da Kanmu Da Yake Sa Mu Ƙware Wajen Koyarwa
“Ka yi [waswasi] cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin ci gabanka ya bayyanu ga kowa. Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka.”—1 TIMOTHAWUS 4:15, 16.
1. Menene yake tabbatacce game da lokaci da kuma nazari?
“GA KOWANE abu akwai nasa kwanaki,” in ji Littafi Mai Tsarki a Mai-Wa’azi 3:1. Wannan haka yake ga nazari. Yana yi wa mutane da yawa wuya su yi waswasi a kan abubuwa na ruhaniya idan a lokacin da bai dace ba ne ko kuma a wurin da bai dace ba. Alal misali, bayan ka yi aiki mai wuya ka zauna ka ci abinci mai kyau da yamma, za ka ji kamar kana so ka yi nazari, musamman idan kana zaune a kan kujerarka na sukuni da kake so a gaban telibijin? Da ƙyar. To, menene maganin yanayin? A bayyane yake, dole ne mu zaɓi lokaci da kuma wurin da za mu yi nazari domin mu amfana ƙwarai.
2. Wane lokaci ne sau da yawa ya fi kyau domin nazari?
2 Mutane da yawa sun ga cewa lokaci da ya fi musu kyau don nazari shi ne da safe sa’ad suka farka. Wasu suna amfani da lokacin hutawa na rana domin nazari na gajeren lokaci. Ka lura da abin da aka ce game da lokaci domin ayyukan ruhaniya masu muhimmanci a misali na gaba. Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya rubuta: “Ka jishe ni rahamarka da safe; Gama a wurinka ni ke dogara: Ka sa in san tafarkin da zan bi; Gama a gareka ni ke ɗaukaka raina.” (Zabura 143:8) Annabi Ishaya ya nuna irin wannan muradin sa’ad da ya ce: “Ubangiji Yahweh ya ba ni harshe na koyayyun mutane, domin in san yadda zan tokare da magana wanda ya gaji: safiya kan safiya ya kan tashe ni, ya kan farkar da kunnena domin in ji kamar koyayyun mutane.” Abin da ake nufi shi ne cewa muna bukatar mu yi nazari kuma mu yi magana da Jehovah sa’ad da muke cikin hankalinmu, ko da wane lokaci ne.—Ishaya 50:4, 5; Zabura 5:3; 88:13.
3. Wane yanayi ne suka fi kyau domin nazari mai inganci?
3 Wani abu kuma domin ingantaccen nazari shi ne kada mu zauna a kan kujera mai sukuni ko kushin. Wannan ba hanya ba ce na kasancewa cikin hankalinmu. Sa’ad da muke nazari, dole ne zuciyarmu ta kasance tana aiki, kuma sukuni da yawa ba ya barin haka. Kuma abin da ake so domin nazari da bimbini shi ne wurin da babu surutu babu abin da zai ɗauki hankali. Ƙoƙarin yin nazari da rediyo yana magana, ko kuma telibijin ko kuma yara suna son ka mai da musu hankalinka ba zai kawo sakamako mai kyau ba. Sa’ad da Yesu yake so ya yi bimbini, ya je wurin da babu kowa. Ya yi magana kuma game da tamanin neman wurin da babu kowa domin addu’a.—Matta 6:6; 14:13; Markus 6:30-32.
Nazari da Yake Sa Mu Ƙware Wajen Ba da Amsa
4, 5. A waɗanne hanyoyi ne mujallar nan Bukata take da taimako?
4 Nazari yana gamsarwa sa’ad da muka yi amfani da abubuwan taimako dabam dabam na Littafi Mai Tsarki domin mu tona da zurfi cikin wani batu, musamman sa’ad da muka yi haka domin mu amsa tambayar wani. (1 Timothawus 1:4; 2 Timothawus 2:23) Da farko, sababbi da yawa suna nazarin mujallar nan Menene Allah Yake Bukata a Garemu?,a da ake samu yanzu cikin harsuna 261. Mujalla ce mai sauƙi amma cikakkiya, kuma tana bisa Littafi Mai Tsarki ne. Tana taimakon mutumin da yake karanta ta ya fahimci abin da Allah yake bukata domin bauta ta gaskiya da wuri. Duk da haka, yadda aka tsara ta bai ba da filin bincike dalla-dalla game da kowane batu ba. Idan ɗalibinka na Littafi Mai Tsarki ya yi tambaya mai wuya game da wani batu na Littafi Mai Tsarki da kuke tattaunawa, ta yaya za ka nemi ƙarin bayani da zai taimake shi ya amsa waɗannan tambayoyi?
5 Ga waɗanda suke da Watchtower Library na CD-ROM a yarensu, yana da sauƙi a samu tushen bayani game da abubuwa da yawa a kwamfuta. Amma mutane da ba su da wannan na’urar fa? Bari mu bincika batutuwa biyu da aka bincika a cikin mujallar nan Bukata domin mu ga yadda za mu faɗaɗa fahimtarmu kuma mu iya ba da amsa dalla-dalla—musamman idan wani ya yi tambaya kamar su Wanene Allah, da kuma yaya kamanin Yesu yake?
Wanene Allah?
6, 7. (a) Waɗanne tambayoyi ne suka taso game da Allah? (b) Wane abu ne mai tsanani wani limami ya bari a lacca da ya yi?
6 Darasi na biyu a cikin mujallar nan Bukata ta amsa wannan tambayar mai muhimmanci, Wanene Allah? Wannan koyarwa ne mai muhimmanci ƙwarai domin mutum ba zai iya bauta wa Allah na gaskiya ba idan bai san shi ba ko kuma yana shakkar wanzuwarsa. (Romawa 1:19, 20; Ibraniyawa 11:6) Duk da haka, mutane a dukan duniya suna da ra’ayi dabam dabam game da Allah. (1 Korinthiyawa 8:4-6) Kowane ussi na addini yana da amsa dabam game da wanene Allah. A Kiristendam yawancin addinan suna da ra’ayin cewa Allah, Allah uku ne cikin ɗaya. Wani shahararren limami na Amirka ya yi lacca mai jigo “Ka San Allah?” amma bai ambaci sunan Allah ba ko sau ɗaya, ko da yake ya yi ƙaulin Nassosin Ibrananci sau da yawa. Hakika, ya yi karatu ne daga fassarar Littafi Mai Tsarki da ta yi amfani da “Ubangiji” da ba a san ko waye ba ne ko marar suna maimakon Jehovah ko kuma Yahweh.
7 Wannan limami ya bar darasi mai muhimmanci sa’ad da ya yi ƙaulin Irmiya 31:33, 34: “Ba kuwa za su ƙara koya ma juna, mutum da maƙwabcinsa, ɗan’uwa da ɗan’uwansa, su ce, Ku san Ubangiji; [Ibraniyanci “ku san Jehovah”] gama dukansu za su san ni, tun daga ƙaraminsu har zuwa babba, in ji Ubangiji: [Ibrananci Jehovah].” Wannan fassara da ya yi amfani da ita ta bar Jehovah, sunan Allah da ya bambanta shi.—Zabura 103:1, 2.
8. Menene ya kwatanta muhimmancin yin amfani da sunan Allah?
8 Zabura 8:9 ya kwatanta abin da ya sa amfani da sunan Jehovah yake da muhimmanci ƙwarai: “Ya Jehovah Ubangijinmu, sunanka yana da ɗaukaka a cikin dukan duniya!” (NW ) Duk da haka, a King James Version, da fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa a Turanci, mu karanta: “Ya UBANGIJI, Ubangijinmu, ina misalin darajar sunanka cikin dukan duniya!” Duk da haka, kamar yadda aka faɗa a cikin talifi na farko, za mu iya samun “sanin Allah” idan muka ƙyale Kalmarsa ta haskaka mu. Amma wane littafin taimako ne na nazarin Littafi Mai Tsarki zai amsa tambayoyinmu game da muhimmancin sunan Allah?—Misalai 2:1-6.
9. (a) Wane littafi zai taimake mu mu yi bayani game da muhimmancin kiran sunan Allah? (b) Ta yaya masu fassara da yawa suka kasa daraja sunan Allah?
9 Za mu iya juyawa zuwa mujallar nan The Divine Name That Will Endure Forever da aka fassara cikin harsuna 69.b Ɓangare mai jigo “God’s Name—Its Meaning and Pronunciation” (Sunan Allah—Ma’anarsa da Yadda Ake Kiransa), (Shafuffuka 6-11) ya nuna babu wani tantama cewa baƙaƙe huɗu na Ibrananci ya bayyana kusan sau 7,000 a littattafan Ibrananci na dā. Duk da haka, limamai da kuma masu fassara na Yahudanci da na Kiristendam sun cire shi da gangan daga yawancin fassararsu na Littafi Mai Tsarki.c Ta yaya za su yi da’awar sun san Allah kuma suna da nasaba da shi idan suka ƙi su kira sunansa? Sunansa na gaske ya buɗe hanyar fahimtar nufinsa da kuma yadda yake. Bugu da ƙari, menene muhimmancin addu’ar Yesu “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka” idan ma ba a kiran sunan Allah?—Matta 6:9; Yohanna 5:43; 17:6.
Wanene Yesu Kristi?
10. A wace hanya ce za mu iya samun cikakken tarihin rayuwa da kuma hidimar Yesu?
10 Darasi na 3 a mujallar nan Bukata shi ne mai jigo “Wanene Yesu Kristi?” A cikin sakin layi na shida, ya ba mu ɗan gajeren tarihin Yesu, tushensa, da kuma dalilin da ya sa ya zo duniya. Amma, idan kana son cikakken tarihin rayuwarsa, ban da Lingila—shi ne The Greatest Man Who Ever Lived, da ake samu a harsuna 104.* Wannan littafin ya ba da cikakken tarihin rayuwar Kristi da koyarwarsa, bisa tarihin Lingila huɗun. Babobinsa 133 sun ƙunshi abubuwa da suka faru a rayuwar Yesu da kuma hidimarsa. Domin bayani, za ka iya bincika Insight, Littafi na 2, a ƙarƙashin “Yesu Kristi” da kuma babi na 4 a littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada.
11. (a) Menene ya bambanta Shaidun Jehovah a abin da suka yi imani da shi game da Yesu? (b) Waɗanne ayoyi ne na Littafi Mai Tsarki suka ƙaryata koyarwar Dunƙulin-Alloli-Uku, kuma wane littafi ne yake da muhimmanci game da wannan?
11 A Kiristendam ruɗani game da Yesu a kan ko shi “Ɗan Allah” ne da kuma “Allah Ɗa”—watau, musu game da abin da Koyarwar Cocin Katolikawa take kira “tushen gagara fahimta na bangaskiyar Kirista,” Allah Uku Cikin Ɗaya. Shaidun Jehovah sun bambanta da Kiristendam, sun yi imani da cewa Yesu, Allah ne ya halicce shi amma shi ba Allah ba ne. Tattaunawa mai kyau na wannan batun yana cikin mujallar nan Ya Kamata ka Gaskata da Dunƙulin-Alloli-Uku?, da aka fassara cikin harsuna 95.d Markus 13:32 da 1 Korinthiyawa 15:24, 28 suna cikin nassosi da aka yi amfani da su wajen ƙaryata koyarwar Dunƙulin-Alloli-Uku.
12. Wace tambaya ce har yanzu take bukatar hankalinmu?
12 Abin da aka tattauna a baya game da Allah da kuma Yesu Kristi sun kwatanta hanyoyin da za mu iya yin nazari da burin mu taimaki waɗanda ba su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba su samu cikakken sani. (Yohanna 17:3) To, waɗanda suka yi tarayya da ikilisiyar Kiristoci na shekaru da yawa fa? Duk da ilimin Littafi Mai Tsarki da suka tara, suna da bukatar har yanzu su mai da hankali ga nazarin Kalmar Jehovah?
Me Ya Sa Za “Ka Mai da Hankali” Kullayaumi?
13. Wane mummunan ra’ayi ne wasu suke da shi game da nazari?
13 Wasu da suke cikin ikilisiya shekaru da yawa za su iya faɗawa cikin halin dogara a kan ilimi na Littafi Mai Tsarki da suka samu a shekarunsu na farko na Shaidun Jehovah. Ba shi da wuya mutum ya yi tunani: “Ba ni da bukatar na yi nazari sosai kamar sababbin. Ban da haka ma, ka ga sau nawa na karance Littafi Mai Tsarki da littattafansa a shekarun nan da suka shige.” Wannan zai yi daidai da faɗin cewa: “Ba ni da bukatar mai da hankali ga abin da zan ci, dubi dukan abinci da na ci a dā.” Mun san cewa jiki yana bukatar abinci da aka shirya sosai, domin ya kasance lafiyayye kuma da kuzari. Haka yake game da kula da lafiyarmu ta ruhaniya da ƙarfinmu.—Ibraniyawa 5:12-14.
14. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali ga kanmu?
14 Saboda haka, ko mu tsofaffin ɗaliban Littafi Mai Tsarki ne ko kuma a’a, muna bukatar mu bi gargaɗin Bulus ga Timothawus, wanda a lokacin ya kai mutum, kuma wanda yake da hakkin kula da ikilisiya: “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka. Ka lizima cikin waɗannan; gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.” (1 Timothawus 4:15, 16) Me ya sa ya kamata mu bi shawarar Bulus? Ka tuna, Bulus ya ce muna da yaƙi da “dabarun Shaiɗan” da kuma rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” Kuma manzo Bitrus ya yi gargaɗi cewa Iblis “yana neman wanda za ya cinye,” wannan “wanda” yake nema zai iya zama wani cikinmu. Gamsuwarmu zai iya kasance abin da yake bukata.—Afisawa 6:11, 12; 1 Bitrus 5:8.
15. Wace kāriya ta ruhaniya muke da ita, kuma ta yaya za mu kula da ita?
15 To, wace kāriya muke da ita? Manzo Bulus ya tunasar da mu: “Ku ɗauki dukan makamai na Allah, da za ku iya tsayayya cikin muguwar rana, kuma bayanda an gama duka, a tsaya.” (Afisawa 6:13) Ingancin waɗannan makamai na ruhaniya bai dangana a kan kyaunsu na farko ba amma kuma yadda aka kula da su. Wannan cikakken makamai na Allah dole ne ya haɗa da sani na yanzu na Kalmar Allah. Wannan ya nuna muhimmancin fahimtar gaskiya da Jehovah ya bayyana ta wurin Kalmarsa da kuma ta hannun ajin bawa mai aminci mai hikima. Nazarin littattafai na Littafi Mai Tsarki a kai a kai yana da muhimmanci wajen kula da makamanmu na ruhaniya.—Matta 24:45-47; Afisawa 6:14, 15.
16. Menene za mu yi domin mu tabbata cewa “garkuwa ta bangaskiya” an kula da ita da kyau?
16 Bulus ya nanata makamanmu na musamman na kai hari “garkuwa ta bangaskiya,” da za mu iya kawar kuma mu kashe kibiyoyi masu wuta na zargin ƙarya na Shaiɗan da kuma koyarwar ’yan ridda. (Afisawa 6:16) Saboda haka, yana da muhimmanci mu bincika ƙarfin garkuwarmu ta bangaskiya da kuma matakai da za mu ɗauka domin mu kula da ƙarfinta. Alal misali, za ka iya tambaya: ‘Ta yaya nake shiri domin nazarinmu na mako ta wajen amfani da Hasumiyar Tsaro? Ina yin nazari isashe da zan iya ‘tada juna a tsimi ga ƙauna da aiki nagari’ ta wajen ba da amsa mai kyau a taro? Ina buɗe Littafi Mai Tsarki na karanta ayoyi da aka nuna amma ba a rubuta ba? Ina ƙarfafa wasu ta yadda nake saka hannu da ƙwazo a taro? Abincinmu na ruhaniya yana da ƙarfi, muna bukatar mu fahimce shi sosai domin mu amfana ƙwarai.—Ibraniyawa 5:14; 10:24.
17. (a) Wace guba ce Shaiɗan yake amfani da ita domin ya yi ƙoƙari ya yi wa ruhaniyarmu zangon ƙasa? (b) Menene rigakafin wannan guba ta Shaiɗan?
17 Shaiɗan ya san raunanar ajizancin ’yan Adam, kuma dabarunsa a ɓoye suke. Hanya ɗaya da yake yaɗa rinjayarsa ta wajen sa hotunan mutane tsirara ya kasance da sauƙin samu a telibijin, Intane, bidiyo, da kuma littattafai. Wasu Kiristoci sun ƙyale wannan guba ta shiga wuraren da su suka raunana, kuma ya kai ga hasarar gata da suke da shi a ikilisiya har ma da sakamako mai tsanani. (Afisawa 4:17-19) Menene rigakafi na guba ta ruhaniya ta Shaiɗan? Kada mu yi watsi da nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, halartar taro na Kirista, da kuma makamanmu daga Allah. Tare, waɗannan suna sa mu iya bambance tsakanin abin da ke mai kyau da marar kyau kuma mu yi ƙyamar abin da Allah yake ƙyamarsa.—Zabura 97:10; Romawa 12:9.
18. Ta yaya “takobin ruhu” zai taimake mu a yaƙinmu na ruhaniya?
18 Idan muka ci gaba da halinmu na nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, za mu samu kāriya mai ƙarfi daga cikakken sani na Kalmar Allah da kuma ingantaccen hari da ‘takobin ruhu, kalmar Allah.’ Kalmar Allah ta “fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Afisawa 6:17; Ibraniyawa 4:12) Idan muka zama ƙwararru wajen amfani da “takobi,” to, sa’anda muke fuskantar jarraba, za mu iya gane abin da ya bayyana marar lahani, ko ma mai kyau, kuma mu fallasa shi cewa tarko ne na mugun. Ma’ajiyarmu ta ilimin Littafi Mai Tsarki da kuma fahimi za ta taimaka mana mu guji abin da ke mugu kuma mu yi abin da ke nagari. Saboda haka, dukanmu muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Shin takobi na ya yi tsatsa ko kuma yana da kaifi? Tuna ayar Littafi Mai Tsarki da za ta ƙarfafa harin yana yi mini wuya ne?’ Bari mu ci gaba da halinmu na nazarin Littafi Mai Tsarki da haka mu yi tsayayya da Iblis.—Afisawa 4:22-24.
19. Wane amfani za mu samu idan muka ba da kanmu ga nazari?
19 Bulus ya rubuta: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” Idan muka riƙe waɗannan kalmomin Bulus ga Timothawus a zuciyarmu, za mu ƙarfafa ruhaniyarmu kuma mu inganta hidimarmu. Dattawa da bayi masu hidima masu ruhaniya za su amfani ikilisiya ƙwarai, kuma dukanmu za mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi.—2 Timothawus 3:16, 17; Matta 7:24-27.
[Hasiya]
a Kamar yadda yake, sabon mutumin da yake nazarin mujallar nan Bukata zai ci gaba zuwa littafin nan Sanin da Ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, dukansu Shaidun Jehovah ne suka buga. Shawarwari da aka bayar a nan za su taimaka wajen warware irin waɗannan matsaloli da zai hana ci gaba a ruhaniya.
b Shaidun Jehovah ne suka buga. Waɗanda suke da Insight on the Scriptures a yarensu za su iya bincika Littafi na 2, a ƙarƙashin “Jehovah,” ka kuma duba babi na 3 a littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada.
c Masu fassara na Spananci da Kataloniyanci sun fice wajen yin amfani da Baƙaƙe Huɗu na Ibrananci, sun yi amfani da “Yavé,” “Yahveh,” “Jahvè,” da “Jehová.”
d Shaidun Jehovah ne suka buga.
Ka Tuna?
• Wane yanayi ne yake ƙara ingancin nazari?
• Wane kuskure ne yawancin fassarar Littafi Mai Tsarki suke yi game da sunan Allah?
• Wane ayoyi na Littafi Mai Tsarki za ka yi amfani da su ka ƙaryata koyarwar Dunƙulin-Alloli-Uku?
• Menene dole ne mu yi domin mu kāre kanmu daga dabarun Shaiɗan, ko idan mun kasance Kiristoci na gaskiya na shekaru da yawa?
[Hotuna a shafi na 27]
Domin nazari mai inganci, kana bukatar yanayi da ya dace
[Hotuna a shafi na 31]
‘Takobinka’ ya yi tsatsa ko kuma yana da kaifi?