Cin Nasara Bisa Kumamanci Na ’Yan Adam
“Himmantuwar jiki mutuwa ce.”—ROMAWA 8:6.
1. Yaya wasu suke ɗaukar jikin mutum, wace tambaya ya kamata mu bincika?
“ZAN yi godiya gareka; gama ƙirata abin tsoro ce, abin al’ajibi ce kuwa.” (Zabura 139:14) Haka Dauda mai Zabura ya rera waƙa yayin da yake bimbini a kan ɗaya daga cikin halittun Jehovah—jikin mutum. Maimakon ba da irin wannan yabo na ƙwarai, wasu malaman addinai suna ɗaukar jiki wurin jirar abu ne da kuma kayan aikata zunubi. An kira shi “abin da yake ɓoye jahilci, tushen mugunta, ɗaurin ruɓa, kejin mugunta, mutuwa mai rai, gawa mai rai, gawa mai tafiya.” Gaskiya, manzo Bulus ya ce: “Cikin jikina, ba wani abin kirki ke zaune ba.” (Romawa 7:18) Amma wannan yana nufin cewa ba mu da bege yayin da muke da jiki na zunubi?
2. (a) Menene “himmantuwar jiki” yake nufi? (b) Wane yaƙi tsakanin “jiki” da “ruhu” ke faruwa cikin mutane da suke so su faranta wa Allah rai?
2 Wasu lokatai Nassosi suna amfani da “jiki” a yin nuni ga mutum a yanayinsa na ajizanci, su zuriya ne masu zunubi na Adamu da ya yi tawaye. (Afisawa 2:3; Zabura 51:5; Romawa 5:12) Gadōnmu daga wurinsa ya kawo ‘rarraunar ɗabi’a.’ (Romawa 6:19) Kuma Bulus ya yi kashedi: “Himmantuwar jiki mutuwa ce.” (Romawa 8:6) Irin wannan “himmantuwar jiki” yana nufin zama waɗanda sha’awace-sha’awace irin ta halin mutuntaka na rinjayarsu kuma yake motsa su. (1 Yohanna 2:16) Saboda haka idan muna ƙoƙari mu faranta wa Allah rai, akwai yaƙi ko yaushe tsakanin ruhaniyarmu da yanayinmu na zunubi da yake matsa mana mu yi “ayyukan jiki.” (Galatiyawa 5:17-23; 1 Bitrus 2:11) Bayan ya kwatanta wannan matsanancin yaƙi a cikinsa, Bulus ya ce: “Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi! wanene za ya tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa?” (Romawa 7:24) Bulus ba shi da taimako ne daga jaraba? Littafi Mai Tsarki ya amsa a’a da babbar murya!
Takamancin Jaraba da Zunubi
3. Yaya mutane da yawa suke ɗaukan zunubi da jaraba, amma yaya Littafi Mai Tsarki ya yi kashedi a kan irin wannan hali?
3 Ga mutane da yawa a yau, zunubi ra’ayi ne da ba a amince da shi ba. Wasu suna ɗaukar kalmar nan “zunubi” aba ce ta wasa cewa furcin dā ne na kwatanta ƙananan laifuffukan mutane. Ba su yi tunani ba cewa “dole dukanmu za mu bayanu a gaban dakalin shari’a na Kristi; domin kowane ɗaya shi karɓi sakamakon aikin da yi cikin jiki, ko nagari ko mugu.” (2 Korinthiyawa 5:10) Wasu za su iya cewa: “Zan iya tsayayya wa kome ban da jaraba!” Wasu mutane suna zama a inda al’adarsu morewa ne na nan da nan, ko ya ƙunshi abinci, jima’i, liyafa, ko abin da aka cim ma. Ba kawai suna son kome da kome ba amma suna sonsa yanzu nan! (Luka 15:12) Ba sa duba gaba da daɗi na nan da nan a kan farin ciki na nan gaba na “rai wanda shi ke hakikanin rai.” (1 Timothawus 6:19) Amma Littafi Mai Tsarki ya koya mana mu yi tunani sosai kuma mu kasance da tsinkaya, muna guje wa kome da zai yi mana lahani a ruhaniya ko a wani wuri. Wani karin magana da aka hure ya ce: “Mutum mai-hankali ya kan hango ciwuta, ya ɓuya: amma marasa-wayo su kan wuce su sha wuya.”—Misalai 27:12.
4. Wane gargaɗi ne da ke rubuce a 1 Korinthiyawa 10:12, 13 Bulus ya bayar?
4 Lokacin da Bulus ya rubuta wa Kiristoci da ke da zama a Koranti—birni da aka san shi da rashin ɗabi’a—ya ba da takamaiman kashedi game da jaraba da ikon zunubi. Ya ce: “Wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi. Babu wata jaraba ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa: amma Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Korinthiyawa 10:12, 13) Dukanmu—matasa da tsofaffi, maza da mata—muna fuskantar gwaji da yawa a makaranta, wajen aiki, ko wani waje. Saboda haka, bari mu bincika kalmomin Bulus mu ga wace ma’ana suke da shi a gare mu.
Kada Ka Kasance da Yawan Gaba Gaɗi
5. Me ya sa yawan gaba gaɗi yake da haɗari?
5 Bulus ya ce: “Wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.” Yawan gaba gaɗi game da ƙarfin ɗabi’armu yana da haɗari. Yana nuna rashin fahimtar mutuntaka da kuma ikon zunubi. Tun da yake mutane kamar su Musa, Dauda, Sulemanu, da manzo Bitrus sun faɗa cikin zunubi, ya kamata mu ce ba za mu iya faɗawa ciki ba? (Litafin Lissafi 20:2-13; 2 Samu’ila 11:1-27; 1 Sarakuna 11:1-6; Matta 26:69-75) Misalai 14:16 ya ce: “Mai-hikima ya kan ji tsoro, ya kuma rabu da mugunta: amma wawa ya kan tada hanci, ya tabbata da komi.” Ƙari ga haka, Yesu ya ce: “Ruhu lallai ya yarda, amma jiki rarrauna ne.” (Matta 26:41) Tun da ba mutum ajizi da aka cire daga sha’awar lalata, muna bukatar mu ɗauki kashedin Bulus da muhimmanci kuma mu tsayayya wa jaraba, in ba haka ba za mu fāɗi.—Irmiya 17:9.
6. Yaushe kuma yaya ya kamata mu yi shiri don jaraba?
6 Yana da kyau a yi shiri domin wahala da zai auku farat ɗaya. Sarki Asa ya gane cewa lokacin salama ne ya dace ya yi gine-ginen mafaka. (2 Labarbaru 14:2, 6, 7) Ya san cewa zai makara ainun idan zai shirya a lokacin da aka kawo masa hari. Hakanan ma, shawara game da abin da za a yi lokacin da jaraba ta faɗo ya fi kyau a yi shi da cikakken hankali, a lokacin da babu tashin hankali. (Zabura 63:6) Daniel da abokansa masu jin tsoron Allah sun yi shawararsu su kasance da aminci ga dokar Jehovah kafin a matsa musu su ci abinci irin na sarki. Saboda haka sun manne wa tabbacinsu kuma ba su ci abinci mara tsarki ba. (Daniel 1:8) Kafin yanayin gwaji su taso, bari mu ƙarfafa ƙudurinmu a ranmu za mu kasance da tsabtacciyar ɗabi’a. Sa’an nan za mu iya tsayayya wa zunubi.
7. Me ya sa abin ƙarfafa ne mu san cewa wasu sun yi nasara a tsayayya wa jaraba?
7 Mun sami ta’aziyya daga kalmomin Bulus: “Babu wata jaraba ta same ku sai irin da mutum ya iya jimrewa”! (1 Korinthiyawa 10:13) Manzo Bitrus ya rubuta: “Ku tsaya ma[Iblis] fa, kuna tabbatawa cikin bangaskiyarku, kuna kuwa sani ’yan’uwanku da ke cikin duniya suna shan waɗannan azabai da ku ke sha.” (1 Bitrus 5:9) Hakika, wasu sun fuskanci irin wannan gwaji kuma sun ci nasara wajen tsayayya musu da taimakon Allah, saboda haka muma za mu iya. Amma, da yake mu Kiristoci ne masu zama a duniya da ta lalace, dukanmu za mu yi tsammanin gwadi ba da daɗewa ba. To, yaya za mu kasance da tabbaci cewa za mu yi nasara bisa kumamanci na ’yan Adam da jarabar yin zunubi?
Za Mu Iya Tsayayya wa Jaraba!
8. Ta wace muhimmiyar hanya ce za mu guje wa jaraba?
8 Muhimmiyar hanya ta daina “bauta ma zunubi” ita ce mu guje wa jaraba inda zai yiwu. (Romawa 6:6) Misalai 4:14, 15 sun aririce mu: “Kada ka shiga hanyar miyagu, kada ka yi tafiya cikin tafarkin mutane masu-mugunta. Ka kauce masa, kada ka gilma wurin: ka kawarda kai, ka wuce.” Sau da yawa muna sane da cewa wani yanayi zai iya kai ga yin zunubi. Saboda haka, abin da ya fi kyau Kiristoci su yi shi ne su yi ‘tafiyarsu,’ su guje wa kowa da kuma kome da zai ta da mummunar sha’awa kuma sa mu yin sha’awar lalata.
9. Yaya aka nanata guje wa yanayin jaraba a cikin Nassosi?
9 Guje wa yanayi na jaraba shi ne mataki na musamman a yin nasara bisa jaraba. Bulus ya ba da gargaɗi: “Ku guje ma fasikanci.” (1 Korinthiyawa 6:18) Kuma ya rubuta: “Ku guje ma bautar gumaka.” (1 Korinthiyawa 10:14) Manzon ya kuma ba Timothawus kashedi ya guji mugun marmarin abin duniya, da kuma “sha’awoyin ƙuruciya.”—2 Timothawus 2:22; 1 Timothawus 6:9-11.
10. Waɗanne misalai biyu ne da suka bambanta suka nuna muhimmancin guje wa jaraba?
10 Yi la’akari da abin da ya faru da Dauda, sarkin Isra’ila. Yayin da yana kallo daga jinkan fadarsa, ya ga mace kyakkyawa tana wanka, sai mummunar sha’awa ta cika masa zuciya. Da ya kamata ya bar jinkan kuma ya guje wa jaraba. Maimako, ya yi tambaya ko waccece wannan matar—Bat-sheba—sakamakon haka ɓarna ce. (2 Samu’ila 11:1–12:23) A wata sassa kuma, yaya Yusufu ya yi lokacin da malalaciya matar ubangidansa ta aririce shi ya kwana da ita? Labarin ya gaya mana: “Da ta riƙa yin magana da Yusufu yau da gobe, ba ya kula da ita ba, da za ya kwana da ita, ko kuwa ya zauna wurinta.” Ko da ba a bayar da umurnan Dokar Musa ba tukuna, Yusufu ya amsa da cewa: “Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?” Wata rana ta kama rigarsa, tana cewa: “Ka kwana da ni.” Yusufu ya zauna a wurin ya yi mata magana ne? A’a. Ya “gudu, ya fita waje.” Yusufu bai ba jarabar yin jima’i zarafi ta sha kansa ba. Ya gudu!—Farawa 39:7-16.
11. Menene zai yiwu idan muna fuskantar jaraba da take maimaita kanta?
11 Wani lokaci ana ɗaukar gudu tsoro ne, amma cire kanmu daga wani yanayi sau da yawa shi ne tafarkin hikima da za mu bi. Wataƙila muna fuskantar jaraba da take maimaita kanta a wajen aiki. Ko da ba za mu iya canja aikinmu ba, akwai wasu hanyoyi da za mu cire kanmu daga yanayin jaraba. Muna bukatar mu guji kome da mun sani ba shi da kyau, ya kamata mu ƙuduri aniyyar yin abin da yake da kyau kawai. (Amos 5:15) A wani waje, guje jaraba zai bukaci guje hotunan sirarun mutane a Intane da wuraren liyafa da ba su da kyau. Mai yiwuwa zai ƙunshi yar da wata jarida ko neman sababbin abokai—waɗanda suke ƙaunar Allah kuma waɗanda za su iya taimakonmu. (Misalai 13:20) Ko menene ya jarabe mu mu yi zunubi, muna da hikima idan mun ƙi shi.—Romawa 12:9.
Yadda Addu’a Za ta Taimaka
12. Wane roƙo muke yi daga Allah yayin da muke addu’a: “Kada ka kai mu cikin jaraba”?
12 Bulus ya ba da wannan tabbaci mai ba da ƙarfafa: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Korinthiyawa 10:13) Hanya ɗaya da Jehovah yake taimaka mana shi ne ta amsa addu’o’inmu don taimakonsa a jure wa jaraba. Yesu Kristi ya koya mana yadda za mu yi addu’a: “Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga Mugun.” (Matiyu 6:13) A ba da amsa ga irin wannan addu’a daga zuciya, Jehovah ba zai yashe mu ba ga jaraba; zai cece mu daga Shaiɗan da ayyukansa na maƙirci. (Afisawa 6:11, hasiya ta NW ) Ya kamata mu gaya wa Allah ya taimake mu gane jaraba kuma mu samu ƙarfi da za mu tsayayya masa. Idan mun roƙe shi kada ya yarda mu faɗi in an jarabe mu, zai taimake mu don kada Shaiɗan “mugun,” ya fi ƙarfinmu.
13. Me ya kamata mu yi yayin da muke fuskantar jaraba ta kullum?
13 Muna bukatar mu yi addu’a sosai musamman ma yayin da muke fuskantar jaraba ta kullum. Wasu jaraba za su iya kawo fama mai ƙarfi cikin jikinmu, da tunani da halaye da suke tuna mana cewa da gaske mu raunannu ne. (Zabura 51:5) Alal misali, me za mu yi idan mun tuna wasu abubuwa da ba su da kyau da muka yi dā suna damun mu? Idan muna cikin jarabar mu sake yinsu kuma fa? Maimakon ka yi ƙoƙarin ɗaure yadda ka ke ji, sai ka gaya wa Jehovah batun cikin addu’a—a kai a kai yadda bukata ta kama. (Zabura 55:22) Da ikon Kalmarsa da kuma ruhu mai tsarki, zai taimake mu mu tsabtace nufe-nufe mara tsarki daga zuciyarmu.—Zabura 19:8, 9.
14. Me ya sa addu’a take da muhimmanci a jure wa jaraba?
14 Da ya lura cewa manzanninsa suna gyangyaɗi a gonar Jathsaimani, Yesu ya aririta: “Ku yi tsaro, ku yi addu’a, kada ku shiga cikin jaraba: ruhu lallai ya yarda, amma jiki rarrauna ne.” (Matta 26:41) Hanya ɗaya da za ka magance jaraba ita ce ka zauna a faɗake ga hanyoyi dabam dabam da jaraba za ta iya ƙunno kai kuma ka lura da dabararta. Yana da muhimmanci mu yi addu’a game da jarabar ban da ɓata lokaci don mu kasance a shirye a ruhaniya mu yaƙe ta. Saboda jaraba tana taɓa mu inda ba mu da ƙarfi, ba za mu iya tsayayya mata mu kaɗai ba. Addu’a tana da muhimmanci domin ikon da Allah yake bayarwa zai iya taimaka wa tsayawarmu gāba da Shaiɗan. (Filibbiyawa 4:6, 7) Mai yiwuwa za mu kuma bukaci taimako na ruhaniya da addu’o’in “dattiɓan ikilisiya.”—Yaƙub 5:13-18.
Ka Tsayayya wa Jaraba da Ƙwazo
15. Menene tsayayya wa jaraba ta ƙunsa?
15 Ban da guje wa jaraba idan ta yiwu, dole ne mu tsayayya mata sosai har sai ta wuce ko kuma yanayin ya canja. Lokacin da Shaiɗan ya jaraba Yesu, ya tsayayya masa har sai da Iblis ya tafi. (Matta 4:1-11) Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya guje maku.” (Yaƙub 4:7) Tsayayya yana soma ta ƙarfafa zuciyarmu da Kalmar Allah kuma tsai da shawara cewa za mu manne wa mizanansa. Zai yi kyau mu haddace kuma mu yi bimbini a kan muhimman nassosi da ya shafi takamanmun kumamanci da muke da shi. Zai yi kyau mu sami Kirista da ya manyanta—wataƙila dattijo—wanda za mu gaya wa damuwarmu kuma wanda za mu je ya taimake mu yayin da muke so mu yi abin da ba shi da kyau.—Misalai 22:17.
16. Ta yaya za mu kasance da ɗabi’ar kirki?
16 Nassosi ya aririce mu mu ɗauki sabon hali. (Afisawa 4:24) Wannan yana nufin mu yarda wa Jehovah ya mulmula mu kuma ya canja mu. Da yake rubuta wa abokin aikinsa Timothawus, Bulus ya ce: “Ka bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, tawali’u. Ka yi yaƙin kirki na imani, ka ribce rai na har abada, wanda aka kira ka zuwa gareshi.” (1 Timothawus 6:11, 12) Za mu iya ‘bin adalci’ ta himmantuwa cikin nazarin Kalmar Allah don mu samu sanin mutuntakarsa da kuma ta yin hali da ya yi daidai da farillansa. Cikakken tsari na ayyukan Kirista, kamar su yin wa’azin bishara da halartan taro, suna da muhimmanci ma. Matsowa kusa da Allah da kuma yin cikakken amfani da tanadinsa na ruhaniya zai taimake mu mu yi girma a ruhaniya kuma ma mu kasance da ɗabi’ar kirki.—Yaƙub 4:8.
17. Yaya muka sani cewa Allah ba zai yashe mu lokacin jaraba ba?
17 Bulus ya tabbatar mana cewa ba jaraba da za ta taɓa mu da zai fi ƙarfin da Allah ya ba mu mu bi da ita. Jehovah zai ‘ba da mafita, yadda za mu iya jurewa da ita.’ (1 Korinthiyawa 10:13) Hakika, Allah ba ya barin wata jaraba ta yi tsanani har mu yi rashin isashen ƙarfi na ruhaniya don mu riƙe aminci idan mun ci gaba da dogara a gare shi. Yana son mu ci nasara a tsayayya wa jarabar yin abin da ba shi da kyau a gabansa. Ƙari ga haka, za mu iya kasancewa da bangaskiya cikin alkawarinsa: “Daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.”—Ibraniyawa 13:5.
18. Me ya sa za mu tabbata za mu yi nasara bisa kumamanci na ’yan Adam?
18 Bulus ba ya tantamar sakamakon famansa a kan kumamanci na ’yan Adam. Bai ɗauki kansa wani da za a ji tausayinsa ba kumami na sha’awa irin ta halin mutuntaka ba. Akasin haka, ya ce: “Haka fa ni ke yin tsere, ba kamar da shakka ba; haka ni ke yin dambe kuma, ba kamar mai-naushen sarari ba: ina dandaƙin jikina, ina kai shi cikin bauta: domin kada ya zama bayanda na yi ma waɗansu wa’azi, ni kaina a yashe ni.” (1 Korinthiyawa 9:26, 27) Mu ma za mu iya yin yaƙi mai nasara gaba da ajizan jikunanmu. Ta wurin Nassosi, littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki, taron Kirista, da ’yan’uwa Kiristoci da sun manyanta, Ubanmu mai ƙauna na samaniya na tanadin tuni a kai a kai da zai taimake mu mu biɗi tafarki na adalci. Da taimakonsa, za mu ci nasara bisa kumamanci na ’yan Adam!
Ka Tuna?
• Me ake nufi da ‘a himmanta ga al’amuran jiki’?
• Yaya za mu shirya domin jaraba?
• Menene za mu yi don mu jure wa jaraba?
• Wane matsayi ne addu’a take da shi a bi da jaraba?
• Ta yaya muka sani cewa zai yiwu a yi nasara bisa kumamanci na ’yan Adam?
[Hotuna a shafi na 8]
Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa mu mutane ne waɗanda ba su da taimako ba game da sha’awa irin ta halin mutuntakarmu
[Hoto a shafi na 10]
Gudu daga jaraba muhimmiyar hanya ce ta guje wa zunubi